Labarai

Matasa sun lakaɗa wa shugaban makarantar sakandare na-jaki bayan kama shi yana lalata da dalibarsa

Matasa sun kama wani mataimakin shugaban makarantar sakandare dumu-dumu yana lalata da dalibarsa, LIB ta ruwaito.

 

Mutumin wanda shi ne na biyu a matsayi a makarantar sakandare nan Kgagatlou da ke Polokwane, Limpopo ya ci na jaki bayan an kama shi yana lalata da dalibarsa yayin da wasu daliban ke karatu a azuzuwansu.

 

A wani bidiyo da ya dinga yawo a Twitter, sai da suka daure shi jikin ice sannan suka dinga dukansa kamar Allah ya aikesu.

 

An samu rahotanni kan cewa ba wannan bane karon farko da aka ritsa shi yana lalata kananun yara ba a makaranta.

 

An raba shi da wata makaranta ne inda aka komai da shi a matsayin mataimakin shugaban makarantar sakandare Kgagatlou.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button