NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

NA CUCE TA

馃挌馃挋馃挏馃枻馃挍鉂�

庐zuwairat( ummu Maryam)

1鈨�

_Alhamdulillah, Allah praise be to almighty Allah_

_Am back again_

Cikin wani gidan Wanda ke ginin kasa mai dauke da daguna biyu wata yarinya ce wacce bazata wuce shekara shabiyu zuwa sha uku ba ke daka sai tim Tim Kawai kakeji saboda yanda take dakan garin furan dake cikin trumi, daga dayan gefen  Kuma wata matace ke hura wuta sai kafawa murhun bakin take tana hura wutan, duk idanuwanta sun chanza kala saboda yanda hayake ke shiga idonta, wata yar yarinya na gani ta taho da gudu da wata faifai

 

“Ammi ki hura da wannan….” Yarinyan ta fada mata, matar dake durkushe gaban murhun dagowa tayi ta sakarwa yarinyan murmushi tare dacewa

“Yauwa…nagode binto…” Matar ta fada tana amsan faifan daga hannun yarinyan.

Da ganin Matan da yanayin gidan kasan gidan kasan masu karfin haline sosai don komai NA gidan is low to the last core, yarinya dake dakan goge zufan goshinta tayi ta kalli matar da aka kira da ammi tace

“Gaskiya ammi gobe mu kai injin…NA gaji da daka Wallahi hannuna duk ya kumbura.. Nidai NA gaji…” Tafada tana turo baki tare da kallon tafin hannunta ya kumbura saboda yawan daka

Ammi kallon ta tayi Sannan ta maida dubanta ga muhur

“In banda abinki dije AI kin San da wannan dakan muke samun abinda zaa bawa awakan nan …in an kai inji ba su bamu dusa…” Ammi ra fada tana hura wutan, dija Kara turo baki tayi

“Wai ammi dole ne mu bar wayan nan awakan?… A saida su mana Kawai…” Tafada in I don’t care manner, ammi kallon ta tayi ta tabe baki

“Ai babu abinda kika Sani..maza ki kara kar su saude su bar ki yau ma…” Ammi ta fada mata bayan ta gama hura wutan. Dija kara turo baki tayi

“Nidai NA gaji….binto…” Ta kwalawa kanwarta kira,

“Naam….” Yarinya ta amsa mata

“Zo ki tayani….” Tafada tana barin tabaryar cikin turmin, ammi kallon ta tayi

“Wai ke wace irin banzar yarinya ce?…yanzu binto zaki barwa dakan furan?…. Dalla ki maida hankali kar lokaci ya kure…sakara Kawai..” Ammi ta fada tana debo taliyan kadi daga kan igiya tana zubawa cikin kwarya dake hannun ta.

Dija tana turo baki ta dake furan ammi tayi molding dinshi ta zuba mata cikin roban da take zuwa talla da ita Sannan tayi mata gammo,

“In kin saida ki sayo magi da hamsin… Fulawa quarter..sai ki sayo sabulu guda daya Dan hamsin da biyar…” Ammi ta fada mata tana Dora mata gammon bisa kanta, dija dai Bata ce kala ba don in da zaa kashe ta ya fiye mata wannan tallan da take amma Kuma Bata Iya kin zuwa saboda ta nan suke samun mostly abinda suke amfani dashi da yau da kullum, furan ammi ta dauki ra aza mata bisa gammon har lokacin Bata bar kumbure2 ba

“Wai ke meke damunki?…” Ammi ta tambayeta, kara turo baki tayi

“Ni wallahi ammi banason talla… In munje garejin daura duk yawancin mazan yan iska ne….” Baki ammi ta bude tana kallon ta, dija ta cigaba dacewa

“Sai suce sai sun taba mutum Sannan su sayi furan sa….” Idanuwa ammi ta zaro tana mamakin abinda yarta take fada mata, kallon yarinyan tayi ta kalli kirjinta dake dauke da boobs yan kanana da basu gama developing ba,

“Wallahi ammi jiya wani cemin yayi in zauna kan kafanshi ya sayi dukkan furan…” Ta fada tana fashewa da kuka, da Sauri ammi ta sauke furan daga kanta tana cewa

“Wai da gaske kike?…”

“Wallahi ammi… Da …gaske…nake….kullum haka suke mana…wasu sun girmi kawu nanu amma duk yan iska me…ni wallahi ammi banason talla…” Ta karasa maganar ta cikin matsanacin kuka, ahankali ammi ta zauna kan Dan kujeran dake gaban ta tayi tagumi Kawai sai ta fara hawaye,

