LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Jan numfashi liman yayi da kallan malam jauro yace. “Na gyara mai karayoyin dake jikinsa. Gashi nasaka mishi magani a raunukan nashi. Allah yasa a samu kansa nan da kwana biyu..
Da sauri MUSLEEMA ta katse liman da cewa. “Babba yana da rai koya mutu.
Murmushi duk sukayi yace mata shi yace da ita. “bai mutu ba MUSLEEMA..
Malam jauro yace. “Nasa Suleiman yaje can cikin garin na gwambe ya kira ɗana Usman. Dan naga kamar saiya saka hannu cikin lamarin ciwan nasa..
Gyad’a kai liman yayi da cewa.. “Ya kamata kam. Kan malam jauro yayi wata magana saiga Usman ya shigo da sallah shi da Suleiman d’in..
“Kaga yanxu muke maganarka nake gaya musu na tura Suleiman ya kiraka kaduba mana Wannan bawan Allahn..
“Eh had’uwa mukayi dashi ahanya dan nima nan na nufo dubaku. Sai yake gayamin wai dama guna zaizo dan kana san nazo na duba wani Mara lafiya..
“Ni na manta ma yau qarshen wata Yayi ranar zuwanka. Ka ganshi nan Mara lafiyan matso ka ganshi dakyau..
Duba na tsanaki Dr Usman yakema ADAMS yana jin mamaki cuwukan dake jikinsa..
Can ya kalli malam jauro mahaifin nasa yace. “Wannan fa Sai an kaishi asibiti dan maganin gida bazai gamsheshi cikin sauri ba.
Dan haka ya zama lalle yau na kuma saimu tafi tare daku dan kuji binciken da za’ayi akansa.
Liman yace.. “Wannan ai ba damuwa. Jeka duba umman taka ka fito muje.
Tashi Dr Usman yayi yashiga can cikin gidan malam inda mahaifiyarsa take. Anan take bashi labarin yanda aka damu Adams. Usman ya tausayama Adams sosai. Hakan yasa zuciyarsa takasa nutsuwa.. Dan haka sai kawai yay ma Mahaifiyar tashi sallama ya fito. Daidai lokacin da liman ya fito daga gidansa dan gayama iyalinsa. Haka suka saka Adams a motar Usman d’in. Liman da malam jauro suma suka shiga motar MUSLEEMA tace zata bisu. Daqer suka lallasheta kana Usman ya jasu basu zame ako ina sai’a ba sai’a cikin garin gwambe cikin asibitin DOCTOR AHMAD…
Anan aka shiga duba lafiyar Adams lungu da sak’o.

Bancike ya nuna TUNANIN ADAMS YA D’AUKE.. Bashi ba tuna wani abu daya faru dashi arayuwa. Sai in yaqa wani nasa ko an ambaci wani abun daya sani wannan ne kawai zai iya sawa asan shi asan daga inda ya fito..

Kasancewar daga cikin garin gwambe zuwa rugar malam jauro akai tafiya me d’an nisa. Sai kawai liman da malam jauro suka tare a gidan Usman danshi ya buqaci dasu zauna kasancewar ana saka ran marfad’owar ADAMS d’in nan da kwana biyu..
Dan yana jiye musu wahalar da zasu sha wajen dawowa idan suka koma gida
Hakan yasa suka yarda.

Anan ko Ruga MUSLEEMA tana cikin wani hali. Dan tunanin Adams ya damu Zuciyarta. Haka kawai taji tana sanshi tana qaunarsa tana tausayinsa.
Yawo na lura da ita. kallanta kawai takeyi dan itama Adams d’in ya bala’in shiga ranta..
Gani take kamar shi d’in jininta ne..

Kwanan Adams hud’u a asibitin ya farfad’o. Saidai kamar yanda binken ya nuna ya manta komai na rayuwa akansa. Hakance ta kasance..
Malam jauro ko sai tambayarsa sunansa yake. Ido kawai Adams yake binsa dashi.
Usman yayi murmushi yace.. “Angayama Baffa tuninsa ya d’auke yanxu ba abinda zai qara tunawa arayuwarsa sai in yaga wani nasa kutunna.

Kwana d’aya su malam jauro suka qara sukace ma Usman zasu koma Ruga dan Allah ya kula da ADAMS kamar jininsa zasu dinga zuwa duk qarshen sati suna dubasa.
Nan yabasu tabbacin zai kula dashi kamar yanda zai kula da kansa..

Dasu malam jauro suka dawo gida Yawo da MUSLEEMA sunzo sun tambayesu ya jikinsa..
Nan liman yake gayama Yawo ga matsalar da shi Adams ya fuskanta na d’aukewar tunani..
Da tausayawa Yaro tace Allah ya dawo mai da tunanin nasa nan kusa.

Saiya kasance kullum Idan MUSLEEMA tazo karatun asuba gun Malam jauro saita tambayesa jikin ADAMS
Tun yanace mata jiki da sauqi harya gaji da amsa mata..
Dayaga tafara zuwa da ranah da yamma tana tambayarsa
Saiya fara d’aukarta duk sanda zasu duba Adams d’in shida Liman.
Hakan ne yasa hankalin Musleema kwanciya. Dan tana ganin Adams d’in yana samun sauqi sosai.

