CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

    Kallon kallo kawai suke ta yi kafin daga bisani ya mik’e tsaye cikin 6acin rai yace ” what the hell did you think you have done!!? Yaya zaki shigo min office ko sallama babu ? Ko kin dauka nan wajene wanda zaki shiga sakaka haka?” Ilham ta gyara murya tana juya manyan idanuwanta ta k’araso gaban table d’in tace ” seriously ka cika zak’ewa d’azu fa muka sha hirarmu da kai a parking lot ,yanzu kuma Kazo kana chanja salo anan nifa gaskiya banason irin Wannan ” Rasheed ya daka mata wani uban tsawa mai tsoratarwa ni kaina saida na girgiza balla ita da take kusa da shi yace ” don’t you dare lie at me!! Yaushe muka hadu da ke?? Kije chan ki nemi sa’an ki kar ki sake sa kafarki a office d’ina in kuma ba haka ba I will definitely ruin your career!! ” Ilham ta bushe da dariya tace ” lallai kuwa zamu ga waye zai yi ruining career na wani a tsakanin ni da kai ta buga table din da hannun ta a fusace ta fice ya bita da kallo yadda take rangwada ya k’ara tabbatar masa cewa y’ar bariki ce wannan ta asali ,shi gashi ko sunanta bai sani ba.
     Ya doki table din gabanshi da hannun shi hakan yasa har wasu takardu suka zube, yace ” what kind of life is this!! Shekaran jiya kawai na shigo k’asar amma komai ya cunkushe min, khaleel ya bi son ransa ya rabani da my precious and now all of a sudden ga wata jaka tana son shiga rayuwa ta babu dalili….. ” Duk abunda ya faru a kunnen Imtihaal ne don ta d’auko files zata kawo mishi ne ta hangi Ilham a cikin office din ,taji duk maganganun da yayi, tabbas hakan yayi tallying da maganar da suka so su sanar da ita shida Sadiq!!. Nan ta daskare ta kasa ko motsawa domin yanzu itama tayi believing cewa ba Rasheed bane na farkon ,because of the way he acted towards her!! A ranta tace but wannan ba shi bane zaisa nayi giving up so easily!!! Tayi wata yar murmushi.

      Tana cikin wannan yanayi captain ya fito daga office bata ma sani ba saida yayi banging k’ofa sannan ta tsorata ta dawo hayyacin ta ,kamar mai kinkina take magana a lokaci guda tana mik’a masa files din hannun ta, ” gashi wannan shi za’a turawa lieutenant colonel” tana kai wannan ta juya ta barshi a gurin shima da sauri ya bi bayanta ,ta shiga motar ta bai wani damu ba shima ya bud’e ya shiga. Motar ta d’auki silence na wajen mintina biyar ,Rasheed kuwa kawai k’aremata kallo yake yi yadda tayi matuk’ar kyau lallai uniform d’in ya karbeta sosai,ita ma kallon nashi take yi duk sun shagala. Khaleel ya fito kenan yana ta kad’a key d’in motar shi ya hango su ,ranshi a 6ace zuciyan shi na tafarfasa yace ” Oohh!! So this is it !! Ai bana so game din yayi over a nan kusa!! Rasheed ban yi expecting haka da wuri ba amma all the same tunda plan A bai zama accomplished ba lallai plan B zan sako a gaba believe me sai na tarwatsa maka duk wani farin ciki kamar yadda nima na rasa nawa farin cikin!!!! Ya ci gaba da tafiyar shi yana lalumar wayar shi a aljihu………..

WAYE KHALEEL??

???????? Jeeddah ja’o????????

[4/23, 12:13 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ???? 9⃣1⃣〰9⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

       Khaleel yana d’aya daga cikin soji masu bincike, aikin shi d’aya da Imtihaal saidai itace babba a gurin sun kuma san amfanin ko wanne irin makami daga k’arfin shi har zuwa weakness nashi da kuma yadda za’a sarrafa shi ,in fact duk wani file na abubuwan gurin yana hannun su ne……
      Khaleel yana da k’anwar shi mai suna Husnah ,kuma asalin haifaffun garin Kaduna ne ,transfer akayi mishi aka dawo da shi Abuja saboda kwazon shi kuma da kaifin basira ya karb’i lambobin yabo da dama, shi da imtihaal. A dalilin Imtihaal suka shaqu da Rasheed har suka zama friends. Husnah k’anwar khaleel tana matuk’ar k’aunar Rasheed yayinda shi kuwa Rasheed bai d’auketa a karan komai ba face k’anwa ,khaleel kad’ai ya san haka…

  Wani lokaci kimanin shekaru uku da suka wuce khaleel ya umarci Husnah da ta bayyana sonta ga Rasheed kuma ta yarda, ta samesu zaune shida Al’amin suna hirar Imtihaal sai ta ‘boye a bayan wani pillar tana jin su. A nan ne hankalin ta ya tashi domin kuwa Rasheed ya bayyana irin son da yake wa Imtihaal kuma yanda ya bayyana ta tabbatar babu abunda zai iya shiga tsakanin soyayyar shi da ita bai kar shi ba!:oops:ko Al’amin ma kasa cewa komai yayi don yasan yadda zuciyar Rasheed take in har aka tab’a abun da ya riga da ya shiga ranshi!!
  Husnah ta ruga a guje ta nufi gida ,khaleel na zaune ta wuce shi da gudu tana kuka bata zame ko ina ba sai cikin d’akin ta ,ta rufe , khaleel yayi yayi ta bud’e tak’i bud’ewa hankalin shi ya tashi.

