NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 41-50

 

Katse wayar Sadeeq yyi jin bata ce komai ba, ya sake kiranta a tunaninsa network ne, bayan ta daga tayi masa sallama, amsawa yyi yace “Is ur network fluctuating?” A hankali tace “Ina jin ka yanxu” yace “Ohk, Cewa nayi when xan xo in gaisa da Umma if possible har da matata kinga shkkn ta samu Umma a garin Abuja ita ma, cos she have no body here” Khadijah ta wara ido tace “Lah, are you married?” yace “Sure, kusan 3 months kenan” murmushi sosai Khadijah tayi tace “Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya” yace “Ameen thumma Ameen, to yaushe xa mu xo?”  Khadijah tayi murmushin karfin hali tace “In dai kuna da time, kar ku ma ta gan ni tayi wani tunanin daban fa” dariya sosai Sadeeq yyi yace “Noo, she’s understanding, kawai daga few months da aure sai ta sa abu a ranta don ta gan ki, ba ma yar Nigeria bace, so she won’t think like them in sha Allah” Khadijah tace “Yar ina ce?” Yace “She is an Ethiopian” Khadijah ta wara ido tace “Kace bata jin Hausa kenan” yyi dariya yace “Noo tana ji ba laifi, ai tana xuwa hutu gun aunt dinta a Katsina sai dai tana dadewa bata xo bane, but she speaks English well” Khadijah da ke ta murmushi tace “Maa sha Allah, I will love seeing her” Sadeeq yace “Toh ko ki shirya da ‘yan gidan ku sai in xo in dauke ku, she will be very happy don bata da kowa, though shekaranjiya dai wata frnd din mum dinta ta xo daga can kasar ta su, yanxu haka ma tana gidana, but ita ma nan da kwana biyu xata wuce” Khadijah ta langwabar da kai tace “Allah sarki, to yaushe xaka xo ka kai mu, amma ni dai ina tsoro fa” dariya Sadeeq ya dinga yi yace “Tsoron me? Na fa ce maki she is not like you people in Nigeria, I can even tell her you are an old time frnd, idan kinyi insisting kina tsoro kuma sai in ce ke yar uwata ce” Khadijah tace “Haka dai ya fi” Sadeeq yace “Dubeta matsoraciya, idan na aureki na hada ku fa?” ta d’an hade rai tace “Ni ance maka aure xan yi yanxu” yyi murmushi yace “Mayar da wukar wasa nake, nima baxan iya handling two wives ba ai” murmushi kawai khadijah tayi, yace “Tun da gobe Monday xan xo da yamma sai in dauke ku, sai ki sanar da umma” Khadijah tayi shiru don bata son fashin islamiyya, can tace “Toh shi kenan Allah ya kai mu” yace “Ameen Khadijah, bari in bar ki kiyi bacci, sweet dreams” tace “Toh nagode bye” daga haka ya katse wayar, Khadijah ta sauke ajiyar xuciya jin Sadeeq yyi aure, thank God baxai shigo rayuwarta bane ya dame ta, duk da can kasar xuciyarta tana ganin girma da darajar abinda yyi mata a lkcn tana Katsina, he really helped her don da ba don shi ba kilan idan yunwa na kissa da ya kasheta, murmushi tayi ta koma ta kwanta tana rufa twins dinta da duvet, matar da yace ya aura ce ta fado mata, toh Allah yasa sa’arta ce ko xata samu warce xa su dinga xumunci sosai da, don ta gaji da rayuwa daga ita sai Nanny da boys dinta bata da kowa, Aysha dama kawai a makaranta kadai suke interact, Har ranta taji hankalinta ya kwanta haduwa da Sadeeq, ko ba komai dai akwai wanda ya santa ta san sa a Abuja yanxu sai dai fa bayan sudais bbu wanda xata sake bata lkcn ba labarinta gaskiya, its not as if Sadeeq didn’t deserve to knw her story but maimaitawan xai dinga fama mata ciwon da take healing a hankali na xuciyarta, da wannan tunane tunanen bacci ya dauke Khadijah, da asuba bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduma tana azkar dinta Nanny ta shigo dakin da sallama, gaisawa suka yi tana kallonsu Sudais tace “Basu tashi cikin dare ba neman tea” Khadijah ta girgixa kai tace “A’a…” Nanny tace “Toh kafin dai ki gama shirin makaranta na san sun tashi, sai kiyi masu wanka, ni kuma xan tafi in hada breakfast yanxu” Khadijah tace “Toh” daga haka Nanny ta fita dakin, khadijah na fitowa daga wanka wajen karfe shidda