NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE

Na fara da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

1)
A komai nawa cikin kazar-kazar nake yinsa, ban cika yin abu da sanyin jiki ba ko yanƙwana, hakan yasa da yawan ƙawaye koma ƴan gidanmu, kai hattama da Gwaggona lokuta da dama su kance min mai jikin maza.
A durƙushe nake ƙofar dakalin ɗakin Inna Amarya ina gyara tsinkakken silifas ɗina, wanda yasha jiki ya gaji da duniya, dan yanzu ma da baƙar leda nake ɗaure shi, ina gama gyara shi na zira a ƙafafuna masu ɗauke da zara zaren yatsu, na gyara zaman fuskar hijaɓ ɗina, na kuma ƙara tallafar allona da kyau, sannan na duƙa tare da ɗaga labule ina cewa Inna Amarya na tafi makarantar asuba.
Bata amsa ba hakan ya bani tabbacin ko bata ɗakin ko kuma bata tashi a bacci ba, saboda haka na zare takalmina na faɗa ɗakin, na ƙaro hasken wutar aci bal-bal saboda ɗakin ya sami wadatuwa da haske kasancewar duku-dukun asubahi ne, ile kuwa sai naga Inna Amarya riƙe da carbi hannu tana lazimi ta ɓingilar da kai gefe tana bacci, nayi murmushi na ƙarasa gabanta, kallonta nake cike da so da ƙauna da kuma tausayawa, na sanya tafukan hannuna na tallabi fuskarta na haɗe goshinta da nawa, ananne kuma ta buɗe ido ta zuba su cikin nawa, tayi firgigit da son farkawa daga baccin da take tunanin gyangyaɗi ne take yi.
“oni Shatu, yanzu Allah kuwa Mairo baki wuce kin tafi makarantar nan ba, sai Malam ya fito ya ganki kija min magana, ko kuma kije a dakeki Kabiru ya tada jijiyoyin wuya yana hayagaga an taɓaki, shikenan yay ta sakawa ana sauya miki makaranta sai kace ke ɗaya ce ƴar gata”.
Duk wannan maganar da Inna Amarya keyi acikin faɗa take yinta, maimakon na yunƙura na miƙe kamar yanda take saka ran ganin nayi, saima na gyara zama tare da lafewa ajikinta, cije leɓe nayi ina ƙoƙarin danne dariyar dake neman suɓuce min saboda yanda naga ta saki baki galala tana kallona. Bata ce min uffan ba haka nima kuma ban kuma cewa komai ba, sai ƙara narkewa da nake ajikinta tamkar magen data sami katifar auduga.
Tsawon mintunan da baza su wuce uku ba sai naji tayi ƙwafa kafin tace, “Allah ya shigo da Amadu nan kusa bada jimawa ba”. Dariya na ƙyalƙyale da ita, na ɗago kai ina kallonta nace,”Inna idan ya shigo me zai yi miki?”. Ba tare data dubeni ba ta ƙarasa tasbihin da take sannan tace, “ya shigo nace masa sauran ƴaƴa duk sun wuce makaranta ke kina nan a zaune”. “idan yazo hukuntani kuma ki hana ba”. Na faɗa ina ƙara ƙanƙameta ina murmushi, inata jiyo takun sauran yaran gidan na wucewa makaranta. Buɗar bakinta zatayi magana aka ɗaga labule, Gwaggona ce bakinta ɗauke da sallama, aciki na amsar sallamar sai Inna Amarya wadda ta amsa a fili suna gaisawa.
“ai zanbi bayanta sai Zulai take ce min ta shigo nan bata tafi ba”.
“umm”. Shine abinda Inna Amarya ta iya cewa kawai, dan ta tabbata Inna Zulai ta faɗi hakanne domin Malam yaji ko kuma ita Gwaggo ta zazzageni da faɗa.
