Lu’u Lu’u 16

*16*
Daga b’angaren Habbee ta numfasa tace “Gimbiyata, ki gafarce mu, tabbas kan ki zai d’aure idan kika ji b’oyayyan sirrin dake tattare da ke, watak’ila ma ki kasa yarda damu, amma dai gaskiya ce wacce kowa ya san ta ban da ke kawai, fatana kawai idan kinji gaskiyar nan kar mu zaba ababen zarginki bare ki hukunta mu.”
Rud’un data shiga ne yasa sai ta ji kamar bata fahimtar, sai kuma tayi k’arfin halin saurin fad’in” Dakata Mah, wai ke ma ya kike neman kin d’aure min kai ne ? So kike ki tabbatar min akwai alamar gaskiya a zantuttukan mutanen nan kenan?”
Numfashi ta sauke har saida ta ji sautinshi a kunnenta kafin tace” Hakane ranki shi dad’e.”
K’ank’ance idonta tayi tana karkad’a yatsanta tace” Kenan gaske da yarinyar nan tace ni yar uwar ta ce? Kuma mahaifinmu shi ne…”
Da k’arfi tace” Kai… Ina ba zai yiwu ba, kuna yanzu Mah?”
Saida Habbee ta kalli lafiyayyen d’aki da suke sannan tace” Wani waje ne mai sirri ne, ya ce kar mu fad’a saboda tsaronmu na wuyansa.”
A harzuk’e tace” Ina kuke mah? Ina son ganinku yanzu.”
A ladabce Habbee tace” Kar ki damu gimbiyata, zamu had’u nan kusa.”
D’auke wayar tayi a kunnenta ta mik’a masa tarz da fad’in” Ina son ganinsu yanzu, ya za’ayi?”
Mik’ewa yayi tsaye yana huro iska ya kalli fuskarta, saida ya mayar da wayar aljihunsa a nutse yace” Ki gane Ayam, rayuwarki na cikin gagarumin had’arin da ubangiji ne kad’ai yasan iyakarsa, ba wai wani banza bane ke neman rayuwarki, masarautu ne suke wawarki, yayin da wasu daga gefe ma suka nemanki ruwan a jallo, dayawansu a shirye suke da su biya bilyoyin kud’i dominki, wasu alkairi ne a zuk’atansua game da ke, wasu kuma akasin haka, na d’auki alhakin kula da ke ne dan na ga na hana masu nemanki cin nasara a kan ki, ki bani dama ki kuma kwantar da hankalinki, hakan zai bani damar ceto rayuwarki.”
A sanyaye kuma a ladabce cikin sigar tausayi tace” Wane irin had’ari ne na ke ciki haka?”
Kai tsaye yace mata” Had’ari ne da ya kai matakin kisa, kamar yanda na fad’a miki kowa da manufar sa ta son samunki, wasu na nemanki ne kawai dan su kasheki.”
Tsoro k’arara ya bayyana a tare da ita ta zazzaro ido ta ji kayan cikinta na neman yamutsawa, ckkin muryar d’ar-d’ar tace” Me na aikata musu haka da suke son kashe ni?”
Da hannu ya mata alamar ta zauna kan gadon, zaunawa tayi tana rarraba ido dan tsorl ya gama kamata, a cikin aljihunsa ya ciro takarda, zaune yayi kusanta ya warware takardar ya mik’a mata yace” Karanta.”
Karb’a tayi ta fara karanta takardar dake nuni a cikin littafi aka cirota ko kuma an buga irinta ne, ba wani dogon bayani bane a takardar face zanannun zanen da aka tsara kuma aka wassafasu a cikin tsari ta hanyar fad’in _” A wace shekara ce? A wane wata? Wace rana ce wannan? Babu wanda zai sani a cikinmu, saidai alamun bincikenan malaman babbar fadar k’asar Texanda dake birnin Khazira ya tabbatar da za ta zo, za’a haifeta ne kawai dan zuwa da sabon tsari sannan ta wanzar da adalci, zuwanta shi zai kawo k’arshen duk wani azzalumi ko da sarkin dake mulki ne, zatayi mulki na ban mamaki da ba’a tab’a kwatanta irinshi a k’asar ba, zata kafa tarihi da dubbanin shekaru zasu shud’e ana magana a kai, tambayar a nan ita ce, *talakawan gari ne zasu haifo wannan biwar? Ko kuma cikin msu kud’i ne da iko ? Ko kuma dai wannan lu’u lu’u zata fito ne daga masarautar khazira*?”_
Da mamaki ta kalleshi dan abun bai wani d’ad’ata a k’asa ba tace” Me wannan ke nufi? Jaridar yaushe ce? Ko kuma labarin film ne, kana so na fito jarumar?”
Wani murmushi ya saki dan sosai ta bashi dariya, gyara zamanshi yayi yace”Kin fahimci me labarin ke magana a kai?”
