BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

      *CHAPTER 1*

Ahankali yasanya hannu a handle ɗin ƙofan yamurɗa yashige, tana tsaye a gaban tanƙamemen gadonshi me tsananin kyau da burgewa, ganinsa ba ƙaramin tsorata ta yayi ba har batasan sanda tazaro ido waje ba tana kallon shi, shima ɗin ita yake kallo cike da mamakinta ganin yanda tafirgita lokaci ɗaya da ganin shigowar sa, hakan yasaka yatsaya yana kallonta na tsawon mintuna uku kafin yaɗauke kansa yaci gaba da takowa ciki cike da tafiyansa na ƙasaita, kai tsaye wajen gadon nasa yanufa ya’aje briefcase ɗin sa da rigan aikinsa asaman gadon, kana yataka  yashige cikin toilet, tana ganin shigewan sa tasaki wani wawan ajiyan zuciya me ƙarfi har da sanya hannu tana dafe ƙirjinta, dasauri tanufi hanyan fita tafice, kai tsaye inda ɗakinta yake tanufa jikinta har yana rawa, sosai tatsorata da ganin da yayi mata, fatan ta ɗaya kar yaɗaura ayan tambaya a kanta, kuma ta gode Allah da be ganta tana wani abun ba da yau kashinta ya bushe.

Kusan 20mint yaɗauka acikin toilet ɗin kafin yafito ɗaure da tawul a ƙugunsa, ɗaya kuma ya ɗaure sa saman kansa, jikinsa duk ruwa ke ɗiga, haka yaƙarisa tanƙamemen Mirror ɗin sa wanda aka cika gaban da kayan shafa kala da iri, zama yayi bayan da yawarware towul ɗin kansa yafara goge suman gashinsa da yake baƙinƙirin me yawan gaske, sai da yagama goyewa tas yabusar dashi kafin yasoma shafa wasu Expensive Lotions akan Black skin ɗin sa me kyan gaske, sai da yagama tas yagyara gashinsa yashafe shi da mayuka masu saka gashi ƙyalli da taushi, bayan ya gama tashi yayi yanufi wajen sip ɗin kayan sa yabuɗe yaciro wata farar riga me gajeren hannu da wuyan V, sai farar Three qweater me manyan aljihu, sai da yashirya tsaf yakoma gaban mirror yafesa tsadadden Parfumer’s ɗin sa me daɗin ƙamshi, yaƙara kallon kansa ba ƙarya ya haɗu sosai duk da shi ɗin me kyau ne, wayoyinsa yaɗauka yafito palow yana tafiya yana dannawa har yaƙariso saman luntsuma-luntsuman kujerun yazauna, ya ɗan jima yana latsa wayan kafin ya’aje yaɗau remote yafara sanja channels, akan CCTV NEWS yatsayar yasoma kallon labaran da ake yi, shi ba kasafai yake kallon fina-finai ba, yafison kallon labarai ko wrestling, Ringing tone ɗin wayan sa ne yasaka shi ɗauke idanuwan sa akan plasma ɗin yamaida kan wayan, kallo ɗaya yayi ma wayan yaɗauke kansa yaci gaba da kallon shi, sai da akayi mishi 2missed call be ɗaga ba, ana 3 ɗin ne yasa hannu yaɗau wayan ganin dai ba fasa kira za’ayi ba, kuma sosai kiran yake damun sa, hakan yasaka yayanke shawaran yaɗauka

“Ya dai?”

Yafaɗa hakan cikin cool voice ɗin sa yana me jingina bayan sa da jikin kujeran, jin muryanta ya doki kunnunsa yasaka shi lumshe idanu yana buɗewa

“My Ib da fatan ka isa gida lafiya?”

Ataƙaice yace “lafiya”.

Shiru ne yagibta a tsakanin su, hakan yasaka shi sake lumshe idanu yana jiran tasake magana, itama daga ɓangaren ta so take yayi mata wata maganar ko da irin tambayar da tayi mishi ne, cikin sanyin murya tace

“Dama na kiraka naji ko ka isa gida lafiya ne, sai anjima..”

Be bari ta aje numfashi ba ma yakashe wayan yana ajewa yaci gaba da kallon sa, sai kuma yaƙara ɗauka yalatsa yanemo wata Number yakira

“Kizo”.

Daga haka yakashe yasake ajewa, 3mint sai gata ta buɗo wani ƙofa ta shigo, ahankali tanufo sa taduƙa agaban sa tace

“Gani Sir”.

Idanun sa akan t.v yace

“Kihaɗa min tea kikawo min”.

“Tom”. Tace dashi tana miƙewa dasauri tanufi hanyar kichen, har ta kama ƙofar zata buɗe taji muryan sa ya ratsa cikin kunnuwanta

“Lubna”.

“Na’am Sir”. Tace hakan lokacin da tajuyo tana kallon sa

“Kibar shi kawai”.