“gashi kuɗin laraba ne dama, sai danaji yara kowa na faɗar abashi nasa sannan na tuna da nata, tunda ita bata da hankalin tuna abubuwa masu muhimmanci, tafi gane sai taje a dawo da ita”. Murmushi kawai Inna Amarya tayi ta miƙa hannu ta amsa tsohuwar ashirin ɗin dake hannun Gwaggo, ita kuma tasa kai tana ƙoƙarin ficewa, Kafin ta fita ta juyo ta kuma cewa da Inna Amarya, “nace yau mu sayo awara ko kuma ayi ƙosai kawai?”. Muka haɗa ido ni da Inna Amarya yanda Gwaggo ba zata gane ba, sannan Inna Amarya tace mata, “a siyo awarar kawai, tunda kinga shekaranjiya da jiyan duk ƙosai akaci”. “to shikenan”. Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin gaba ɗaya acikin sanyin jiki.
Ɗabi’u da kyawun hali, da sanyin jiki irin na Gwaggona su mutane suke min Kwaɗayin samu, ni kuwa a haƙinta babu ɗaya dana ɗauko musamman ta ɓangaren haƙuri, ban sanshi ba ni kam.
Gyaran muryar dana jiyo ne daga tsakar gida yasa na bankaɗa ƙasan gadon ƙarfen Inna Amarya na faɗa ciki a gigice, jikina banda ɓari da kyarma babu abinda yake yi, tsorona Allah tsorona Ya Amadu ya shigo ɗakin Inna Amarya, ko kuma uwar gulma Inna Zulai tace masa ban tafi makaranta ba. Banda sauke numfashi da sauri da sauri babu abinda nake yi.
“kya iya fitowa ai, naji kamar ɗakin Malam ya shiga”. Inna Amarya na faɗar haka nasa kai zan fito daga ƙasan gadon, aiko sai jin sallamarsa kake ya shigo ɗakin, babu shiri na kuma maida kaina Allah ya taimakeni bai ganni ba, da yau saina gane bani da wayo, Ya shigo ya zauna ya gaida Inna Amarya sannan ya tashi ya fice, yana ficewa kuwa na fito, dan nasan ɗakin Gwaggo ya faɗa kuma idan ya shiga yana jimawa bai fito ba, takalmana da allona a hammata na fito saɗaf-saɗaf na fice daga gidan, ina isa bakin zaure na arta ana kare, ban tsaya kuma a ko’ina ba sai makaranta, kuma ko dana isa Malam ya tambayeni dalilin makarar dana yi sai nace masa Ya Amadu yace dan Allah yayi haƙuri zaizo yayi masa bayani. Malam Nasiru ya kaɗa kai kawai ya bani hanya na wuce, darajar Malam kaɗai ita take saka shi ɗagawa ƴan’gidanmu ƙafa a duk wani lamari daya shafemu a makarantar.
Da an idar da sallar asuba muke shiga makarantar asuba, ba kuma a tashinmu sai ƙarfe takwas, sannan ƙarfe goma mu ƙara komawa. Muna kan hanyarmu ta dawowa ne mukaci karo da Ya Kabiru, tun daga nesa ya buɗe haƙora yana sakar min ƙawataccen murmushinsa wanda ke daɗa fitar da ainihin kyawunsa, gani nake kaf duniya babu wani namiji me kyau kamar Ya Kabiruna, haka kuma babu ƙanwar data yi dace a rayuwarta kamarni, samun Yaya mai nagarta hali, dattako, ilimi, haƙuri da sanin ya kamata kamar Ya Kabiruna sai an shirya. Shekaruna goma sha huɗu a duniya, a idon jama’a da dama na girma amma banda idon Ya Kabiru, domin kuwa shi kullum a wajensa jaririya nake, ɗanya shagaf ma kuwa, baya min wannan kallon girman da mutane ke yi min, saboda haka ne ma sau tari idan nayi abin faɗa sai yace a ƙyaleni ai ban san me nake ba, da saurana har yanzu, a bari lokacin dana girma sai a dinga yi min faɗan, shine lokacin nasan me ake cewa me kuma ake nufi, amma yanzu idan sunyi a banza dan ba fahimta nake ba, a banza kuwa, domin ni dai Mairo da wuya ayi min faɗa na gane me ake nufi, indai ba wai nice nayiwa kaina faɗan ba.
