HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 45*

A kwana a tashi asarar mai rai,ga shi har an samu kimanin wata biyu da rasuwar Fauzee,kowa ya sa ki jikinsa an koma rayuwa kamar da,sai idan an yi wani abu za ka ji an ce Allah ya jiƙan Fauzee,a haka bikin Umma ya rage saura ƙwana ukku a yau ne kuma ƴan amana zasu gabatar da partynsu.
Yau tun da safe Husna da duk ma wani mai hannu da tsaki a cikin group ɗin bai samu zama ba,basu nan basu chan suna ƙoƙarin ganin komai ya tafi akan tsari,cikin ikon Allah kuma sai komai yana tafiya yanda suka tsara sai dai ƴan abubuwan da ba za a rasa ba,cikin ikon Allah kuwa sai ga shi zuwa ƙarfe ukku har an gama decoration ɗin wurin.
Sai da suka ga komai ya yi yanda suke so,sannan mazan suka tafi gida dan su yi wanka,idan suka dawo sai matan su tafi su ma,duk wani abu da aka tanada na ci ko sha sai da su Husna suka tabbatar ya zauna a wurinshi, ƙarfe huɗu dai-dai mai Dj yazo inda aka tanadar masa ya aje kayanshi.
Huɗu da minti goma sha biyar mazan suka dawo,nan su Maryam suka bi Husna gidansu a chan zasu yi wanka(gidansu Husna yafi kusa da inda za a yi partyn,shi yasa suka kai kayansu chan.)
Ko da suka je gidansu Husna basu zauna ba, Fadila ita ce ta fara shiga wankan,kafin ta fito Husna ta yi masu turaren kayan,ta na fitowa Maryam ta shiga,kaya kawai Fadila ta sanya ta zauna Husna ta fara yi mata ƙwalliya, shaf-shaf ta gama mata,ganin Maryam ba ta fito ba yasa Husna nufa toilet ɗin Mama ta shiga na ta wankan a chan,kusan a tare suka fito ita da Maryam, sallar la’asar suka fara yi sannan Maryam ta zauna ita ma,cikin ƙwarewar aiki Husna ta gama ma Maryam ƙwalliyarta.
Nan fa kira ya fara shigowa wayar Husna,ganin mai kiran yasa Husna yin murmushi ta kalli su Maryam ta ce,”Mu yi sauri mu fita ga amarya chan fa na jirana.” Husna ta faɗa lokacin da ta ida ɗaura ma Maryam kallabi,Masha Allah sun yi kyau sosai,kamar jira ake Husna ta zauna gaban madubi sai ga kira ya fara shigowa wayarta.
“Anty Maryam ku zo mu tafi kawai dan ba zasu kyaleni ba in ba zuwa nayi ba.”
Ta faɗa tana gyara akwatin kayan ƙwalliyar,sai da ta gama maida kayan ciki sannan ta rufe.
“Ke ba ki ƙwalliyar ba Husna,dan Allah ki zauna kiyi sai mu tafi.”
Maryam ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe akwatin kayan ƙwalliyar,murmushi Husna ta yi ta ce,”Anty Maryam ki bari mu tafi idan naje nayi ma amarya sai nima nayi a chan ɗin,kin ga amarya tafi ni buƙatar ƙwalliyar.”
Husna ta yi maganar tare da bubbuga bayan Anty Maryam, murmushi kwance akan fuskarta.
“Wai zaman me kuke a ɗaki har yanzu baku fito ba?”
Muryar Mama dake tsaye bakin ƙofar ɗakin,suka tsinkaya a cikin kunnuwansu, murmushi Husna ta ƙara yi ta ce,”wai Mama dole sai nayi ƙwalliya kafin mu tafi bayan ga amarya chan na jirana.”
Labulen ɗakin Mama ta riƙe ta ce,”Aa ba za a yi haka ba,ku je dai ayi ma amaryar ina fatan dai kin gama ma su Fadila ƙwalliyar?”
“Na gama masu Mama.”
Husna ta faɗa tare da yafa gyalenta, akwatin ta ɗauka ta fito tsakar gida,ganin haka su Maryam su ma suka biyo ta wajen,kallonsu Mama ta yi ta ce,”Masha Allah kun yi kyau sosai, Allah ya kawo mazaje na gari,ku yi sauri ku tafi har biyar saura minti goma.”