  A bakin k’ofar ya kwana har gari ya waye yana tashi kamar zai bud’e kofan kuma sai ya fasa yayi tunanin bacci take yi ma ,sai ya wuce masallaci ,kusan k’arfe bakwai ya shirya zai fita sai ya gwada murd’a door handle din kawai kofar ta bud’e………

    Tunda yake bai tab’a shiga tashin hankali irin na ranan ba , a gurin ya durk’usa jikinshi na rawa kamar mazari ,yana hawaye da kuka mai sauti na ban tausayi ,ya d’aga kanshi yana kallon ta Kwance bakinta duk Jini har ta hanci ga kumfa ,wasu kananan magunguna a zube  a k’asa hannunta guda ta damk’e wata paper ,ya d’aura kanta a cin yarshi yana hawaye yana karanta abunda ta rubuta.

     Mikewa yayi tsaye idanuwan shi duk sun kad’a sun yi jajir ya damk’e paper d’in yana ambaton sunan Rasheed har wajen sau uku sannan ya fice daga d’akin ,dama basuda kowa sai k’anwar baban su itama tana cikin gari don tayi aure ,anan akayi janaiza ,khaleel tun daga wannan ranar ya dauki alkawarin sai ya zubar wa Rasheed hawaye domin dalilin shi kanwarshi ta hallaka kanta kuma ita ce Hasken idanuwan shi a rayuwa bashida abunda ke saka shi farin ciki irin Husnah.. Amma kuma cikin ruwan sanyi ya yi niyyar yi.

Wannan yasa lokacin da Rasheed zai yi tafiya zuwa Pakistan General Abubakar Rasheed ya zabi khaleel yayi shige irin na Rasheed domin kar a yi suspecting wani abu a base ,saboda shima Rasheed da wata fuska zai shiga Pakistan din ,mission din ba karami bane , khaleel ya ji dadi da jin haka yana ga kamar wannan shine step na farko da zai fara amfani da shi don rusa farin cikin Rasheed, kafin ya tafi kuma babu wani day to day activity na Rasheed da khaleel bai sani ba ,domin dole ne yayi acting as Rasheed, harta lokacin da Rasheed ke waya da Imtihaal an sanar da shi ,da duk wasu abubuwan da ya kamata ya sani tunda shi basajan Rasheed ne!!…..
Zuwan Ilham ya ‘kara masa k’arfin guwiwa na tarwatsa soyayyar Rasheed da Imtihaal!!
 Wannan kenan

????????Jeeddah ja’o????????
[4/24, 9:05 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????9⃣6⃣〰1⃣0⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

       Imtihaal ta murd’a key d’in motar ta fice a d’ari ,shi kuwa Rasheed na zaune yanda yake yana kallonta bata fasa gudun ba kuma ba hanyar da ya kamata subi ta bi da su ba , da yaga abun natan na yi ne sai ya ce ” park d damn car Imtihaal ko so kike ki hallaka mu ne?bata bi ta kanshi ba ,direct wani city Hall ta wuce da shi shi de bai yi magana ba tun daga wancan maganar ta bud’e kofa ta fice  shima hakan yayi ya bi bayanta though bata umarce shi da ya yi hakan ba…..

   Hall d’in cike yake da sojoji wad’anda ake damawa da su a Army wasu ma bak’i ne daga Niger ,totally Rasheed ya manta da za’a yi taron tuni ya fara Sosa ‘keya Imtihaal ta juyo sai dariya take masa ,da iPad d’in hannun ta ta bugi kafad’ar shi  sannan ta wuce ciki ta barshi nan a tsaye ranshi fal farin ciki yau abunda yafi soyuwa a zuciyar shi ta yi managing to forgive him???? sannan ya wuce ciki.

   Major Ali wato mahaifin Imtihaal ya ji dad’in ganin reunion d’in y’arsa da Rasheed domin kuwa babu abunda ke burgeshi irin yaga y’ar shi cikin farin ciki kasancewar ta marainiya , bata samu motherly love ba sai daga gurin mahaifiyar Rasheed abunda ya sake ‘kara musu shakuwa kenan, ta kula da ita ta kuma tarbiyyantar da ita bisa tafarki na addini ,ita dai matsalar Imtihaal dama chan a fannin dressing ne da makeup shine kad’ai Inna ta kasa gyara mata don in tayi kokarin yi to bazasu wanye lafiya ba. General ma ya ji dad’in ganin hakan ba kad’an ba.

   Kowa ya ci yasha ana ta murna amma banda khaleel da ke zaune yana kallon su ,yayinda ganin shima yana cikin damuwa kamar yadda take ciki yasa Ilham itama ta yi joining nashi, suka d’an fara hira. “Amma Muryar ka seems familiar ! Kamar na tab’a jin Muryar ka at several occasions gashi kuma sai yau na tab’a ganin ka” abunda Ilham ta Fadawa khaleel kenan. Murmushi kawai yayi ba tare da ya amsa ba ya d’auki glass cup yayi sipping sannan ya maida kallon shi ga su Imtihaal. Cikin ranshi yace ” Celebrate all you want !! Day will come that your laughter will turn to streams of hot tears!!!!

????????Jeeddah ja’o????????
[4/25, 6:23 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣0⃣1⃣〰1⃣0⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      Alhamdulillah komai ya dawo kamar yadda yake tsakanin Rasheed da precious nashi kamar basu taba samun sabani ba, suna tafe a hallway din headquarters na defence sai zuba Imtihaal take yi kamar aku ,in da sabo ya saba da irin surutai na Imtihaal saboda haka baya damun shi Sam!!