Yana faɗan haka yamiƙe tare da wayoyinsa yanufi ɗakin sa, sai da taga shigewar sa tasaki ajiyan zuciya, shiru tayi tana tunani kana cike da sanyin jiki takoma inda tafito

Be jima ba yafito riƙe da keeys ɗin mota, ya sauya shigan sa cikin wata Farar t.shirt me dogon hannu da zanen cat ???? agaban rigan, sai dogon wando pencil blue colour, ƙafansa da Combat kalan wandon da ratsin fari, yana saka wrist watch a hannun sa yabuɗe ƙofan yafice, directly compound ɗin gidan yanufa yanufi wajen da yake aje cars ɗin sa, acikin wata kyakkyawar farar Mota yashiga yaja slowsly yanufi bakin  Gate, gateman na ganin shi yataso yabuɗe masa yafice, ahankali yake tafiyar hakan yasaka ya ɗau tsawon 30mint kafin yadangana ga wata tanƙamemen Gate, abuɗe yatarda Gate ɗin hakan yasaka yatura hancin motansa ciki, kai tsaye inda ake ajiye Motocin gidan yanufa yatsaya daidai setting wata Black cars, atare suka fito yayinda suka kalli juna suka sakar ma junan nasu murmushi, bayan ya rufe motan yataka yanufi wajen shi, tafawa suka yi suka cafke hannayen su

“Ya Bro”.

“Manya-manya iyayen mu, sai yau zan ganka?”.

Cewar Sameer yana kallon sa da murmushi a face ɗin sa

Ɗan shafa kansa yayi yace

“Uhmm Bro kenan Bara ka gane bane, aiki ne yayi min yawa fa”.

“Na sani ai ba sai ka faɗa ba, ku da kuke manyan mu”.

Smile kawai Khalil yayi be ce komi ba

“Ok muje ciki nima yanzu isowa ta kenan”.

Tare suka jera suka nufi hanyar da zai sada su da main Palow, Kai da ganin su kasan jini ɗaya ne su sabida tsananin kamannin su, sosai komi nasu yakasance ɗaya har ta da skin ɗin su, tsawo ne kaɗai Khalil yafi Sameer dashi, yayinda shi Sameer ɗin matsakaici ne kuma yana da ɗan ƙiba sosai.

Suna shiga da sallama matar dake zaune saman sofa ta’amsa musu, kallo ɗaya zakayi mata katabbatar da ita ce mahaifiyarsu bcoz tsananin kamannin da suke da juna, sai dai ita fara ce sosai saɓanin su da suka biyo Mahaifinsu

“Mom”.

Suka faɗa atare suna nufar inda take, Sameer har da ƙarawa da sauri yaje yayi Hugging ɗin ta yana sakar mata kiss a goshi, sannan yasami wuri gefenta yazauna yana ɗaukan Apple ɗin dake gaban ta cikin plate, sai da yagutsira yace

“Mom Afternoon”.

Lokacin da shima Khalil yaƙaraso yazauna ɗaya side ɗinta suka saka ta atsakiya, atare tashafo kansu tana murmushi tace

“Welcome My twinsies, nayi kewarku kwana biyu, musamman ma kai Autana”.

Taƙarisa maganar ta tana kallon Khalil da shima yakarkace kai yana kallonta, ƙara shafo kanshi tayi tana faɗin

“Ya aiki?”

“Alhmadulillah Mom”.

Sameer yace “Mom ni fa?”

Kallon shi tayi, da ido tatambaye shi mene?

“Naga kina kallon sa ne kina tambayansa banda Ni”.

“Oh to ai sai kajira nagama dashi ko? Ko kai ba Babba bane?”.

Ɓata fuska yayi yace “kullum haka kike cewa ai, dole sai kin nuna banbanci a tsakanin mu”.

“Kaima ai ban hanaka zuwa inda akafi sonka ba, sai kabari dai nagama tambayan Autana kafin nazo kanka”.

Murmushi yayi yace “Mom kenan, wanda kika damu dashi ɗin ma ba take yake yi ba, ina nan zaune ai zan ganku a rana”.

“Ee dai nasan haushi kake ji don nafi nuna masa kulawa”.Cewar Mom tana dariya

Lokacin ne Khalil yaɗago kansa daga latsa wayan da yafara yi, yakalli Sameer yaharare shi yana ɗauke kai, waro ido Sameer ɗin yayi yace

“Mom harara na yake yi fa”.

Mom tace “to ai kaine kamatsa mishi Ni banga laifin shi ba ai”.

“Mom ni yunwa fa nake ji”.

Cewar Khalil yana langaɓe kai

“Oh sorry My Son, bari insa akawo maka, me kake so?”

“Mom koma menene kukayi zanci, bazan iya jiran adafa min wani ba”.

“Okey”. Mom tace hakan tana ƙwala kiran ƴar aiki

Sai da tazo tafaɗa mata tahaɗo ma Khalil abinci takawo masa nan, sannan takalli Sameer tace

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button