Zee Baby Book 1 Page 3

*Free Page 3*

….nutsuwa ya sakama kansa ya qaqaro murmushi yana kallonta ya janyeta daga jikinsa ya kama hannuta suka nufi inda ta yasar da Abbayar ya sunkuya ya dauka haka kawai yakejin ciwon kallon da Jamal yake mata saka mata Abbayar yai suka dawo saman kujere. kusansa ta zauna tana murmushi zata kwanta jikinsa ya kiya ya kalleta da harshan turanci yace” kanwata ykk ina kika shiga har tsawon kwana biyu? hannusa ta rike ta fara magana da Hausarta babu wani kwarewa ” Ahukhuya banason Nigeria na gudu gidan abokina Maharaz ya boyeni kwana biyu yana bani kulawa yanzu ina cikin bacci Dan buro ubansa yazo yana matsani niko na saka masa kunama adiyan kaya na gudo gida ta fada tana wata irin dariya idanuwanta sun kade sunyi jajir alamar bata huceba kunyace ta kamasu ya kalli hannusa da ta rike tana murzawa tana dariya kamar zarara aransa yace ya Allah ka rabanin da wannan shawa Dan naga wannan

Ko munje ba daina tabani zatayi ba naga tabi’artace taba jikin mutum batare da ta kawo komai araiba sakinsa tayi ta Mike ta nufin gun Raiyan ta fada jikinta tana mata magana da larabci tana sakar mata kiss”ummina nayi missing dinki? ta rumgumeta gam tana kukan shagwaba ajiyar zuciya ta sabke tana buga bayanta Alamar lallashi fada ta Shiga mata da nasiya ta lallabata har tayi shiru dagowa tayi ta kalli manal ta harareta” ke Dan uwarki shine zaki wani zo gidanmu ai kinsan bananan salon ku tadawa ummina hankali? dariya manal tayi tana kallon jannat” habibty ummi taje ta dauko mu fah kallin jannat tayi ta mata magana da idanu ta mayar mata mik’ewa tayi daga jikinta ” kuzo muje ciki banyi sallah Azuhur ba tashi sukayi suka bita Mahabeer sosai yakejin sonta cikin ransa kai tsaye tin lokacin da ta rumgumeshi kallon ummi yai

ya fuskan ceta suna magana Jamal ko har yanzu wandonsa baibar motsiba ummi Raiyan tace” Mahabeer ba fah lako lako zakuyi mataba Dole sai kun zage kun zazare mata to bare kai da take ra’ayinka Akan Al’mahadee wato Dr Sardauna don haka ka sa mata idanu sosai don Allah kusa ta dawo cikakiyar mutum ina so naga zaeenaba ta nutsu tazama kamilar mace tayi nisa dani ko hankalina ya kwanta ko iyayena zasu yafemun tunda sun nuna itace basu kauna sunfi son abokan haihuwarta mazan biyu sun rabani dasu sunsaka ‘ya’yan cikina sun gujeni sun tsaneni ni da Zaeenaba saboda ta nuna kauna gareni wlh ina sonta bana son rabuwa da ita amma Dole zan hakura saboda hankalina zai fi kwanciya inaji tsoron ya saka akasheta ta fadi tana goge hawaye Dan tasan tabbas Zee taga kukanta akwai bala’i ajiyar zuciya ya sabke cike da tausayinta ” ummi Raiyan kiyi hakuri

Insha Allahu zata nutsu kuma zaku shirya da mahaifanki wlh Dole yaranki zasu nemeki koba bajima yanzu ma hankaline bai gama ratsasu ba shekara sha bakwai ne fah suke ciki to cikin su Zaeenaba tafisu wayo ita da take mace ajiyar zuciya ta sabke ” to da fatan zaka yimun koda wata daya kafin ku tafi? idanu ya zaro ummi wlh bakin kwana ukku zanyi mukoma aiki sunmun yawa bakiga shi Al’mahadee da bashida dama Dole nine nazo murmushi tayi ” to Allah ya kaiku lfy ya kuma hada fuskokinmu da Alkhairi? ” Ameen ummi suna cikin hira akayi kiran sallah la’asar suka Mike sukaje sukayo Alwalla suka tafi masallacin da yake manne kusa da gidan ummi ta Mike ta shiga tayi sallah zuciyarta babu