       Uncle Hashim da uncle Hamman da kuma wasu guda biyu su ma dattijawa ne zaune a falon sun Imtihaal an tarbesu sosai cikin karamawa ,daya daga cikin dattijawan wanda da ka ganshi kaga General don suna kama ya fara magana bayan ya gode ma ubangijin sammai da kassai, ” Major Ali , wato abunda ke tafe damu ba wani bak’on abu bane face maganar nan ta nemawa d’an mu Rasheed auren d’iyar ka Imtihaal…. Kafin ya k’arasa Major yace ” Haba !! Toh yanzu banda General da abunshi ai Imtihaal y’arsa ce ,yana da iko akanta yana da ikon bayar da ita ga duk wanda ya chanchanta, kar fa a manta Imtihaal ta samu kyakkyawan tarbiyya ne daga gurin su ,sune komai nata domin ni nayi imani sunan uba kawai naci ,Nikam a gurina wannan ba matsala bane , with all my heart na amince hundred percent. Duk suka fara hamdala ana godewa Allah ,sai a lokacin kawu Hamman yace ” toh muna dad’a godewa Allah ,Allah kuma ya yi mana jagora yasa ayi a sa’a???? ya karashe maganar da wani murmushi Marar adadi, nan bayan sun d’an yi hira suka kama hanyar tafiya ,Saidai basu tafi ba har saida suka tabbatar an sa ranar auren nan da wata d’aya!! Farin ciki fal ran General Abubakar da Inna domin sun fi kowa sanin yadda d’ansu da Imtihaal ke kaunar junansu , Sadiq da Al’amin kuwa suna samun news din suka k’udiri niyyar yi masa albishir saboda haka Inna ta fasa k’iran sa ta sanar da shi ,ita ma dai Imtihaal bata san wainar da ake toyawa suna chan suna harkokin su.

    Ilham na tafe tana ta rangaji kamar bazata taka k’asa ba ,a cikin wannan yanayin kamar ance ta d’ago kanta sai tayi ido hud’u da Khaleel yana zaune sai kalle kalle yake yi yadda kowa yake safa da Marwa kullum nan ne wajen zaman shi dama , k’arasa wa tayi inda yake ta zauna a gefen shi tana k’are masa kallo kafin daga bisani ta ce ” Jiya da dare a gurin partyn nan you luk some how disturbed da ka ga Rasheed tare da Imtihaal !! What is the problem ? Khaleel yayi wani mahaukacin dariya ,ya zari karan sigari guda daga aljihun rigar shi ya kyasta ashana ya d’an zuk’a kafin ya ci gaba da cewa ” kina so kisan ma’anar wannan kallon da nayi musu ne?? Sai ya mik’a mata card nashi ,yace meet me tomorrow by 8:00 pm a arena zan fayyace miki komai ” yana kai Wannan yayi murmushi ya tashi yana gyara rigar shi kafin ya take sauran sigarin ya yi tafiyar shi ,yayinda ita kuwa ya barta nan ta sak’a Wannan ta kunce wancan…….

????????Jeeddah ja’o????????
[4/26, 4:00 PM] Jeeddah ja’o????: ☄???? CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣0⃣6⃣〰1⃣1⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

        Imtihaal na isowa  gida  ta iske Dad a Falo yana kallon news, cike da fara’a ta yi sallama tak’arasa cikin falon  shima fuskar shi cike da annashuwa ya d’auki remote ya rage muryan TV sannan yace ” my little darling! Welcome back home” cikin langwami ta k’arasa kusa dashi ta zauna k’asa yayinda shi kuma yana sama tace “Sannu da hutawa Dad! Naje dubaka a office baka nan Wai baka fita ba ,I hope komai lafiya?” Major yayi murmushi yace ” ah lafya lau my princess , bak’i nayi ne kuma they are very important persons ,in fact they are here for you!” Imtihaal ta zaro idanuwa waje tace ” Ni kuma Dad??  I just hope ba wani matsala, dad in ma maganar files din ne na riga na gama aikin su, mutumin baya Nigeria yanzu haka yana south Africa shi da wasu yaransa guda uku ,komai na gama bincikowa Dad bayar da su ne ban yi ba.” Tana kai wannan Dad ya katse ta kafin ta sake fad’ar wata Kalmar ” Ba wannan zancen bane my daughter! This one is different, daga gidan su Rasheed ne aka turo don nema mishi auren princess d’ina ,you see now my little princess is all grown up gashi zata yi aure tabar Daddy;) ya yi winking mata ido.
        Cikin jin kunya ta rufe fuskar ta da hannayenta tana dariya ta mik’e da sauri tayi upstairs shi kuwa Major dariya ma ta bashi, ya girgiza kai yace ” Bafulatana kawai sarkin kunya????..,…….

      Karfe takwas daidai ta iso Arena (Eagle square stadium) tana shigowa taga gurin wayam kamar ba kowa, sai cikin field d’in wasu matasa suna training duk da wannan daren , stadium d’in koda alluran ka ne ya fad’i zaka iya samu, guri kawai ta nema ta zauna sannan ta fiddo da wayarta don ta k’ira shi amma kafin tayi dialling k’iran shi ya shigo ,kai tsaye ta d’auka ta kara a kunne ” ki duba left side ta inda kike zaki ga wani a zaune kanshi rufe da hood ki karaso inda yake ki zauna.” Abunda khaleel ya fad’a mata kenan gami da katse wayar.
        Ta tashi ta nufi inda ya sanar da ita ta kuma zauna kusa da mutumin, bai wani 6ata lokaci ba ya yaye hood din daya rufe fuskar shi ya juyo sukayi ido hud’u:oops:

Gabanta ya fad’i ta mik’e tsaye tace ” Raaash….ed!!! What are you doing here captain?!!! ” khaleel da ya saka fuskar roba irin na Rasheed yayi wata muguwar dariya yace” come on take your sit ! Meye kin wani firgita kamar wanda kika ga dodo??”

    Saida Ilham ta samu natsuwa tukunna don tun lokacin da Rasheed ya mareta take tsoron sa. Khaleel ya yaye mask d’in da ke fuskar tashi, a nan ya kwashe labarin duk abunda ke faruwa tun daga mutuwar k’anwar shi har tafiyar Rasheed da kuma dawowan shi ,har ma da fansa da yayi niyyar d’auka akan Rasheed!………..

