Labarai

Kotu ta yanke wa Sifeto-Janar na Ƴan Sanda watanni 3 a gidan yari

Kotu ta yanke wa Sifeto-Janar na Ƴan Sanda watanni 3 a gidan yari

 

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Talata ta yanke wa Sufeto-Janar, IGP, na ƴan sanda, Usman Baba, zaman gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zargin kin bin umarnin hukuncin da wata kotu ta yanke na kin mayar da wani jami’in dan sanda, Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritaya ta ƙarfi da yaji bakin aiki.

 

Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Okoli, Arinze Egbo, ya shigar, ya kuma gargadi Baba kan rashin bin hukuncin da kotun farko ta yanke a baya.

 

Mai shari’a Olajuwon ya yi gargadin cewa idan Sufeto-Janar din ya kasa wanke kansa daga laifin ƙin bin umarnin kotu, to za a sake daure shi na tsawon watanni uku a gidan yari.

 

Mista Okoli, a cikin wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/637/2009, ya kai karar IGP ne a matsayin mai shigar da kara a cikin lamarin.

 

Mai shigar da karar, wanda ya roki kotun da ta bayar da umurnin a dawo da shi bakin aiki, ya ce majalisar ‘yan sanda wacce a halin yanzu ake kira da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, PSC, ta yi masa ritaya ta dole ba bisa ka’ida ba a shekarar 1992, a lokacin da ya ke rike da mukamin cif sufritenda na yan sanda na jihar Bauchi da dai sauransu.

 

Ya ce ritayar da ya yi ta dole, a karkashin doka ta 17 na 1984, haramtacciya ce.

 

Mai shari’a Okorowo, a hukuncin da ya yanke a ranar 21 ga Oktoba, 2011, ya ba da umarnin tilasta wanda ake kara (IGP) da ya aikata wannan umarni kamar yadda doka ta tanada.

 

Ya umurci IG da ya bi umarnin hukumar PSC, kamar yadda ya ke kunshe a cikin wasikar su ta ranar 5 ga Mayu, 2009 (tare da Ref. PSC/CSP/01/11/295A), inda ya umarce shi da ya mayar da Okoli cikin ƴan sandan Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button