BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

     *_????BAƘAR INUWA....!!????_*
               _{Gara rana dake}_
   *_Bilyn Abdull ce????????_*

Da sunan ALLAH mai ramahama mai jinƙai

Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki, ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni da al’umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Yanda muka fara lafiya ALLAH yasa mu kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali????????.

Ya rabbi ka gafartama mahaifina, ka ƙarama iyayena biyu mata da suka rage lafiya mai amfani.????????????

Littafin BAƘAR INUWA ƙirƙirarran labarine da baida alaƙa da kowa da komai. An yisane domin faɗakarwa, nishaɗi, ilimantarwa, harma da ban haushi ta wani sashe. Dan haka a wannan gaɓar ina son jan hankalin mai karatu, yayma kansa adalci yayma marubuci adalci.

A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi. Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili, ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba. Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi daban-daban, addinai daban-daban, yaruka daban-daban. Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za’a fahimceni

Banyi wancan dogon bayanin bane dan na canja kowa, nayi ne kawai dan ya zama dai-dai da fahimtar ka a ƙwaƙwalwarka da tuntar da kai wanene MARUBUCI a taƙaice. Domin kuwa KOWA masoyin Bilyn Abdull ne, amma bai zama kallai ita ta zama abin SON kowa ba.☺️

Alhamdulillahi ZAFAFA BIYAR sun sake dawowa gareku da sabbin salo daban-daban. Muna fata ALLAH ya baibayemu da alkairinsa mu da ku dake tare da mu. Sannan muna roƙon wanda ma basu tare damu, kodan sauke haƙƙi kuzo dan ALLAH ku saya da kuɗinku badan zamu iya furta kalma mara daɗi gareku ba. Dan kuwa koda wasa bama fatan jifan wani ɗan uwanmu musulmi da kalmar (ALLAH ya isa akan littafi). Masu saya ku fitar, dan girman ALLAH kuji tsoron ALLAH. Badan mu ba, badan mun isa ba. Kuyi haƙuri ku daina aikata mana hakan, domin UBANGIJI ya hana zalunci a tsakaninmu.☺️????????

Masoya kumuje zuwa, domin kuwa yanzu za’a far share filin wasan, dan wannan karon tafiyar ZAFAFA ta dabance????⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️.