     Ilham ta mik’e tsaye ta kama kunkumi tana karewa Stadium d’in kallo kafin ta ce ” Lallai wannan wasan zai yi kyau !!! Kai zaka rama abunda Rasheed yay ma k’anwar ka ne ,ni kuma zan d’auki fansa ne akan Imtihaal ,she is my target kaga kenan duk tafiyar d’aya ne. Rasheed ya sa hannu ya mari fuskata amma ba laifin shi bane laifin wannan gud for nothing d’in ne ,da nayi zaton samun shi is easy but tunda har maganan auren su ake yi this means ya min nisa saboda haka in jifa ta tsallake kai na ta fada kan koma waye!!” Duk suka bushe da dariya khaleel ya matso kusa da ita yace ” Yauwa y’ar gari!!!!”………….

????????Jeeddah ja’o????????
[4/27, 10:11 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣1⃣1⃣〰1⃣1⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

        TWO WEEKS LATER……..

  Yau saura sati biyu kachal auren Rasheed da Imtihaal, su Ruky kam tun daga yau ma tana hanya abunka da kirjin biki????. Rasheed na zaune a office yana waya, jin ‘karar bud’e k’ofa yasa yayi saurin d’agowa a zatonshi Precious d’in shi ne ,amma sai yaga akasin hakan domin kuwa Mujaheed ne tare da Al’amin da Sadiq suka shigo, yayi murna sosai ba kad’an ba ganin mutane masu muhimmanci a rayuwar shi irin su ne suka shigo ya zagaya suka yi hugging juna cike da shauqi yace ” Guys wallahy kun zo at the right time coz am very confused!!” A tare suka kwashe da dariya Mujaheed yace ” Kad’an ma ka gani within these weeks sai ka ma fi haka ramewa! Al’amin yace ” bama wannan ba tukunna  akwai  fa sauran abubuwa a gaban mu ,come on take the whole day  off! Muje mu k’arasa sauran shopping da zamuyi”  Rasheed ya had’e rai yace ” Gaskiya ni bazan fita haka in uniform ba ,akwai zafi zan nemi kayan da zan sha iska. Mujaheed ya katse shi da wuri yace ” tab!! Ai kana shiga gida nasan bazaka fito ba saboda zaka had’e da kakcy kuyi ta hirar ku da bata k’arewa.

     A haka suka jashi ya fita shopping din ba tare da ya koma gida ya chanza ba.  Suna gamawa about k’arfe takwas na dare kawai suka nufi silver bird chilling a movie theatre???? ba su suka bar silver bird ba sai kusan sha d’aya saura. Suna shigowa ko kula su bai yi ba suka jidi kayayyakin ya na ta musu dariya suna shigewa ya juya ya nufi side d’in kakcy nan ya zauna suka bud’e sabon shafin hira in takaice muku sai kusan karfe biyu ya samu ya kwanta don saida ya tabbatar ta samu bacci ko da suka gama hirar ma……….

????????Jeeddah ja’o????????
[4/29, 9:58 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CIGABAN CAPTAIN RASHEED????☄
Episode ????1⃣1⃣1⃣〰1⃣1⃣5⃣????

      Safiya mai cike da Ni’ima, ruwan sama suka tashi da shi marka-marka garin shiru alamun kowa yana indoors. Rasheed yayi juyi a hankali yake bud’e idanuwa har ya tashi ya zauna kuma ,ya sake dukunkunewa a bargo.

Duk abunda yake yi Sadiq na zaune a kan reading chair rik’e da jarida yana kallon shi bai sake motsawa ba har Sadiq ya kammala abunda yake yi yayi wanka ya shirya tsaf still mutumin bai tashi ba ,a hankali ya d’ebo ruwa mai sanyi a fridge ya watsa masa.
A firgice Rasheed ya Mik’e ya bi bayan Sadiq da gudu har downstairs k’arar wayar Sadiq ne yasa suka tsaya Rasheed ya bugi kafad’ar shi sannan ya wuce ya nufi d’akin su Inna don su gaisa daga nesa Sadiq yace ” bro Karfa ka manta karfe sha d’aya zamu fita , look at the time yanzu its almost 10:20am ka shirya da wuri pls:roll:. Ko kulashi Rasheed bai yi ba ya d’auki glass na fresh fruit drink ya wuce side na mom yana dariya.

  Imtihaal da k’awayen ta Ruky kaxs , Mrs Zainab Ahmad and Zeetu ne zaune suna shaqatawa a Grand palace anyi serving nasu spring rolls da banana milk shake suna ta chilling da ka gansu kasan daga shopping suke suka d’an tsaya su yi chilling don ga dukkan alamu basu ma gama ba.” Yan mata kuyi sauri mu tafi mana nifa Wollah na fara jin bacci” Zeetu ne ke maganan lokaci guda kuma tana wasa da bakin glass na milk shake nata. Imtihaal ta hararota ta ce “toh  Sannu kasa sarkin bacci kin fi waye jin barci ki duba fa kiga tun nine muke yawo yanzu wajen sha biyu ai in baccin ne ma duk zamu fara complain ba ke kad’ai ba???? Ruky kaxs ta kwashe da dariya tace ” Nidai yanzu ku tashi mu karasa gurin kayan nan muga ko an gama dinka wa. Zainab Ahmad dai bata ce ‘kala ba ta mik’e tsaye duk suka fice bayan sun yi settling bill

????????Jeeddah ja’o????????
[4/29, 11:38 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣1⃣6⃣〰1⃣2⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

     Suna fita har zasu shiga mota kamar anche “kalli chan ” Ruky kaxs ta hango motar su Rasheed sun yi parking ,Rasheed yana jingine a jikin motar yayin da Sadiq da Mujaheed suka shiga wani shop. Ruky ta d’an buji hannun Mrs Zainab Ahmad tace ” kinga chan mutumin fa” ta nuna Direction d’in da yake,Zainab tace ” heee!! What a coincidence gashi kuma fa Chan muka nufa! Imtihaal ta kauda kai ta tsare ,Wai sai sun bar gurin zata je. Zeetu tace ” toh Sannu!! Mukam kinga tafiyar mu in kinga dama ki biyo mu tunda ai kayan naki ne. Duk suka wuce suna zolayarta suka barta a gurin kamar gunki….

