Labarai

Kabilar Latuka: Kabilar da sai saurayi ya sace budurwar da yake son aura kafin iyayenta su bashi aurenta

A sauran kasashen duniya, sai namiji ya fara neman soyayya da kuma amincewar mace tare da izinin iyayenta sannan maganar aure ta kankama da.

Ga mutanen kabilar Latuka, komai ya sha bamban, don saurayin tare da taimakon abokansa ko ya yi hayar wadanda za su sace budurwar da ya gani yana so.

Bayan satar, zai sanar da mahaifinta sannan mahaifin ya kama shi ya zane a matsayin amincewarsa, daga nan za a fara shirye-shiryen aure.

Kabilar Latuka su na da wata al’adar ta daban a wurin neman aure. Bisa al’adarsu idan saurayi ya ga budurwar da ya ke son aure, dole ne ya sace ta inda zai yi hayar wasu maza wadanda su yi kwanton bauna, su damke budurwar da ta sace zuciyar tasa.

Bayan sace ta, za su wuce da ida zuwa gidan saurayin ne inda za a ajiyeta ta ba tare da son ranta ba, daga bisani saurayin zai je ya sanar da mahaifinta.

Wani abin mamaki shi ne, bayan sanar da mahaifin matar, mahaifin zai zane surukin nasa ne a matsayin amincewarsa.

Kabilar Latuka

Ba za a iya tantance kwatankwacin zafi ko kuma tsananin dukan da mahaifin nata ya ke yi ba amma daga zarar mace ta ga namiji ya yi garkuwa da ita, kawai za ta cire ran auren zabinta wanda tayi burin zama dashi har karshen rayuwarta.

Bikin su ya sha bamban dana sauran al’umma

A sauran kasashen duniya, ana yin gagarumin biki ne waje mika mace gidan mijinta, wanda yawanci mahaifin amaryar ne ya ke damka ta ga masoyinta, bayan mata da miji sun amince da juna sun sasanta kawunansu kuma sun yarda za su zauna tare, sai dai ba haka bane ga mutanen Latuka.

Su tasu al’adar sai bayan manemin yarinya ya sace ta sannan sai ya tura magabatansa suje nemo masa aurenta.

Har a lokacin yarinya tana can a boye, amincewar mahaifinta ake jira ko kuma akasin hakan. Ko wacce amsa ya bayar, walau “e” ko “a’a” daga bakin mahaifin yarinyar dole ne shagali da hidima ya biyo baya.

Mahaifin budurwa na dukan saurayi a matsayin amincewa da bukatar auren ‘yarsa

Idan mahaifin yarinyar ya amince ya karbi wanda ya sace diyarsa a matsayin siriki zai yi dukan tsiya a matsayin nuna amincewarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan dukan da ake yi yana nuni da cewa duk mutumin da ya yarda ya karbi wannan dukan yana son auren budurwar tasa.

Haka zalika idan mahaifin yarinyar ya ki amincewa da auren, saurayin yana da zabin ko dai ya mayar da ita ga iyayenta ko kuma ya riketa.

Kabilar Latuka manoma ne da kuma makiyaya da ke rayuwa a saman tsaunin kudancin Sudan kuma ba sa da addini.

Duk da yadda jama’a ke sukar al’adar tasu, sun toshe kunnuwansu sun ci gaba da aiwatar da ita tsawon zamani

Daga @Hausa Legit

 

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button