NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 1

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*
*_©2019_*

*بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ*

_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._

           *[1……]*

     …………Tafe take tana zirar da hawaye masu d’umi da saka k’unar zuciya. Kasantuwar Nikab d’in dake sakaye da fuskarta ya hana bayyanuwar kukan nata ga mutane, dukda dai hakan bai hana wasu kallonta ba, musamman wad’anda sukeda tabbacin itace.
      Cikin Nutsuwa da sanyi take tafiya, kanta a k’asa dukda kuwa tana sanye da dogon hijjab da nik’ab. Isowarta inda zata yasa ta tura murfin k’ofar gidan kalar madara ta shiga da sallama.
     Dattijuwar da bazata gaza shekara hamsinba ta d’ago daga d’ibar ruwan da take a rijiya ta amsa Mata.
       “Wa’alaikissalam, yanaga kin dawo dandanan? Kobaki iskeshi a gidan bane?”
    Nik’af d’inta ta yaye, kamilalliyar fuskarta ta bayyana, ta d’an sakin guntun murmushi tace, “Eh Umman mu, na tarar har ya tafi kasuwa”.
      Batareda ta jira amsar Umman tasuba ta wuce gaba. Binta da kallo Umma tayi, ko kad’an bata yardaba, tasan ta 6oye mata ainahin abinda yafarune acan kamar yanda ta saba gudun kar ranta ya 6aci. Ta d’an sauke ajiyar zuciya tana girgiza Kai, sannan ta ajiye gugan hannunta ta d’auraye hannun da ruwan data jawo ta nufi d’akin da yarinyar ta shiga.
       Zaune ta isketa ta zabga uban tagumi tan

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button