  Rasheed na kallon duk abunda suke yi kawai ya basar ne kamar bai gansu ba. Ganin sun tsallaka sun barta yasa ta yi sauri itama don ta tarosu tana isa tsakiyar kwaltan kawai wata bak’ar mota Jeep Prada mai tinted glass ta yi wuf ta gabanta ,ko da motar ta wuce duk suka nemi Imtihaal suka rasa.:oops:

 Rasheed ya yi wurgi da papers na hannunshi ya shige motar kamar zai tashi sama ,yana wani mahaukacin tuk’i ba tare da ya saurari traffic light ya bashi right na movement ba ya kutsa kai da gudu mai tsanani, yana bin bayan wannan motar wanda itama gudun take yi kamar zata tashi sama. Cikin y’an mintina motar ta 6ace masa dalilin Wutar da ta kama daga bonnet na motar duk da ya samu ya tsaya amma k’ofar motar tak’i bud’ewa gashi kuma hanyar kamar babu kowa sai buga k’ofar yake yi amma ta kame. Haka hayak’i yayi masa over ya kasa yin komai  gashi kuma Wutar bata daina ci ba…..

  Motocin fire fighters ne da su Sadiq ga kuma Ambulance da kuma y’an K’ungiyar Red Cross suka iso da kyar aka samu aka cire k’ofar motan aka fiddo da shi Sadiq cikin matsanancin kuka yace wa su Ruky su wuce gida kawai shi zai tafi asibitin a ambulance da Rasheed, Ya kuma umarci Mujaheed da ya sanar da General abun da ake ciki……

???????? Jeeddah ja’o????????
[4/30, 6:49 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣2⃣1⃣〰1⃣2⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      “What!!?” Innalillahi wa inna-ilaihirrajiun!! Wane asibitin?? Ok I’ll be on my way” Abunda General ya iya cewa kenan da Mujaheed ya sanar da shi abunda ake ciki a waya, Hankalin kowa ya tashi saboda haka Inna ma tace bata ga ta zama ba,tare suka nufi asibitin da Dad d’in Imtihaal mutumin da ba’a ma sanar da shi halin da y’ar shi ta shiga ba….

   “Doctor pls do your best to save him!! Pls I beg of you!  Plssss!!” Cikin rudani da tashin hankali Sadiq yake maganar, Dr ya sa aka dakatar  dashi daidai kofar emergency room. “You have to stay here sir ,wait outside pls” Abunda d’aya daga cikin nurses d’in ya fad’a kenan yayinda suka k’arasa tura Rasheed dake Kwance rai a hannun Allah a kan stretcher…….

    Inna ta kasa zama sai kai kawo suke daga ita har Sadiq. Abbah ya k’araso kusa da Sadiq gami da dafa kafad’ar shi yace ” Be a man my son in shaa Allah He’ll be alright I know he’ll fight through it instead of being worried why not pray for his wellbeing! Nasan yadda kake ji a ranka yanzu coz baka da wani wanda ya wuce Rasheed but I want you to be strong my son”
  Sadiq ya sake fashewa da kuka, cikin kuka yace “Abbah in da nasan haka zai faru bazan tilastawa Rasheed sai Mun fita ba a wannan lokacin, kuma sannan da bamu je wajen ba da motar su kawai zasu shiga su koma gida, amma saboda sun ga Rasheed a tsaye ne suka taho, and now my friend is hospitalized because of me and his fiancé Imtihaal is being kidnapped !! Dum!!!! Kirjin Inna ya buga ta juyo cikin rudani tace ” Imtihaal!! Ta rik’e hannun Sadiq iya  k’arfin ta ” Yaya akayi haka ? Ina aka kaita? Su waye suka d’auke ta?? Ka sanar da ni mana Sadiq ba magana nake maka bane ??!!” Tana magana tana jijjiga shi. Da kyar ya bud’e baki yace “Inna nima ban sani ba, hankali na baya tare da ni ,am very confused! Bansan ta ina zan fara ba ya sulale ya zauna kan wani waiting chair yayinda Major Ali (Dad d’in Imtihaal) tuni ya riga ya saddaqar, suna cikin wannan yanayin likita ya fito daga emergency room, da sauri suka ruga domin suji lafiyar Rasheed.

   Doctor !!yaya jikin nashi ? How is he?!! I hope he’s alright ? Likitan yayi murmushi gami da dafa kafad’ar Sadiq yace ” yes !! D’an uwanka yana nan lafiya ,he just suffer some cases of suffocation ,kasan hayak’i ne yayi masa yawa hakan ya sa duk wani air pass way nashi suka kusa daina function ,its good kun kawoshi Twenty minutes earlier da ina tabbatar muku da cewa we couldn’t have save him ,kuma ku godewa Allah (S.W.T) Domin shine me yin yanda yaso kuma a lokacin da yaga dama, ya kaddara cewa d’anku yana da sauran kwana a nan gaba. In kun gama ina son ganin mahaifin patient din a office nawa pls akwai wasu papers da zai yi signing a kai da kuma wani muhimmiyar magana da zamuyi……..

????????Jeeddah ja’o????????