Daga inda yake ya buɗe min hannu, na tafi da ɗan guduna zan faɗa jikinsa na rungume shi sai kuma ya sarƙafe hannayensa yaƙi bani damar hakan, na cuno baki gaba cikin shagwaɓa ina bone fuska, fuskarsa na bayyanar da ƴar siririyar dariya ya dafa kafaɗa yana cewa, “muje ki rakani shago na siyowa Gwaggo sikari”. Hannuna acikin nasa muka ƙarasa har shagon Bala, ya auna sikari ya bamu, mun juyo zamu tafi yake cewa Ya Kabiru a faɗawa Malam dan Allah idan kuɗaɗen nan da yake binsa zasu samu yana da buƙatarsu, yana so zai ƙaro kayan shago, Ya Kabiru ya jinjina masa tare da cewa, “to Bala insha’Allahu zan sanar masa. Nawane kuɗin dama?”. “dubu huɗu ne da dari uku, ɗazu ma Adawiyya tazo ta karɓi ɗari to amma ita wannan a barta”. “to Bala an gode Allah ya saka. Kuɗin kuma in Allah ya yarda za’a kawo maka”.
Har muka iso gida idona a rufe yake, zuciyata na wani irin zafi, bana so ba kuma na ƙaunar naji ana bin Babana bashi, duk da cewa saita kai maƙura sannan Baba yake amsar bashi, shi ɗinma kuma a wurin Bala ne kawai, kuma baya wuce dubu ɗaya ƙasa da hakan, dama ni irin wannan wulaƙancin nake gudu, banda tozarci a gaban mutane yake cewa ayiwa Malam tuni da kuɗin da yake binsa, sanin kansa ne ci da sha da sutura basu gagaremu ba, muna da rufin asirin da munfi ƙarfin roƙa a wurin wani, haka kuma Baba yanada wadatar zucin da babu mai yi masa kallon faƙirin talaka, balle har ake yamaɗiɗi da shi a bainannasi ana cewa ana binsa dubu huɗu, me akai akayi dubu huɗun, na tabbata da Inna Amarya tasan da wannan bashin da tuni ta biya, idan ba ita ba Ya Amadu tunda shi yafi Ya Kabiru ɗan samu duk da cewar shima buga-buga ce yake yi ya samu.
Shigowarmu Babu wanda na kula, na saki hannun Ya Kabiru na shige ɗakin Inna Amarya, dukkuwa da cewar kowa na zaune tsakar gida za ai karin kummalon safe, tunda na shiga ɗaki na kifa kaina da gwiwata ban ɗago ba har tsawon wucewar wasu daƙiƙu masu yawa, Inna Amarya ta shigo tana ta kiran sunana amma ban amsa ba, tazo ta ɗago kaina, ta zaro ido tana kallon fuskata dana haɗa uban zufa kace ruwa aka sheƙa min, idona yayi jajur duk sanadin ɓacin rai, da ace Bala iyaka mu da shi yay maganar ba zan damu kamar haka ba.
Tayi salati ta sanar da ubangiji, “Mairo lafiya? Wa ya ɓata miki rai?”. Bance mata ƙala ba sai rumtse ido danayi sosai tare da jinginar da kaina jikin bango, tayi tambayar duniya akan meke damuna ban bata amsar ci kanki ba. Har ranta ya ɓaci ta tashi ta fita ta bani wuri, ina cikin wannan yanayinne na neman mafitar yanda za’ai a biya bashin da ake bin Baba, sai naji an dafa goshina, da lallausan hannu mai cike da wata iriyar ni’ima, na buɗe idanuna na saukesu akan mara lafiyar gidanmu wadda tun tasowarmu mukafi yi mata kallo da mahaukaciya, shekaru goma sha huɗu kenan haka na taso na ganta bata ummm bata um-um, sai dai tabi mutane da ido kawai, ni tun tana bani haushi ma har ta fara bani tausayi, saboda duk sanda na kalleta idanunta cike yake taff da ruwan hawaye, ni nama rasa wanne irin ruwan hawayene wannan da basa zuba saida su tsaya acikin ido.
