LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Bayan sati d’aya ne Adams ya koma duk wani aikinsa. Inda yaci gaba da ɗora aya aduk inda ya tsaya..
NUFAISAT ji take kamar yanxu tafijin dad’in ADAMS.. Kodan kullum zuciyarta qara sanshi take ne????
TAUDHAT har yanxu bata dena shege ayarta da malamin nata ba.
Abin nata dai saici gaba yake.
Dan lokacin da ADAMS ya b’ace
Bama Alhazawanta dama tayi wany’anda tasansu tunkan auranta da ADAMS d’in..
Toh yanxu ma data koma gidan ADAMS d’in ji take aranta badena harka zatayi dasu ba.
Saidai zatafi bama malamin nata mahimmanci saboda maganin matan da yake had’a mata. Sannan yace mata karta kuskura tayi ciki da wani idan bashi ba. Dan idan tayi asirinta zai tonu..
Wannan yasa take ankarewa da duk waƴanda take harka.
ADAMS da aminin Dadynsa wanda ya tsinceshi sunje wajan daya tsinceshi sunyi binciken duniya mutanan qauyen dake kusa da d’an dajin sunce basusan ADAMS ba. Kuma baiyi rayuwa dasu ba.
Atak’aice dai wata d’aya Dadyn Adams dashi Adams d’in suka d’auka suna zagaye kaf qauyukan dake makwaftaka da wannan waje da wannan direban yayar da ADAMS suna bincikesu akan koya tab’a rayuwa awajensu..
Amman sam basuci karo da Wanda Yace yasan ADAMS ba.
Haka suka hak’ura suka barma Allah lamarin kan ya basu haske danshi kad’ai yasan meya faru..
Abin ya dami MUSLEEMAT da YAWO ganin basuga dawowar ADAMS awannan ranah ba.
Hakan yasa YAWO tafitta yawan nemansa ko wani abu ne yafaru dashi. Kasancewar ya faɗi baya jin daɗin jikinsa. Saidai neman duniyar nan ba inda YAWO bataje ba Amman kome kama da ADAMS bata gani ba.
Hankalin YAWO dana MUSLEEMA ya tashi mutuƙa da’aka wayi gari still ba batun ADAMS
Nan YAWO tayi gun Malam jauro takwashe komai tagaya masa.
Yayi mamaki matuƙa dajin batunta.
Hakan yasa liman yayi mai shela akan duk matan rugan suzo.
Babu ɓata lokaci nan take kowa ya hallara a fadar malam jauro.
Qarema jama’ar tasa kallo yayi tsaf yana nazarinsu sannan ya shiga basu labarin ba’aga ADAMS ba. idan da wanda yagansa yayi magana…
Nanfa waje ya hargitse da magana. Kowa faɗin albarkacin bakinsa yake. Masu salati nayi masu gwalma nayi masu jajantawa nayi.
Masu gwalma faɗi sukeyi.. Ai dama daga ganin Adams ba mutumin arziqi bane. Daga ganinsa wani abu yazo nema cikin rugar. Qila ya samu abinda yake nema d’in ne yasa shi gudu abinsa dan tsabar mugunta shi ba’asan inda yake ba. Ba’asan cikakken sunansa ba. Kawai dan gwaninta YAWO takama tabashi jikarta ya kunsa mata cikin yara uku aigashi ya tafi ya barta da tagumi..
Masu salati ko mamakinsa suka dinga yi dan basu zaci hakan daga garesa ba.
Masu jajantawa ko gani suke kodai wani abu ne ya faru dashi. Ko wani ne yasace shi.
Kowa dai da abinda yake fad’a..
Da Malam jauro yaga ba wanda yake da sani akan abinda yake san sani. saiya saka mutanansa kan suje su duba mai ADAMS d’in ko Allah zaisa adace..
Daga nan ya sallami kowa ya kama gabansa
Anan yaba YAWO hak’uri kan takwanatar da hankalinta insha Allah za’a gansa.
Da damuwa YAWO tadawo gida ta shidama MUSLEEMA yanda akayi..
Hawaye ne yaketa faman sauka akuncin MUSLEEMAN. Tana qaunar ADAMS tana san rayuwa dashi. Bata san wani abu ya rabasu. Haka tana fatan Allah yasa agansa..????
Har sati biyu ba’aga ADAMS ba..
Wannan yasa duk MUSLEEMA tashiga tashin hankali da damuwa. Kullum kuka take babu dare babu ranah. Tun YAWO na bata baki hardai ta hakura tafitta daga harkarta.
Dan ita YAWON ta d’auki zancikan da mutanan rugar suke fad’i nawai ya gudu ne ya barsu..Hakan ne yasa tanemi damuwar tata tarasa.
Lamarin MUSLEEMA fa yanxu yafara ba YAWO tsoro. Dan duk ta fige tafita a hayyacinta.
Kallo d’aya zaka mata kasan tana D’AUKE da matsananciyar damuwa…
Bata da wani furuci saina Ahmad wato Adams YAYANTA.
Musamman idan takalli kyawawan yaran data haifa dashi. Nan Zuciyarta take karyewa hawaye yata ambaliya afuskarta..
Yau ALHAMIS da misalin qarfe goma sha d’aya ne Iro ya nufi gidansu MUSLEEMA dan ya jajanta mata. Sannan ya d’an bar mata alama na har yanxu fa yana qaunarta.