“Ya Allah.. Gamu gareka…ga yar marainiyarka gareka…ya rabbi kar ka bari a cutar da yar marainiyarka….” Tafada cikin kuka, kallon dija dake hawaye tayi Sannan tace

“Dija…inda nasan yanda zanyi da ko kadan bazakiyi tallaba…amma ke kanki kinsan halin da muke ciki… Kin koshi da taliyan da kika CI?…” Ammi ta tambayeta, cikin kuka ta gyada mata kai alaman AA,

“To kin gani…dukda tallan da kike ba koshi muke ba…kiyi hakuri …wata rana sai labari…” Ammi ta fada cikin kuka, dija Dan turo baki ta kara tana cewa

“To ammi ki yiwa inna ladio magana mana ko zata samo min gidan aiki a birni kaman yanda Ladidi takeyi….” Idanuwa ammi ta zaro,

“Allah ya sauwake…ban yarda kije aikatau….ke Kawai Allah ya rufa mana asiri..Kuma kar ki yarda wani ya taba koda akaifanki ne balle jikin ki…kina jina?…” Ahankali ta gyada mata kai ta Kara cewa.

“Nidai ammi..nafison…” Sallama wasu age mate dinta yasa tayi shuru Bata karasa maganar da tayi niyyan fada ba, yan fura2 ne kusan su takwas suka shigo Dan karamin gidan

“Kam yau anci saa kin shirya baki tsaya bata mana lokaci ba…” Inji daya daga cikin yanmatan, hararanta dija tayi

“To uwar iyayi…” Inji dija, ammi Dora mata furan tayi tana cewa

“Kar ki manta abinda NA fada maki..kinji?..”

“To ammi…” Tafada Sannan suka fita daga gidan, daman da akwai wani mai motan dake daukan su daga kauyansu zuwan cikin garin daura dake jihar katsina. Ammi daki ta shiga, nima binta dakin nayi, ina ganin yanayin rayuwarsu nace alhamdulillah Allah dai yasa babu wayanda ke zaune a irin wannan gidan a zahirin rayuwa don their life is low beyond words, tagumi ammi tayi tana tunanin yaushe wahalan su zai kare don kullum gani take kaman is getting worse, gashi yaranta hudu Kuma dija ce babban cikin su,

“Hmmm..ya rabbi ka tausaya mana…” Tafada tana Dan mikewa kan tabarman dake kasan dakin da ko cement babu.

A chan wani bangare NA Kano kam wani gida ne cike ana ta bude akwatuna da alaman lefe aka kawo, duk wacce ka gani kasan yan Hutu ne don every body around is glowing kaman  babu wahala cikin duniya.

“Amma wannan kayan sun hadu da yawa..kayan kaman na mata biyu?..” Inji wata mata, Dariya Matan wurin suka saki Sannan daya daga cikin su tace

“Ai yanda mutum yake hakan komai nace yake…baku ganin yanda diyar tawa take kaman ita tayi kanta?…” Inji wata mata, guda daya daga cikin su ta saki don murna,

A daya daga cikin dakunan gidan kam wata beautiful lady ce zaune kanta babu headtie sai yanmata biyu zaune kusa daita sai hira suke, da alaman lefen ta aka kawo,

“Kinsan wallahi sai kin bani wannan swiss lace din…tunda an kawo maki uban kaya…” Inji daya daga cikin yanmatan dakin, wacce akayiwa magana Dariya ta saki Wanda yasa hakorin Makkah dake bakinta ya bayyana,

“Dan wannan babu case…” Shuru tayi ta kalli wayanta daya fara ringing, murmushi ta saki tana dauka wayan, yanmatan kallon juna sukayi suna cewa

“Halan angon ne?…”

“Yes…babyna ne…” Tafada tana picking wayan,

“Baby…” Ta fada cikin sexy voice, daga Chan bangaren aka saki murmushi, wani saurayi ne zaune a office, yana Dan buga pen dake hannun shi ahankali kan desk dake gabanshi, yana jin muryan Mufida ya ajiye pen din tare da yin mika Sannan yace

“My angel ya kike?…”

“Lafiya lau…ya kake ya rayuwa?..”

“Alhamdulillah… An kawo kaya ko?..” Ya tambayeta in a low voice

“Yes baby….is so beautiful…” Tafada cikin whisper, Dariya yayi yana biting lip dinshi ahankali Sannan yace

“Not as beautiful as you…ai in ma shigo Kano sai NA kara kai personal shopping.. Kayanda babu idanuwan da zai gani sai ni kadai…” Murmushi mufida tayi tana sauraron yazid cikin so da kauna,

“Is that necessary?..” Ta tambayeshi ahankali,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button