[5/1, 8:18 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣2⃣6⃣〰1⃣3⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

     Sadiq ya d’an nisa sannan yace ” doctor, zamu iya ganawa da patient d’in kuwa?” Likitan ya juyo da murmushin shi yace ” No my son! Yanzu bazai yiwu ba har sai Mun yi transferring patient din zuwa VIP room tukunna sai ku duba shi but for now yana buk’atar Hutu saboda, ka ‘kara hak’uri……

      K’arfe takwas na dare Inna tana zaune kan kujera as a gefen gadon Rasheed tayi jigum ta k’ura masa ido Sadiq ya jingina da bango ya nad’e hannuwan shi a kirji idonshi a kan Rasheed baka jin k’arar komai a d’akin sai na na’urar da take aiki. Bud’e kofar da likita yayi ne ya dawo da su daga tunanin da suka shiga duk suka maida duban su ga likitan.
  ” Har yanzu soja bai tashi bane? Inna ta d’an yi murmushin dole tace Eh bai tashi ba. Likita ya gama dube duben da zai yi sannan yace” zai iya farkawa a ko wanne lokaci daga yanzu you need to stay closer to him because zai iya tashi cikin ko wanne yanayi depending on abunda ya faru da shi, don’t worry we’ll also stay alert:)
Inna kai kawai ta girgiza ba tare da ta tanka ba……

???????????? ????????????

   Gudu motar take yi kamar zasu tashi  sama tun da Imtihaal ta hango yadda motar Rasheed ke cin wuta yayin da yake bin bayansu ta saddaqar babu wani mai cetonta sai mahaliccin ta saboda haka ta yanke shawarar amfani da k’arfin da Allah yay mata, mutanen da suka sa ta a tsakiya sukayi mata alluran bacci ganin tana neman zubar da su gaba d’aya da motar a take ta sulale ta zube k’asa sannan suka samu natsuwa suka nufi hanyar zuwa Lagos..,……..

    A hankali yake motsa hannun shi ,idanuwan shi suna bud’ewa kafin su ankara yayi wuf ya mik’e yana faman fizge cannular dake hannun shi Sadiq yayi kokarin rik’e shi ya fizge kamar mahaukaci da kyar ya iya furta sunan Imtihaal. Sun ga hauka iya hauka kam a wannan daren don saida akai mishi alluran bacci tukunna hankalin kowa ya kwanta ,shi dai buk’atar shi ya fita neman masoyiyarshi bai kuma damu da halin da yake ciki ba…….

 My dear readers!!:) kar ku ga kamar ana ja muku rai ne dalilin rashin turo muku da wuri ,Aa Sam ba haka bane ,kwata kwata I am busy this days ,but I’ll continue squeezing tyms at least to make ur day!! Luv you all!!

   ????????Jeeddah ja’o????????

[5/3, 11:01 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣3⃣1⃣〰1⃣3⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

       A hankali ta bud’e idanuwan ta tana bin d’akin da kallo ba tare da ta motsa jikin ta ba, d’akin babba ne sosai babu komai cikin shi sai wani yamutsatsen katifa wanda take Kwance a kai daga nan kuma sai band’aki wanda ko marufi bashi da, window’n d’akin nada matuk’ar tsayi yadda duk kokarin mutum bazai iya kaiwa ba batare da ya nemi wani abu da zai taka ba. A nutse ta tashi ta zauna tana sake kare wa d’akin kallo ,wanda duk farin fentin ya k’ok’e ya zama brown don datti ga kuma Cobwebs ta ko ina musamman ma k’ofar band’akin a takaice dai d’akin ya yi shekara da shekaru bai samu tsafta ba.

    Gaba d’aya abun duniya ya dameta ta rasa ta ina zata fara , tana cikin wannan yanayin ne aka bud’e kofa, cikin sauri ta Mik’e tsaye gami da k’ura masa ido ???? gaba daya ta kasa tunanin abu daya, gani take kamar mafarki take yi. “Khaleel!! Me kake yi anan kuma? Ina nufin daman kai ne ka sa aka d’auko ni??” Khaleel yayi wata muguwar dariya yace ” Baby!! I hope you are not surprised coz bana expecting haka daga gareki , wannan ai irin aikin mu ne ko ba haka bane? By the way naga kamar yunwa na damunki ko? Bari yanzu a kawo miki abinci, in yaso sai na dawo anjima muyi magana ko?”. Imtihaal tace ” bana buk’atar sauraron ka ,koma me zaka ce ina so ka mayar da ni inda ka d’auko ni sannan ka sanar da ni ,a yanzu bazan saurareka ba !!!” Dariya kawai khaleel yayi ya juya saida ya isa bakin k’ofa ya tsaya chak ba tare da ya juyo ba yace ” Hmmmm Baby kenan babu matsala ai ,kiyi ta zaman har sai lokacin da kika yi ra’ayin sauraran abunda zan fad’a miki sai ki sanar da ni ,ni yanzu na tafi…….

  “Haba Sadiq!!! In su sun hanani tafiya ai kai bazaka min haka ba ,bazan iya barin Imtihaal all alone haka ba I have to go and rescue her , nasan zata tsammace ni this is the best time for me to show her how much I loved her ,pls brother I need to get out of this hospital!!!” Sadiq yayi shiru na d’an wani lokaci sannan yace ” ok amma saidai mu tafi tare coz I can’t leave you go out there alone!!” Ba tare da Rasheed ya amsa masa ba ya mik’e tsaye gami da zare drip d’in da ke hannun shi ya soka alluran a jikin katifan ya sakala takalman shi suka fice daga wurin cikin sirri. Suna fita basu zame ko ina ba sai defence headquarters duk abubuwan da Rasheed ke buk’ata ya d’eba sannan suka kama hanyar barrack. Rasheed na zaune a mota Sadiq ya shiga cikin gidan ya d’ebo musu abubuwan da zasu buk’ata ya fito babu kowa a falon duk suna side d’in kakcy……..

   Hanyar da accident din ya afku suka nufa ba tare da sun san ina ne ainihin inda kidnappers d’in suka nufa baa………..