Jinjina kai tayi ta yatsina fuska tace” Kusan haka.”
Shi ma jinjina kan yayi yace” Ayam wannan rubutun wani babban mutum ne yayi shi, wannan mutumin shi ma yana da baiwa irin ta wannan da akayi magana za’a haifa, sanadin baiwar da Allah ya masa gaba d’aya masarautar khazira aka shiga girmamashi, sanda ya sanar da abinda zai faru gaba ba kowa ya yarda ba, saidai kuma an zuba ido ana jiran tsammanin a ga ta inda wannan zab’abb’iyar zata sake fitowa.”
Gyara zama ya sake yi ya sauke numfashi yace” Shekara ta dubu biyu daidai wata na hud’u sarauniyar khazira ta samu ciki, tun samun cikin na ta sai wasu alamomi suka dinga bayyana mata a mafarkinta, bayan ta sanar da babban malamin fadar k’asar wanda yake jika ne ga waccen zab’abb’en, sai ya sanar da ita ai tana d’auke da cikin wannan ‘yar baiwar ce, sai gashi kam bayan wata shida ta haifi yarta mace wacce aka lak’abawa sunan *Zafeera* tun kafin ma a haifeta, wanda Zafeera yake nufin haske marar yankewa, a wajen wasu haihuwarta zai kawo k’arshen matsaloli da dama musamman na mulkin zalinci da sarki ke yi a wannan lokacin, amma a wajen wasu bayhanarta sharri ne da kusantowar rugujewarsu, hakan yasa a daren da aka haifeta, tun bata bud’i ido ta kalli mahaifiyarta ba sai aka nemeta aka rasa.”
Cike da jimami da rashin jin dad’i Ayam tace” Ayyah, to amma ya mahaifiyarta tayi? Gaskiya akwai tashin hankali.”
Siririn murmushi yayi yace “Ba kamar yanda kikayi hasashe bane.”
Gyara zama tayi tace “Ban gane ba?”
Kallon fuskarta yayi yace “Mahaifiyar da kan ta ne ta b’atar da ‘yarta ta hanyar damk’a amanarta ga amintacciyar jakadiyarta da kuma mijinta.”
Waro ido tayi tace “Toh? Amma gaskiya tayi k’ok’ari, kuma hakan ya k’ara tabbatar min da soyayyar uwa daban take.”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa sai kuma yayi shiru, ita ma d’an shiru tayi na dak’ik’u sai kuma ta kalleshi tace “To amma mahaifinta fa? Ban ji ka ambace shi ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke ya tsura mata ido yace “Ba da sanin mahaifin yarinyar ta bada ita ba.”
“Me ya sa to?” Ta tambaya tana tsareshi da ido, mik’ewa yayi tsaye ya juyo ya fuskanceta yace “Akwai wani al’amari ne a tare da shi mahaifin na ta, amma yanzu ba zan sanar da ke ba kai tsaye.”
Mik’ewa tayi ita ma tace “Me yasa to?”
D’auke idon shi yayi a cikin na ta yace “Ki tambayi wani abun daban ba wannan ba, lokaci ne zai fahimtar dake waye shi d’in.”
Girgiza kai tayi ta gyara tsayuwa tace “To amma me yasa ka bani wannan labarin? Kana da wata alak’a ne da masarautar Khazira ?”
Kallonta yayi sosai cikin tattausan murya yace “Bana da wata alak’a da ita, ai kin gani ni ga masarautar mu nan, amma fa ke kina da alak’a da wannan masarautar.”
Ya fad’a yana nunata da yatsa, zaro ido tayi tsabar mamaki sai kuma ta k’ank’ance su tana kallonshi kamar bata gane me yace ba, a hankalce ta shiga d’ora duka kalamanshi a mizani kafin daga bisani ta kalleshi tace” Wace irin alak’a? Na rok’eka Umad kar ka ce min labarin daka bani ina da nasaba da shi.”
Hannayenshi biyu ya zuba cikin aljijun rigarshi ta sanyi bak’a mai hula sannan ya kalleta yana sauke numfashi, jinjina mata kai yayi sosai sannan ya d’ora da fad’in” Tabbas, labarin dana baki ta ko ina kina da nasaba da shi, Ayam ke ce wannan yarinyar baiwar, ke ce lu’u lu’un Khazira, Ayam ke ce *Zafeera*.”
Zuba masa ido tayi, jiri ne ta ji ya fara d’ibarta, da d’an sauri ta shiga sauke numfashi tana girgiza kai tana so tayi magana, saidai tashin hankali da halin ba zatar data shiga ya fi knarfin d’aukar hankalinta, kafin ta ankara jirin nan ya kwasheta ya zubar a k’asa, dan dama tana tattare da matsananciyar yunwa ga baccin data kasa samu tayi.