Yanda na ƙura mata ido ina kallonta sai naga ta rufe nata idon, yau ranar farko da naga wannan ruwan hawayen sun zuba tsawon shekaru goma sha huɗu, tayi zaman raƙumi tare da kamo kaina ta kwantar bisa cinyarta, ƙirjina ya shiga harbawa, faɗuwar gaba ta tsananta gareni, ban san dalili ba, amma dai na tsinkayi zuciyata da abinda bata taɓa ji ba sai a wannan cinyar, ko kaɗan banji ƙyanƙyaminta ba, dukkuwa yaran gidanmu har toshe hanci suke idan suka zo wucewa ta kusa da ita, to amma ni sanin da nayi mata na samun kulawa daga wurin Gwaggona yasa bana ƙyamarta ko kaɗan, dan a kullum Gwaggo na dafa mata ruwan zafi ta rakata bayi tayi wanka ta bata kaya masu kyau ta saka, ta kuma fesheta da turare masu ƙamshin gaske, irin sittirun da take sakawa ya banbanta da irin wanda muke sawa, namu sittru ne irin na ƴaƴan Malam Audu, ita kuwa duk sitturar data saka sai naji an magantu akai, sai dai idan ba’ayi baƙo ba, ananne zakaji yana faɗar darajar kayan dake jikinta, kuma ni tunda nake da Gwaggona bata taɓa saka kuɗinta ta ɗinka min sutura ba, sai dai Inna Amarya ko kuma kakarmu Yagana, nakanji haushi sosai na cewa Yagana ni nasan Gwaggona riƙona take ba ƴarta bace ni, tunda bata siya min kaya da kuɗinta sai dai ta siya wata mahaukaciya data tsintto, kuma ma kaya masu tsada, dan haka ni ba ruwana da ita ko gaisheta na daina yi, wataran har na kanyi tantamar inda Gwaggo ke samun kuɗin da take siyar mahaukaciyar gidanmu kaya nake, domin wataranma idan naji kuɗin wasu kayan sai naga ko jarinta na barkono da kuka aka tattara bai zasu kai wannan kuɗin kayan ba, idan na ishi Yagana da mita sai dai ta kalleni tace Yaro yaro ne, ni kuma hakan na ƙara ƙufular dani.
Ina kwance akan cinyartata na lumshe ido tare da shaƙar ni’imtaccen ƙamshin dake fita daga jikin zanenta, naji yatsun hannuna sun sarƙe acikin nata, da ɗayan hannunta kuma tana shafa sumar kaina a hankali, lokaci ɗaya naji na fara samun sassaucin raɗaɗin zafin da nake ji a zuciyata, nutsuwar da nake neman rasawa ta dawo, har ina sauke ajiyar zuciya. Can kuma sai nayi zumbur na tashi daga saman cinyartata, na waro ido ina kallonta, ni gani nake idan aka mata magana baji take ba, tunda ko kayi sai dai ta bika da ido kawai, na yatsina fuska na shiga yi mata alama da hannu, ina nufin ta tashi ta fita kar Gwaggo tazo ta sameta, saboda ba zan taɓa mantawa ba da wata rana, bayan Gwaggo ta gama shiryata tana zaune can wajen zamanta a tsakar gida, dama sai dare yayi ne take shiga ɗakin Gwaggo tayi bacci, a wannan lokacinne ina zaune kusa da ita ina mata labari, saiga Gwaggo tazo ta hauta da faɗa sosai akan ba ruwanta da ƴarta karta ƙara dosar inda nake, idan ba haka ba zata saɓa mata, idan bata yi wasa ba ma zata koreta daga gidanta, a ranar har naji haushin Gwaggona saboda rashin tausayin data nuna akan mara lafiya, na kuma jima ina cewa Allah yasa kar nayo halin Gwaggona na rashin kyautawa, gwamma nayi halin Malam shine yasan mutum da darajarsa, aiko ile saiga Malam ya fito daga ɗaki yanama Gwaggo faɗa akan ta daina yi mata irin haka.