????????Jeeddah ja’o????????
[5/3, 11:39 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣3⃣6⃣〰1⃣4⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

     “I told you Ilham cikin sauk’i zamu cimma burin mu ,yanzu nasan babu d’aya daga cikin iyalan biyu da hankalin su ke Kwance cikin nutsuwa, musamman shi lover boy din Looser Rasheed” khaleel kenan yayi maganar hannun shi rik’e da glass na ruwa. Ilham tayi wani murmushi tace ” ban san me ya rasa ba a jiki na da har zai so wancan kazamar, lallai sai na 6ata mata fuska sai muga wanda zai biyota da sunan wani abu Wai so!!! ” ta mik’e tsaye tace yanzu zan bata zab’i ta rabu da shi ko kuma in kashe ta kowa ya huta!! Khaleel ya mik’e tsaye yana faman kunna sigari yace ” Oh come on! Kema kin san da kamar wuya ace ta janye, kuma in kin kasheta ai baki rama ba bazai tab’a jin ciwon sosai ba kamar yadda zata gama numfashinta nan k’arshe a gaban shi, nifa babu komai a raina da ya wuce fansa!! Kamar yadda na rasa farin ciki haka shima sai na dandana masa bak’in ciki Mara misaltuwa!!! Sai yayi bak’in cikin da yafi wanda nayi!!! Ina tabbatar miki da cewa in kinga ban tarwatsa rayuwar Rasheed. Ni k’anwa ya kashe min amma kuma itace farin ciki na ,tunda shi bashi da wani farin cikin da ya wuce Imtihaal sai na tarwatsa mishi farin ciki ,the game has just begun !! Wannan somin tab’i kenan!!!” Yana kai wannan ya bushe da wata muguwar dariya.
    Ilham kuwa cikin zuciyarta cewa tayi ” Amma fa wannan mutumin da gaske yake!!” Ita kanta tasan nata wasa ne a kan nashi domin Kishi kawai ne ke damun ta…

     Inna tana ta kai kawo a cikin VIP room d’in asibitin (d’akin da Rasheed ke  jinya) hankalin ta a tashe , sauran ma sun yi jigum musamman Al’amin da Mujaheed. “Wannan wane irin yaro ne Rasheed!? Pls ka sake trying numbern Sadiq ko za’a same shi. Al’amin ya sake dialling numbern wannan karon ya shiga amma ba’a d’auka ba. Haka suka tattara suka koma gida, Isarsu Falo Inna ta yanki jiki ta fad’i cikin sauri aka kaita d’aki ,Abbah ya kira Dr Mufeen domin ta duba lafiyarta………..

     Jikin ta na rawa saboda wani mugun zazzabi da ke neman rufeta, a hankali ya bud’e k’ofar gamida wurga mata leda d’auke da take away da kuma robar ruwa guda d’aya , haka ya saba yi mata cikin kwanaki hud’u da tayi kamar wata dabba ,ya juya zai fita tace ” Kai!!! Wai ni me nai maka ne a rayuwa!!! Me na tare maka !? Kazo ka ajiye ni kamar wata dabba ka kulle a keji ,sai wulak’anci daban daban ,ni gaskiya na gaji ka fitar dani daga nan gurin in ba haka ba…….!! ” In ba haka ba me!!!!??? ” ya katseta da sauri sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta ,karan sigarin da yake sha kawai ya manna mata a kafad’a tayi wani ihu ,shi kuwa dariya kawai yake yi irin na k’eta. Ilham na jin ihun ta rugo gami da banko k’ofar d’akin ,jin hakan yasa ya d’auke karan sigarin yana kallon Ilham yayinda take ta Ajiyar numfashi kamar ita aka sawa Wutar ………..

      Shin Ilham tana tausayin Imtihaal ne ko kuwa har yanzu tana kan bakan ta?!! Ku biyo ni a next episode domin jin yadda zasu k’are!!

????????Jeeddah ja’o????????
[5/3, 12:13 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣4⃣1⃣〰1⃣4⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

       ” Kinga !!! Wannan shine babban dalilin da yasa bana aiki da mata!! Tausayi baya d’aya daga cikin akida na ,tausayi ya dad’e da barin zuciyata bashi da gurbi ko na misqala zarratin!! Saboda haka in har Kinsan you cannot control your patience with abunda nake aikata wa sai ki daina sauraron abubuwan da zanyi domin sanin kanki ne ban kawo Imtihaal nan gurin don taji dad’i ba ,ba kuma don a bani kud’i ba! She is here because ina so in d’au fansa!! Ilham ta mik’e tsaye ta fice ba tare da ta ce k’ala ba kai tsaye ta shige mota ta zauna , sai da ya gama guntun juice nashi dake glass cup sannan ya mike yana gyara kwalar riganshi shima ya fice ya isketa a motar ,ba tare da ya tanka mata ba ya tada motar suka bar gurin,………..

   Imtihaal har ta saba domin muddin suka sa kafa suka fita wannan lokacin toh baza su dawo ba sai washegari k’arfe takwas ,dan fursuna ma ya fita jin dad’i da walwala…
   ” Rasheed Lagos kuma? Kana tunanin zasu tsallake duk garurruwan da ke kan hanya kuwa? Rasheed yayi murmushi yace ” ga Abun da yasa nace maka Lagos suka nufa, ya nuna masa wani numberplate na mota da ke jefe a ‘kasa kusan kilometres uku daga inda accident d’in ya faru da kuma wani ID card jefe a gefen plate din wanda yayi indicating wanda ya jefar a Lagos yake , Rasheed ya cigaba da cewa ” mistakenly aka jefar da wannan kuma basu damu su d’auke plate d’in ba saboda suna tunanin still ana biyo su ne ,a garin shiga motar ne ID d’in ya fad’i ‘kasa ,saboda haka Sadiq Lagos muka nufa!!” Sadiq cike da mamaki yace ” you are right bro!! Come on!!! Suka shiga mota a take suka d’au hanyar Lagos………..