Dadi batason rabuwa da yar tata amma da ta tuna rashin jinta gashi batasan me zai faru a gaba ba Dan rashin jin. Yar tata sai ahankali gashi tana Addu’a ba dare ba rana amma baby wani sauyi Zee baby ko suna shiga ta tube kayan jikinta tana rawa da juyi sai ihu takeyi tana dariya daga ita sai shegiyar rigar nan manal tace” my habibty wlh iskanciki gaba yakeyi fah fasa rawar tayi wata shegiyar tsayuwa akarkace tana kallonta shekeke tana murmushi ” bari nayi bautar Allah na gama zanci durin uwarki la’ada waje yasin bathroom ta shige jannat ta kalli manal ” wlh duk kece kika koya mata Hausa da zage zage gashinan akanki take sabkesu wlh dazu naji kunyar abun da ta fadi gaban baki? dariya manal tayi” naji amma shaye shaye wa ya koya mata Dan kaniyar mai da famiki shurba daga cikin toilet ta lailayo zagi ta dirka musu ta ciko Dan bokiti da ruwa ta bude kofar ta watso musu ” sheguna ina jinku fah ta koma taci gaba da wankata ta dauro Alwalla ta fito tabude wardrobe dinta ta bude ta ciro Abbaya ta saka ta nade kanta da mayafin ta shimfida dadduma tayar da sallahr Azuhur, suko kayansu sukacire suka canza da nata suna mata Allah ya isa azuciya tana idarwa taji kiran la’asar ta tashi ta tayar suma Alwalla suka dauro sukayi sallah tana gamawa ta ci uwar kwalliya tasaka wata atamfa bakace mai ratsin fari dinki Riga da siket manal ce me musu dinki tare su ukku kullum to jannat ba’a barinta tana sawa agidansu saide idan ta fito gashinta ta sarce ta daureshi tayi masifar kyau kamar ka saceta sai dai dinkin ya fito da surata yan mazaunanta masu daukar hankali sai motsi suke tana kadasu gangan tana musu gwalo manal tace ” dallah can figigiyar banza nacemiki ki faso gari kizama yar duma duma A dama dake kullum ke kamar kinashan ruwan zafi ta fesa turare

ta kallesu ” wlh manal danayi jiki gwara daga haka nakara tsotsewa Dan uwarki ko ba jiki akwai kayan aiki ta juyo mata yan mazaunanta masu qira coca cola tana fito da harshe waje tana kadawa ihu suka saka ” ku tashi muje parlo ku gaishe da Dan uwana kuma wlh sai kun duka har k’asa fitowa sukayi suna dariya gun mahabeer suka nufa ta zauna kusansa suko suka duka suna masa sannu da zuwa cikin fara’a ya amsa yace” ko zaku bimu Nigeria ne kai suka girgiza suna dariya Zee ta jinginu da jikin Mahabeer ashagwab’e tace” Ahukhuya nima bana zuwa fah ta Kara shigewa jikinsa tana turo baki aransa Adu’a yakeyi Allah yakawo masa dauki son yarinyar yamasa mugun kamu ga wata muguwar shawarta da yakeji janyeta yayi yana murmushin karfin hali ” kanwata kiyi hakuri muje sati dayane zakiyi ki dawo ko ummi ya fada yana kallon ummi dariya tayi” eh sati daya zakiyi habibty ajiyar zuciya ta sabke” to naji amma da anyi sati zaka maidoni kuma ba gidansu wannan banzan gayan bane zan zauna ko ummi ta matso ta doketa abaya tun karfi take dukanta tana mata magana da larabci saida ta Saki Kara ta rukunkume Mahabeer tana kukan sangarta tare dukan yai yanaba ummi hakuri ransa babu dadi Dan yaji haushin bugun da take mata kamar yayi kuka yace” haba ummi Raiyan Zee yarinya ce fah lallabata zamuyi zata daina masa amma dukan yayi yawa sai ajimata ciwo ai idanu ummi Raiyan ta zuba masa cike da mamakinsa ” haba Mahabeer yanzu ahakane zaku ku gyarata kana daure mata gindi wlh shiyasa naso yazo da kansa tun kafin su isa can taci gidansu la’ada waje cikin shashekar kuka tace” Ahukhuya kagani kullum sai ummi ta dokeni saboda wannan mungun mutumin wlh idan mukaje Nigeria mutikar na Ganshi akasar idona

idanusa kafin na dawo Allah na dauki Alkawarin sai na Rama abinda akamun akansa ta fada tana Kara rumgumesa tana kukan takaicin duk lokacin da zata zageshi sai ummi ta doketa kuma duka ba na wasaba shiyasa takejin duk duniya ta tsaneshi sama da komai Hasbinallahu Wani’imar Wakim kawai yake maimaitawa gashi bayason kukanta daurewa yayi yana bubbuga bayanta ” yi hakuri kanwata nima bazan yardaba anaci miki mutumci yi shiru kinji ya leko fuskarta shiru tayi ta boye kanta kirjinsa samu yayi ya lallabata ya janyeta jikinsa Jamal da idanu yake binsu yanajin haushin yada idan tahau jikin Mahabeer yake janyeta baya bari ya rage zafi ba lallashinta ya shiga yi har ta Saki ranta suko su manal sunsha mamaki Dan sunsan Zee baby bata cika kuka ba a Al’amuranta kuka baya cikin tsarin rayuwarta ummi dai da idanu take binsu yau ta Mahabeer take ta Saki jikinta sai labari take bashi yako maida hankalinsa kanta sai dariya yakeyi Jannat na tayasu Dan Mahabeer ya burgeta bashida damuwa akwai fara’a
Saida akayi kiran sallah magrib suka Mike sukayi shirin zuwa masallaci suma su Zee baby suka tafi suyi sallah sai tsokanarta sukeyi wai taga Dan uwanta ta sheresu dariya tanusu batace dasu komaiba,

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button