Yau malam jauro ya shirya shida liman suka nufi cikin garin na gwambe lokacin watannin ADAMS bakwai Usman na lura da lafiyarsa su kuma suna masu zuwa dubasa.. Adams ya samu sauqi sosai..
Ba abinda yafima Malam jauro dad’i da kulawar da Usman yabama Adams d’in sai ganin yanda ADAMS din yake amfani da ilimin addinin da Usman d’in ya bashi.
Sallarsa anitse. Komai nasa dakeyi a nitse yakeyi.
ADAMS yafi gane yaran Hausa dan shi Usman yafi masa ba fullanci ba.
Dake dama rugar malam jauro had’akata ce. Ana jin Hausa ana jin fillanci. Hakan yasa su malam jauro jin dad’in yanda ADAMS din yaji hausa.
Usman yace da mahaifinsa malam jauro yasama ADAMS suna Ahmad kasancewar basu san sunansa ba. Sunji dad’in sunan dan haka suma sukace da sunan zasu dinga kiransa.
Haka suka dawo da ADAMS cikin Rugar malam jauro suna masu yimai addu’a akan Allah ya dawo mai da tunaninsa Susan daga inda ya fito..

Saidai da suka dawo MUSLEEMA taje tasama malam jauro daru kan saiya bata Yayanta Ahmad ya koma gidansu..

Murmushi yayi da kallanta yace idan naba Yawo shi a’ina zata sashi.
Tace ai akwai d’akuna agidansu tashare ko’ina duk inda ya zab’a anan zai zauna..
Da farko malam jauro yaso qin yarda Amma dataje tasa Yawo agaba da kuka dole Yawo tazo ta ruqi malam jauro yayarda Adams ya koma gidansu MUSLEEMAT

Abin yama MUSLEEMA dad’i.. Dama shima Adams baya san nesa da MUSLEEMA.
Saboda tun lokacin dasu malam jauro suke zuwa da ita dubasa ya lura da qaunar da take masa.
Hakan ne yasa yafi sakewa da ita fiye dasu su malam jauro d’in..
Saboda yanda take da dad’in hira Gashi Yana tsintar kansa cikin nisha’i idan Yana tare da itan..

Sosai itama Yawo taji dad’in yanda ADAMS ya dawo gidan nasu..
Yana zuwa gun malam jauro d’aukar karatu da safe da yamma idan ya dawo kuma ya shiga daji cikin awaki yana dubasu.
Tunda ya fara kula da dabbobin nasu Sai Yawo taga kamar yafi kowa iya kiwo
Dama ya hutashar da MUSLEEMA dan yanxu bata zuwa ciwan..
Dan Idan kaganta a wajen ciwan to taje hira da yayan nata Adams ne wato Ahmad kamar yanda suke kiransa dashi….

Sha kuk’uwa me tsanani tashiga tsakanin MUSLEEMA da ADAMS


Malam jauro ne da liman amininsa da Yawo da d’ansa Iro da MUSLEEMA suke zaune kan tabarma a kofar gidan malam jauron..
Malam jauro yace.. “Dama abinda yasa na taraku magana nake san nayi daku akan alqawarin Auran dake kan MUSLEEMA da d’ana Iro ganin da nayi Yanxu takai shekarunta na Aure..
Murmushi Iro yayi dan shi aduniyar nan ba wacce yake so kamar MUSLEEMA. Yana mata wani mugun so wanda shi kansa bazaice ga ranar daya soma yi mata shi ba.
Dan ya dad’e da santa aruhinsa shine ma ya gayama mahaifin nasa yana Santa har dai alqawarin Auran nasu ya hau kansu shi da ita.
Jan numfashi Yawo tayi da cewa. “Ai wannan ba matsala bane malam. Yaran nan duk naka ne. Kawai asaka ranah ayi musu auran babu wani damuwa..

Murmushi jin dad’i malam jauro yayi da kallan MUSLEEMA wacce taturo baki gaba yace da ita. “Lafiya dai y’ata kike turo baki ko aran ne baki so.
Da sauri ta d’aga mai kai.
Yaci gaba da cewa. Toh meyasa baki so.
Cikin zubar hawaye tace.. “Ni Wallahi malam bani san Iro ni YAYANA nake so..
Gyara zama malam jauro yayi da cewa.. “Waye yayan naki..
“YAYAH Ahmad mana….
Saurin bige mata baki Yawo tayi dayi mata dak’uwa tace. “Saiki mutu dasan nashi aranki ai. Aure dai tsakaninki da Iro sai anyi. Ni dama nasan ba banza ba kika ninema Ahmad d’in nan tun ran farko…
Aiko dajin hakan MUSLEEMA tafashe da kuka tana cewa.. “Ni wallahi YAYANA NAKE SO. Shi nake so..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button