“Innalillahi mun makara wallahi ƙarfe biyar da aka sanya za a fara,Anty Maryam ku yi sauri mu wuce,ina ganin kawai ku wuce wurin partyn dan ku kula da wurin,ni kuma na taho tare da amarya idan mun gam…”
Kiran da ya shigo a wayarta ne ya hana ta ƙarasa maganar ta,ganin mai kiran yasa ta ɗauka tare da nufar hanyar waje,hannu kawai ta ɗaga ma su Maryam alamar sai sun haɗu chan, Ibrahim ne ke kiranta ɗagawa ta yi tare da sallama.
“Amincin Allah ya tabbata a gareka masoyi.”
“Tare da ke gimbiya,yau gaba ɗaya kin manta dani koh?”
Ya faɗa dan ya tsokaneta, murmushi ta yi har yana jiyo sautin shi ta ce,”haba Malam yau gaba ɗaya duk muna tare shi ne za ka faɗi haka?”
Shi ma dariyar ya yi,”kina ina haka naji kamar kina tafiya?” Ibrahim ya faɗa yana dariya.
“Gani na fito zan tafi yi ma amarya ƙwalliya.”
Ta faɗa tare da ɗagama wani mai keke napep hannu.
“Okay kiyi sauri dan Allah kin ga lokaci na ƙurewa,amma ban yadda ba ke kiyi ma fuskar ki ƙwalliya ba.”
Ya ƙarasa maganar shi cikin kishi,sanin abin da yake nufi yasa ta yin murmushi ta ce,”ƴallabai ban yi ba dama.”
“Yauwa Tawan shi yasa nake ƙara sonki,a kullum kina girmama abin da nake so,kina ƙoƙarin kiyaye abin da bana so, Allah ya kauda idon mahassada akanmu, Allah ya tsareman ke sai kin iso.”
Yana fadar haka ya datse wayarshi bai tsaya jin amsarta ba.
“Hajiya ina zan kai ki?”
Muryar mai keke napep ce ta daki dodon kunnenta,saurin dawowa hayyacinta ta yi nan ta faɗa masa,tare da shiga suka tafi.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 46*

Mintina ƙalilan suka kai su ƙofar gidansu Umma,ko da ta sallami mai keke napep gidan ta shiga,tana zuwa babu ɓata lokaci ta fara yi ma amarya ƙwalliya,sun ɗauki lokaci ana ƙwalliyar,kowa dai yasan yanda shirin amarya yake,dan haka sai biyar da minti goma sha biyar suka gama,gamawarsu babu daɗewa aka zo ɗaukarsu,ko da suka isa wurin da ake partyn har da rabi ta yi,gaskiya wurin ya ƙawatu sosai.
Cikin tsari aka shiga da amarya wurin,sai da aka kai amarya kan kujerarta sannan mai dije ya saki kiɗa.
Su Husna ko zama basu samu yi ba saboda yawan mutane,suna kai da komowa ganin komai ya tafi yanda aka tsara,duk wanda yazo wurin suna ƙoƙarin ganin ya ji daɗin wurin, Alhamdullih komai ya tafi dai-dai dan mutane sun yaba ƙwarai da karamcin mutanen gidan ƴan amana,ba kamar Husna da kowa ke burin haɗuwa da ita,aikuwa an yi wasa da dariya kamar ka da a rabu,saboda magana har sai da muryar Husna ta shaƙe.
Su Husna basu samu natsuwa ba har sai da aka tashi,lokacin ana ta kiran sallar magrib,mutane aka fara jigilar ɗauka,sai da aka kai kowa gida lokacin ne su Husna suka fara shirin tafiya nasu gidan,lokacin har an shiga sallar isha’i, kayayyakin da aka yi amfani dasu ne suka rinƙa fiddowa,kowa na ɗaukar kayan da ya zuɓo abin da ya kawo,ganin ba a rage komai ba yasa Chairman ce wa,
“Wai Husna ina namu kason ne?”