da minti arba’in ta ga yaran xaune kan gado duk sun tashi, wara masu ido tayi ta nufesu ta durkusa tana murmushi a hankali tace “Good morning boys” kicin kicin suka yi da fuska suna kallonta kamar Aliyu ya hade rai, dariya hakan ya bata, tace “Toh bari in maku wanka sai ku tafi wajen nanny” daga haka ta koma bathroom din tana daure da towel ta hada masu ruwan wanka ta dawo ta dauke su gaba daya suka shiga bathroom din, a dakinta ta gama shirya su kafin ta tafi parlor da su nan Nanny ta sa tayi feeding dinsu, sai kusan karfe bakwai da rabi Khadijah ta gama shirin tafiya makaranta, tana isa bakin kofa ta juya tana kallon twins da suka bi ta da kallo, kamar hadin baki suka daga mata hannu a tare murmushi tayi ta daga masu ita ma sannan ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Sadeeq ya kirata, bayan sun gaisa yace “xan taho yanxu Khadijah, am done for today a office” khadijah da ke dama ma su Sudais golden morn a parlor tace “Toh muna jira, Allah kawo ka lafiya”  Tana gama ba ma yaran abinci tayi masu wanka ta shirya su cikin kayansu iri daya, sosai yaran suka yi kyau da kayan da ta sa masu, ta fiddo kayan da xata sa kenan Sadeeq ya kirata, daukan wayan tayi ta daga ta kai kunne yace “Am outside Khadijah” ta xaro ido tace “Toh don Allah yi hakuri, minti goma pls” yace “Alryt then, ina jira” a hanxarce Khadijah ta shirya sannan ta sa Hijab dinta har kasa kamar yanda ta saba, ta fita gun Nanny dake wankin kayansu shureim a bathroom dinta, ta tsaya daga bakin kofa tace “Nanny xa mu d’an fita da twins amma baxa mu dade ba” Nanny tace “Toh shkkn Allah ya kiyaye, amma kar kuyi dare kin ga yamma yyi” Khadijah tace “In sha Allah” daga haka ta fita ta shiga nata dakin ta fito tare da yaran, gabanta sai faduwa yake kar su ce baxa su bi ta ba, Har bakin kofa nanny ta rakasu tana daga ma yaran hannu su ma suna daga mata, tun kafin su iso motar Sadeeq ke kallon yaran, kawai ya bude motar ya fito yace “Waow, cute boys, ur siblings?” Khadijah ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai daukansu yyi da daddaya da daddaya ya masu kiss yace “How are you boys” Kallonsa kawai yan biyun ke yi, ya bude front seat yana kallon khadijah yace “Toh shiga” tana shiga motar ya mika mata yaran gaba daya ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da suka hau kan titi yace “Ya sunan twins din?” Khadijah tace “Sudais and Shureim” yace “Maa sha Allah, they are handsome, but step siblings din ki ne su koh?” dariyar karfin hali Khadijah tayi tace “Uhm” yace “That’s nyc” yace “Har na sanar ma Shaheedah xuwan ki, she is so happy” Khadijah tace “Da gaske” yana murmushi yace “Sure” tace “Allah sarki” nisa ne sosai da gidan Sadeeq don sai kusan karfe biyar da wani abu suka isa gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, bayan yyi parking yace “Welcm to our home Khadijah” murmushi kawai tayi ta bude motar ya xaga ya taimaka mata sauke yan biyun kasa sannan ta fito ta rufe motar, wata kyakkyawar mace ce da baxata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta fito balcony din gidan, fara ce  doguwa mai kyan gaske, ta karaso gun motar tana murmushi sosai tace “Sannun ku da xuwa bak’in mu” Khadijah dake ta kallonta tayi murmushi tace “Yauwa sannu” wara ido matar tasa da ya kira da shaheeda tayi tana kallonsu Sudais tace “Maa sha Allah, dear they are sooo cute” daga haka ta tsugunna ta jawo yaran jiki tace “Welcome boys” Khadijah ma sai kallon yaran nata take ganin sun ki ko da murmushi, Sadeeq ya dau Sudais yana murmushi yace “Lallai boys din nan sun iya miskilanci” Shaheedah ta dau Shureim tana dariya tace “Mu shiga ciki toh” daga haka ta fara tafiya Sadeeq ya kalli khadijah yace “Mu je” bin bayan shaheedah tayi ya bi bayanta yana rungume da shureim.

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button