Na ƙara miƙewa zaune ina ƙara roƙon mahaukaciyar nan akan ta tashi ta fita, sabon takaicinma ban san sunanta ba, tunda na taso ban taɓa jin an kira sunanta ba sai dai KE kawai, taƙi motsayawa sai kafeni da ido da tayi, irin kallon da naji yana neman tsinkar da jijiyar jikina, na rufe ido na kauda kai sannan na juyo a fusace na doka mata tsawa nace ta tashi ta fice, ai ban gama rufe bakina ba saiga Gwaggo ta shigo ɗakin, ranta a matuƙar ɓace sai huci take.
Kallo ɗaya tayi min ta ɗauke kai sannan ta maida dubanta ga mahaukaciyar tana yi mata nuni da bakin ƙofa wanda ta ɗage labule, karo na farko da naji Gwaggo ta ambaci sunanta, acikin yanayi na tafarfasar zuciya, “Kulu tashi ki fice, ki fice tun kamin raina ya ɓaci”. Cikin sanyin jiki kulu ta miƙe jikinta na rawa, tana zuwa dab da inda Gwaggo take sai ta ɗan dakata da tafiya. ” ba zaki fita ba saina saka an ɗakko min ƙatti a waje sun fita dake”. Gwaggo ta kuma kai yatsanta dai-dai idon Kulu tamkar zata tsone shi, “ba tun yau ba nake faɗa miki babu ruwanki da ƴata, ki fita a sabgarta, ke nake taimakawa dan haka ba sai kince zaki sakamin ba ta hanyar shiga rayuwar ƴata ba. Yau ta kasance rana ta ƙarshe da zan kuma ganinki kusa da Mairo, wallahi duk ranar da kusancin inuwarku ma ban gamsu da shi ba, la shakka sai kin bar gidan nan…fice”.
Gwaggo ta ƙarashe maganar a hasale, Kulu kanta a ƙasa ta fice a bar tausayi, jikina yayi matuƙar sanyi da abinda Gwaggo tayi mata, na kuma ji haushin Gwaggona ya kamani, sam bai kamata tayiwa mara lafiya haka ba a matsayinta na musulma.
Ficewarta faɗan kuma sai ya dawo kaina, “ke kuma ai kinji me na faɗa mata, idanma ita bata fahimta ba ai ke kin fahimta, ki saɓa daga yanda nace”.
“Allah ya baki haƙuri Gwaggo, insha’Allahu ba zaki sake ganina da ita ba”.
Bata tankani ba tasa kai ta fice, nayi zaman daɓaro anan wurin, kamar na saka kuka haka nake ji, sai dai ni ɗin ina da taurin zuciya, ba abu kaɗan ke sakani kuka ba, ni hasali ma abu ɗaya nasan yana sani zubar hawaye, taɓa mahaifina.
Ban san lokacin da Ya Amadu ya shigo ba, sai ganinsa nayi a tsakiyar kaina, da alamu ma ya shura tsawon wasu mintuna tsaye a wurin, ban farga da hakkan ba sai dana ji Inna Amarya na cewa, “ga Kununta nan, kasata ta sha, ni dai ban san me akayi mata ba”.
Shiru yayi baice komai ba, sai bayan fitar Inna Amarya ne ya rage tsawonsa ya tsuguna gabana, muryarsa acan ƙasan maƙoshi yace,”kuka kika yi?”. Na ɗago da dara-daran idanuwana na zubesu cikin nasa, domin ya samu amsar da yake buƙata. “to me ya kawo ɓacin ran?”. Naja hanci sannan nace masa, “Bala Mai Shago yana bin Baba bashin kuɗi naira dubu huɗu da ɗari uku, kuma yace yana buƙatar abinsa da akai masa nan bada jimawa ba”.
“Bashi?”. Ya tambayeni da tantamar abinda na faɗa. “ehh ka tambayi Ya Kabiru ai agabansa ne ma ya faɗa, Kuma sai daya faɗa da ƙarfi duk jama’ar gari suka ji”.
