Labarai

Akalla mutum 8 ne suka rasa ransu a Hatsarin Mota Ƴan unguwar Kofar Mani a jihar Zamfara

Inna Lillahi Wa inna Ilaihi Raji’un!

Kamar yadda shafin Jakadiyar Zamfara a shafin Facebook suka wallafa.

Ƴan Unguwar Kofar Mani dake Gusau, Jihar Zamfara, su takwas (8) sun rasu sanadiyar hatsarin Mota.

 

Allah ka jikansu ka gafarta masu.

A wani labarin kuma;

Aƙalla mutane 11 ne ‘yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin yana ɗauke da guba a ƙauyen Ikobi dake ƙaramar hukumar Apa dake jihar Benuwai.

 

Mazauna garin sunce ana tunanin cewa mutanen waɗanda duk ‘yan zuri’a ɗaya ne sun ci wani abinci ne da yake ɗauke da wasu sinadarai na guba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin su tare da jikkata wasu, kamar yadda Thisday ta wallafa.

 

An bayar da sunayen waɗanda suka mutu sanadin cin abincin da Peace Ochoyoda, Aboyi Ngbede Ochefije, Ochefije Ojo, Maria Ojo, Aipu Ochefije, Mary Ochoyoda, Ehi Abu, Blessing Abu, Ojochono Daniel, Adi Ale, da kuma Favour Edoh.

 

Majiyar mu ta ƙara da cewar mutane shida daga cikin waɗanda suka ci abincin sun mutu ne a wannan rana da suka ci abincin. Su kuma ragowar mutane biyar ɗin sun mutu ne bayan wasu ‘yan kwanaki.

 

Wani daga cikin mutanen ƙauyen mai suna Ochoyoda Abu, ya bayyana cewa ya rasa matar shi mai suna Mary, da ‘yan uwan shi mata su biyu; Ehi da Blessing, da kuma ɗiyar shi mai suna Peace.

 

Dagacin ƙauyen na Ikobi mai suna Farfesa Muhammed Adah, a hirar shi da manema labarai ta wayar tarho ya bayyana cewa wani abu makamancin wannan ya taɓa faruwa a watan Satumba da ya gabata.

 

Yace sun fara fargabar cewa abincin yana ɗauke da guba ne bayan da mutane biyar na farko suka mutu. Yace ya zuwa yanzu sun gayyato ƙwararrun jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta jihar don gudanar da bincike.

 

Dagacin ya ƙara da cewa har ya zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto basu samu sakamakon gwaje-gwajen.

 

Majiyar tamu ta ƙara da cewar akwai waɗanda kuma sunci abincin amma basu mutu ba, sai dai an garzaya da wasu daga cikin su zuwa asibiti wanda daga bisani duk aka sallame su.

 

Sai dai a nata ɓangaren, jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sandan jihar ta Benuwai, SP Catherine Anene ta bayyana cewa a rahoton da suka samu, mutane bakwai ne suka mutu a rana ɗaya bayan cin abincin.

 

 

Ta ƙara da cewar a ranar 14 ga watan nan da muke ciki akwai wani wanda ya mutu a wannan gida. Wata mata daga cikin ‘yan gidan ta deɓo wani ajiyayyen abinci sannan ta dafa shi inda mutane guda 12 suka ci.

 

Bayan cin abincin nasu ne duk suka kama rashin lafiyar da tayi sanadiyyar mutuwar guda bakwai daga cikin su a rana ɗaya. Sannan kuma tace an garzaya da ragowar biyar ɗin zuwa asibiti inda daga bisani suka warke kuma aka sallame su.

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button