Aiko yana zuwa ya tarar da ita a tsakar gidan nasu. Takama Yaranta tsam ta rungumesu sai baccinsu suke. Ita ko sai zubar hawaye take.
YAWO na gefe tana kwad’an latas..
Hankalin Iro yayi matuqar tashi da ganin MUSLEEMA. Baiyi tunanin zata saka damuwar ADAMS aranta haka ba.
Ta fige ta lalace kamar ba MUSLEEMAN daya sani ba.
Nan take zuciyarsa takarye. Tsoro ya kama zuciyarsa. Dan ya tabbatar idan taqara d’aukar lokaci ahakan ba makawa saidai azo a d’auki gawarta ta mutu..
Bakinsa na rawa ya gaisar da YAWO ta amsa da murmushi tana rayawa aranta dama shi MUSLEEMAN ta aura da yanxu duk wiya bazasu Shiga wannan tashin hankalin ba.
Gaskiya tausayin MUSLEEMA ya kama Iro. Wannan shine karo na farko daya tab’a aikata wani abu yaji bai kyauta ba arayuwarsa. Dan haka Ahankali ya qara tsaida idansa akanta yace.. “Nayi miki lefi MUSLEEMA. Najefa rayuwarki cikin wani hali. Na cutar dake saidai kafin na gaya miki ina san kiyafe min…
“Babu wani lefi da wani d’an Adam zaiyimin wanda bazan iya yafe masa ba. Iro koma me kamin na yafe maka. Dan ina ji ajikina nikam rayuwata tazo qarshe. Saboda nayi rashin abinda na kwallafa araina akansa. MUSLEEMA ta gayamai hakan da damuwa.
Jan numfashi yayi cikin tausayawa yace.. “Nine silar jefaki cikin wannan yanayi.
Nine na b’atar miki da mijinki uban y’ay’anki saboda na rikesa azuciyata tun lokacin dana bar mishi ke. Barin mishi ke danayi bana Allah bane awannan lokacin.
Nan Iro ya kwashe komai na yanda yayima ADAMS ya gaya ma MUSLEEMA da YAWO..
Hankalin su yayi matuqar tashi sosai.
Nan take YAWO tafashe da kuka wiwi.
Dama ita MUSLEEMA tunda yafara koro mata bayanin hawayenta yaqi tsayawa..
Da sanyin jiki iro ya qarasa durqusawarsa ga MUSLEEMA yaci gaba da cewa.. Wannan shine abin daya faru. Kuma shine abu na farko dana aikata arayuwata yanxu zuwa gareki naji ban kyauta ba. Dan Allah MUSLEEMA kiyafemin.
Rintse idanta MUSLEEMA tayi tace dashi. “Ka aikatamin abinda bazan iya yafe maka shi cikin sauri ba. Kajefa rayuwata cikin wani hali wanda bansan yazanyi ba.
Ka tarwatsa min Farin ciki na. Ka b’ata tunanina. Yanxu har yaushe kake tunanin zanga mijina uban Y’ay’ana..
Lokacin daka tashi aikata Wannan aika aikan naka meyasa bakayi tunanin yaran nan nawa ba.
Iro kacuceni karabani da FARIN CIKIN RUHINA. Ka rabani da LEEKITAN dake gyara ZUCHIYATA.
Saboda dashi ne nake samun nutsuwar ZUCHIYAR.
Yanxu ZUCHIYAR ta hargitse. Ta b’aci. Ta zaga zuwaga tunanina. Ta b’atamin tunanin.
Kasan yanda nake ji araina kuwa..
Ji nake ZUCIYATA nayimin zafi. Tana yimin wani suya. Tana yimin wani raɗaɗi. Ina tabbatar maka bazata dena yimin hakan ba har saina gamu da Yaya Ahmad. Ya gyaramin tunani..????
"Zaki gamu dashi MUSLEEMA. Dan garin KANO na tura shi. Kuma na gaya miki Sunansa LEEKITAN ZUCHIYA. Dan haka naji waƴannan matan sun faɗi... Iro ya katseta da faɗin hakan hawaye na zubar masa.
Jan numfashi tayi dace masa.. “Kaje nayafe maka. Tunda kabani sheda d’aya na sunansa. Badai kace sunansa LEEKITAN ZUCHIYA ba.
Yace “eh haka naji matan sunce..
“Kaje kawai.. Dan Wallahi d’aukewar numfashi ce kawai zata hanani zuwa garin KANO neman mijina.. MUSLEEMA ta faɗi hakan da goge hawayenta..
Dan sanyin jiki Iro ya tashi yabar gidan.. Yana zuwa gidansu ya gayama Malam jauro mahaifinsa shinefa silar b’acewar ADAMS. Ya kwashe komai ya gaya masa.
Ran malam jauro yayi matuqar b’aci… Dan har yaso yayima Iro d’in baki liman ya Shiga tsakani…
Dama shi malam jauro sam zuciyarsa bata yardar mishi ADAMS guduwa yayi ba.. Gashi ko gaskiya ta bayyana..
Nan ya taka qafarsa yaje ya tarar da YAWO da MUSLEEMAN ayanda Iro ya barsu. Sai subar hawaye suke.
Yaba YAWO hakuri sosai har sanda taji kunyarsa. Ganin babba dashi yana qoqarin durqusa mata.
Haka dai suka bar gidan shida liman zuciyarsu babu daɗi.