Numfashi naji ya sauke kafin ya saka hannu a aljihu ya zaro ƴan ɗari biyar biyar guda goma, ya miƙo min yace na kaiwa Bala ɗin nace masa an gode. Nayi saurin yunƙurawa zan miƙe ya maidani na koma na zauna. “ki fara cin abinci”. “Yaya ba zan iyaci ba, idan na kai masa tukunna zanfi samun natsuwar ci”. Ya kaɗa min kai kawai, har naje na kaiwa Bala kuɗinsa na dawo Ya Amadu na inda na barsa a zaune, sai dai da alama yayi zurfi cikin duniyar tunani, na zauna kusa da shi na jawo kwanon kunu na buɗe awara dake cikin marar tuwo, na ɗau awarar zan kai bakina sai ganin Ya Amadu nai ya miƙo min wata, kallo ɗayaa kawai na masa sannan na buɗe baki ya saka min kafin nan ya kuma ɗauko kwanon kunun ya kafa min a baki na kurɓa, guda uku kawai naci naji na ƙoshi saboda kasa sakewa da nayi da shi, da ace Ya Kabiru ne dama ko baice zai bani da kansa ba zance ni shi zai bani, amma shi Ya Amadu yau ɗaya sai nake jin nauyin hakan, na karayar da kai ina cewa Yaya na ƙoshi, sai ya zare min wannan manyan idanuwan nasa masu shegen firgitarwa, hakan yasa ba shiri naci gaba da karɓa inaci sai dana cinye tass.
“me kika yiwa Gwaggo?”. Ya jefo tambayar fuska babu walwala, shi dama fuskarsa kullum haka take.
“shigowa tayi taganmu tare da Kulu, amma wallahi Ya Amadu bayan haka ban mata komai ba”.
“daga yau nima idan na ƙara ganinki kusa da Kulu saina yankaki har lahira, i mean it Mairo ba zan ƙyaleki ba, tunda ke ba kya gudun ɓacin ran mahaifiyarmu”.
“insha’Allahu zan kiyaye, amma fa ni ai bani ke zuwa inda take ba, ita take zuwa wurina”.
“su sauran yaran gidan baki kalla idan taje wurin guduwa suke su barta ba, ko ke ɗaya ce da ba kya jin magana ba zaki abinda akace miki ba”.
Na girgiza masa kai, “A’a Yaya, kawai tana bani tausayi ne, sai naga bai dace dan tana cikin wannan halin ba da take tsananin buƙatar wani kusa da ita kuma muke gudunta ba, lalurar nan ba ita ta ɗorawa kanta ba fa”.
“ai biki fimu sanin hakan ba ko”.
“to ayi haƙuri”.
Inna Amarya ta shigo ɗakin tana faɗin,”ni dai na rasa wannan dalili, idan kun san matar nan zakusa jininku suke ƙyamarta me zaisa kuce zaku jawota jikinku dan taimaka mata.
To ni dai gaskiya a daina samin Ƴa a gaba da faɗa, tunda ma ba ita take kai kanta wurinta ba, yauwa, ita da take zuwa inda take dan haka ita za kuyiwa faɗa…idan ka gama abinda ya kawoka ɗakin sai ka miƙe ka fita, ni ban kiraka dan kasa min ƴa a gaba kana mata faɗa ba, kiranka nayi kaji damuwarta ka lallasheta, ah tau tashi kaje haka Amadu na gode, mu kwan lafiya”.
“mu kwan lafiya kuma Inna?”.
Tana warware tabarma tace, “ehh Amadu mu kwan lafiya ni kam”.
Yana murmushi yace, “yanzu fa garin ya waye Inna, ƙarfe tara ne fa”.
“ehh na sani ai kaje ni kam dan Allah na gaji da ganinka haka”. Siririyar dariya sauke bisa laɓɓansa ya fita a ɗakin bayan yace da Inna Amarya ya wuce wurin aiki.
SIRRIN ƁOYE

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button