Episode 1

………….Tafe yake tamkar iska zata kwasheshi ya faɗi dan sauri. Yayinda yake ƙananun surutai kai kace sabon kamune a hauka. Ya sake cin tuntuɓe a karo na biyu, sai dai cikin sa’a ya dafe bangon gwaguyayyen gidansa saɓanin ɗazun da sai da ya kai ƙasa. Dogon tsaki yaja zuciyarsa na sake hasala da kumbura har cikin maƙogwaro. Cikin son huce haushinsa da takaici yasa ƙafa ya daki murfin gidan na sa da duk ya cinye da tsatsa tsabar daɗewar da yay, dan tunda aka gina gidan banajin an taɓa sauya ƙyauran saboda koɗewa da ciccinyewar da yay na tsatsa tamkar tsohon drom ɗin ƙarfe.
Ball ya fara da butar da ke a farkon shigowa, inda alamu suka nuna toilet ɗinsu ne a wajen. Ta tafi ta daki ƙarshen bango, murfin yay gefe itama tai gefe.
Baba Nafi da ke alwalar magrib ta ɗago kai cike da nutsuwa da sanyinta ta dubesa. Sai kuma ta maida kanta ƙasa saboda uwar hararar daya zuba mata kai kace idanun nasa zasu zubo ƙasa ne.
“Kowanne shege da ke gidan nan ya fito!!”. Ya faɗa a kausashe yana dukan langa-langan da aka zagaye saitin inda yake tsaye matsayin kitchen ɗin girkinsu.
Cikin takaici da haushi aka bankaɗe labulen ɗakin tsakkiya, “Kai ko malam ka dinga sassauta ma zuciyarka mana dan ALLAH!, da wannan farar magriban da kowa ke ƙoƙarin kai abincin buɗa baki bakinsa maimakon a ganka bayan liman kana shirin gaida UBANGIJI sai ka lalace da neman masifa da tijarar hana iyalanka su susha ruwa cikin salama kamar yanda ka hana kanka?”.
Fici-fici yay da ido yana duban ta cikin ɓacin rai. Ya tattaro duka takaicinsa da damuwa zuwa cikin baki. Nunata yay da ɗan yatsa yana karkaɗa hannu cikin gargaɗi. “Larai ina rabaki da tararmun numfashi idan ina magana amma baƙya kiyayata. Na rantse miki da ALLAH idan ban sauke dukanin abinda na kwaso bisa kanki ba kice ba sunana DAUDA jikam mai ɗan-wake ba.”
Baki ta taɓe da sakin labulen, sai dai bakinta bai mutuba. Da ga cikin ɗakin take faɗin, “Can kaji da fitinarka ba’a kaina ba. Baka sauke haƙƙin bani abinda zanci a cikin wata mai falala ba bazaka sauken gangar ɗan bazakuɗa ba. Kai da ka kwaso abarka can ta ƙare maka ba Larai ba.”
Duk da ya jiyota sai bai tanka ba, ya cigaba da ƙwala shelar kiran kowa yazo gabansa. Shiru babu wanda yay tari tamkar kowa ya mutu a gidan. Wani ƙududun takaicin baƙin ciki daya taso masa daga tsakkiyar zuciya ya jawo da ƙyar zuwa maƙoshi ya fesar ta baki.
“Eh lallai ta tabbata an gama maidani ɗan iskan ƙasan gada, yo banda ana ɗaukata girman fadar karuwai harni dake amsa sunan maigida a gidan nan zanzo ina magana ku barni ina ɓaɓatu ga ƙwalon shege haihuwar tasha ko?..”
“Kayi haƙuri malam mudai salla muke wlhy, suma kuma nasan…..”
Wuff Larai tayo waje tana gyara zaninta dake neman ɓallewa saboda tsabar sauri, cikin harziƙowa ta tare numfashin baba Nafi mai maganar cikin sanyi da rashin son hayaniyarta “To annamimatu kinsan me? To muma sallar muke sai a maida sherin da ake son ƙulla mana cikin ciki ko?”.
“ALLAH sarki Larai nima ai abinda zance masa kenan bawai wani abu daban ba”. Baba Nafi ta sake faɗa a sanyaye.
Baki larai ta taɓe da juya ƙeya ta tura kallabinta disko gaban goshi, daddagaggiyar ƙeyarta ta bayyana. Murmushi kawai Baba Nafi tai da girgiza kanta ta ɗauke idonta gareta.
Duk abinda suke yana tsaye sai faman kumbura yake da harar ɗakin ƙarshe da ke jerin nasu baba Nafin. Sai dai baice uffan ba. Kusan mintuna biyar aka ɗaga labulen ɗakin aka fito. Mace ce ƙyaƙyƙyawa da bazata gaza shekaru talatin da biyar ba zuwa da bakwai. Daka ganta kaga ƴar duniya bugun farko. Sheƙeƙe ta dubesa shi da matan nasa ta watsar tana taunar chewing gum tamkar ba azumi aka kai ba yanzun nan.
“Wai Lafiya kaketa faman shela da farar magriba ko ruwa bamu kai bakinmu ba? Haba yadai kamata asan da da yanzu akwai banbanci, dan da kana juyamune muna haƙuri da tujaranka saboda kanada uwar kuɗinka a ƙugu, amma yanzu baka barinmu da cikinmu da hidimar ƴaƴanmu ka kuma haɗa mana da tijara da gadara BAƘAR INUWA……”
“Asabe! yanzu nan nine baƙar inuwar?”.
“Na tsakkiyar jeji ma kuwa, har gwara RANA DA KAI”.
Wata shegen dariya Larai ta bushe da shi, ta callara guɗa tana duban Asabe. “Kina birgeni amarya, idan mu latsamu a tauna baida wahala ke ai kin wuce kanwar lasa”.
Baki Asabe ta taɓe ta ɗauke kanta gefe. Wani irin ƙududun baƙin ciki ya sake kume Malam Dauda. Ya nisa tamkar bajimin sa dake a ganiyar tozon girma yana ballama Asabe ƙarfen ƙafarsa harara. Shikam ai auren bariki bai masa rana ba. Fuska ya sake tsukewa yana kai hannu ya kaɗo mutsiyar tuƙin tuwonsu dake rataye jikin kwanon kitchen ɗin.
“Matsalar mutum ce wannan kuma. Ina son naji wane shege ne tambaɗaɗɗe yaje wajen Jabiru mai shago ya amso lemon kwalba da cin-cin ɗin da matarsa keyi yace injini?”.
Kallon-kallo Nafi da Larai suka shigayi, sai dai komai babu wadda tace tunda sunsan shima yasan wadda zata iya wannan aika-aikar ai. Kuma shine ya bata wannan dama ɗin tun tana amarya, gashi yanzu tsahon shekaru goma sha bakwai har ƴan matanta na yawo galla-galla a gidan harsu huɗu komai ya gagara canjawa……
“Wai ba magana nake ba ne? Ko sai na maida ƙasan gidan nan zuwa sama ne!!?”.
Malam Dauda ya faɗa a matuƙar tsawace tsabar hasalar da zuciyarsa ke sake masa na baƙin cikin bashin da aka cimasa bayan baida ko sisi dana sharesan da akai yana magana. Nanma babu wadda ta tanka sai ƙarar taunar chewing gum ɗin Asabe kawai dake tashi ɗas-ɗas…

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button