Ya yi maganar yana buɗe kular da ke gabanshi,dariya kowa ya yi sannan Husna ta ce,”Malam ni ban ɗibi komai ba.”
Kowa idanuwa ya zuba mata,dan sai da aka ce ta ɗiba ta aje wanda zasu ci idan an gama,ganin kallon da kowa ke mata yasa ta katse masu shirun.
“Kai da har na ɗiba kuma mutane suka rinƙa zuwa babu abin da za a basu,shi yasa ni kuma na ɗauki wanda na aje na basu.”
“Amma yarinyar nan kin gama damu wallahi,nan wata baƙar yunwa nake ji duk yau ban ci komai ba,nan niyyata na samu abin da kika aje mana na ci.”
Dabai yai maganar yana harararta,ganin haka yasa ta yin dariya ta ce,”To su acici Mala’ikun tauna ni ban ake komai ba duka na rabar!”
Kafin Dabai ya yi magana sai Abu Abdul Rahman ya rigashi,”Ustaziya dan Allah ki miƙo mana ko mun cinye mu ƙara gaba.”
Kallonshi ta yi sai kawai ta kama dariya ganin yadda duk suka yi zaman ci,”wallahi ni ban rage komai ba kuma ku tambayi Anty Maryam ku ji.”
Husna ta faɗa tana ƙara sakin dariya,duk maida kallonsu suka yi kan Maryam dake tsaye,ganin suna kallonta yasa Maryam ce wa,”Da gaske Husna ke yi ba a rage komai ba wallahi.”
“Amma dai gaskiya kun gama damu wallahi,yanzu duk kayan da aka ci amma ace ban damu? Da nasani da tun ana ci zan karɓi nawa!”
Ibrahim ya faɗa da iyakar gaskiyarshi,kallonshi Husna ta yi suna haɗa idanuwa sai ta kashe ma shi ido guda, ɗaure fuska ya yi tare da ɗauke kanshi.
“Da wannan zaman da mun san abin da ya kamata kawai, wallahi yunwa nake ji kamar an sace man yan hanjina nake ji.”
Sulluɓawa ya faɗa dan shi tun da aka fara maganar bai yi magana ba,kowa shiru ya yi yana tunanin abin da ya kamata,ganin babu wanda ya ce komai sai Husna ta ce,”akwai abinci gidanmu ko muje chan sai aci?”
Ta ida maganar tana murmushi,dan ta san da gaske yunwar suke ji,ita kanta yunwar ke damunta dan duk yau sau ɗaya ta ci abinci,nan take suka yarda da shawararta dan ita kaɗai ce mafita a garesu,nan fa suka shiga Mota aka ta da,basu tsaya a ko ina ba sai kofar gidansu Husna,dan babu nisa sosai a tsakani,fitowa suka yi daga cikin motar gaba ɗayansu,matan suka fara shiga cikin gidan,bayan minti biyar sai ga Maryam ta fito kiransu,cikin gidan suka shiga.
Falon Babansu Husna aka sauke mazan,kular abinci ce a gabansu sai ta miya,ko da suka aje ma Mazan komai da zasu buƙata sai su ka wuce ɗakin Husna inda su ma chan zasu ci abinci su, kasancewar kowa yunwa yake ji sai ba ka jin hayaniyar komai sai ƙarar cokulla.
Basu bar gidansu Husna ba sai goma saura,nan fa suka yi sallama da Husna,inda aka wuce dasu Maryam dan kusan hanyarsu ɗaya.
Husna na komawa gida nan fa ta tattare komai da aka ɓata, kitchen ta kai su ta wuce ɗakin Mama,nan ta zauna tana ba Mama labarin yanda komai ya gudana,sun daɗe suna tattaunawa sannan Husna ta yi ma Mama sallama ta nufi ɗakinta.
Wanka ta shiga ba ta daɗe ba ta fito,rigar bacci kawai ta sanya ta hau kan gado,har ta gama addu’oin kwanciya bacci,tana shirin kwanciya sai ga kiran Ibrahim ya shigo, ɗauka ta yi tana gyara kwanciyarta, kasancewar duk a gajiye suke sai firar ba ta yi nisa ba suka yi sallama,kwanciya ta gyara babu daɗewa bacci ya ɗauketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button