Al-Ajab

Magidanci ya cinnawa ƴaƴan matarsa wuta bayan ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama wani mutum mai shekaru 54 da haihuwa da laifin kona ‘ya’yan matarsa guda biyar a unguwar Fagun da ke garin Ondo.

 

Odunlami, Sufeto na ‘yan sanda, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, kuma ana kan binciken wanda ake zargin, yayin da kuma wadanda abin ya rutsa da su ke karbar magani a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo.

 

Sai dai wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa matarsa ​​wadda ita ce mahaifiyar yaran da abin ya shafa ta bata masa rai saboda ‘yar rashin fahimtar juna da suka samu.

 

Sai dai wata majiyar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne saboda matarsa ​​ta hana shi hakkinsa na aure.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button