        “Al’amin Rasheed bai dawo ba ko? ” Inna da ke Kwance ne keyin wannan tambayar kafin ya bata amsa wayar shi tayi ringing ,yana d’agawa yaga Numbern Rasheed jiki na rawa ya d’auka ” Hello Rasheed ina ka shiga ne haka? Ga Inna ta damu sosai tana son ganin ka ,pls tell me ina kuke ne ?? Daga dayan ‘bangaren Rasheed yace ” lafiya nake Bro! Ina hanyan Lagos state pls I ka bawa umma wayan! ” babu musu ya mik’a mata cikin sauri ta mik’e zaune ta kara a kunne ” My son !! Yaya zaka tafi haka! At least sai ka sanar da mu inda kake baza mu hana ka ba , amma ka tashi ka tafi cikin dare duk hankalin kowa ya tashi kum…..  Ya yi saurin katseta da ” Mom don Allah kiyi hakuri kawai na kasa daurewa ne ,wannan shine lokacin da zan nunawa Imtihaal that she’s adored by me ,iyaka kaunar da zan nuna mata kenan in je in yi rescuing nata daga hannun mutanen da suka d’auke ta. Kuma na tabbatar Mun kusa cimmusu domin kuwa Mun samu clue wanda zai iya taimaka mana mu sameta, albarkar ki kawai muke buk’ata da kuma addua????????. Inna ta yi ta musu addua tana sa musu albarka kafin daga bisani ta mik’a wayar ga Al’amin… Inna ta samu relief da taji Muryar d’anta.

????????Jeeddah ja’o????????
[5/4, 1:16 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣4⃣6⃣〰1⃣5⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

    ” Victoria island ne address d’in jikin katin, me zai hana mu tafi a matsayin bak’i a gareshi ,in har mutanen area d’in suka sanar damu inda zamu iya samun shi sai mu far masa cikin sauk’i amma yanzu in mukaje kai tsaye ,akwai possibility zai iya sanin ko ni waye ,I definitely have this feeling saboda haka Sadiq inaga dole mu nemi Al’amin domin nasan he will play it well , amma kafin nan yanzu mu fara bincike ko waye wannan  Yusouf Adewonmi d’in !!” Duk Rasheed ne ke wannan maganar yayin da suke tsaye a bakin bar beach na Victoria Island????…

       A gurguje ta shigo hannunta d’auke da sachet na anti_malaria da kuma bottle na ruwa ta mik’a mata, sai da ta kusan mintina biyar sannan ta karb’a ta sha ,itade Ilham batace ‘kala ba ta juya zata fice ,Imtihaal da bata da wani ishashen k’arfi ta kamo k’asar rigarta tace ” yanzu ke da kece a position d’ina ya zakiji! Tell me the truth from d bottom of your hrt !!! Wanne irin reaction zaki bayar?? Kar fa ki manta ke mace ce , kawai saboda son zuciyar ki zaki kai kanki ga halaka,a yanda mata ke da raunin nan kina tsammanin khaleel ko da ya kashe ni zaki zama free ne?? Dole kema zai dinga bibiyar ki domin zai yi tunanin zaki fallasa duk wani sirri nasa da kika sani ki je kiyi tunin irin hadarin da ya jefa ki a ciki babu ghaira babu dalili kun sato ni, kina tunanin haka zan dawwama cikin wannan kurkukun naku ne? Ko da ba raina nasan dole sai kun fitar dani waje me kike tunani ne Ilham?? Nasan yanzu kina tunani ko abunda nake fad’i gaskiya ne ko?? This is not the right time to think ,Kije ki samu nutsuwa ,yanzu abunda ya fiye miki shine ki fice daga nan tun kafin ya shigo ya ga cewar yau har kin rigashi shigowa daga nan kuma sai ya fara doubting abilities naki as a villain!! ”

   Da sauri Ilham ta fice ba tare da ta juyo ba ta danna key din ta rufe yadda yake sannan ta tafi fitanta kenan ta hango motar shi yana shigowa gidan tuni ta lab’e bayan wata k’ofa har saida ya wuce ciki sannan ta fice ta bar gidan. Tafiya yake yana murmushi irin na k’eta har yakai bakin k’ofar d’akin ya saka key ba bud’e, yana shiga kamshin turaren Ilham ne ya fara bugan hancin shi yayi wata muguwar dariya irin na k’eta sannan ya k’araso cikin d’akin kai tsaye yaja kujerar sa da ya saba zama ya ya zauna
   ” tun yaushe ta shigo d’akin nan??? Me kuma kuka tattauna? Imtihaal tayi banza da shi ta kauda kanta gefe. Ranshi a bace ya zabura ya shak’e ta kana ya had’a ta da bango ya kaura mata mari. ” ba magana nake miki bane !! Tell me when exactly did she come in ,and what did she told you what are her plans!! ” Imtihaal ta hankad’a shi gefe guda duk gashin kanta ya barbaje tana ta huci a lokaci guda tace ” OVER MY DEAD BODY!!  Ta tofa masa miyau a fuska , kusan minti biyu bai d’ago ba ya zaro tissue a aljihun shi ya goge fuskar tashi yana wata muguwar dariya sannan ya d’ago gami da doketa ta bayan hannu ta zube a k’asa warwas bakinta ya fashe ,cike da nuna jarumtar ta ta sa hannu ta goge jinin tana masa wani mugun kallo ,ji yake kamar ya shaketa,ta sheqa lahira amma tukunna so yake ya gama sanin take taken Ilham!!! Yayi wata yar karamar tsaki sannan ya juya zai fice ,karaf idonsa ya kai kan maganin da Ilham ta kawo mata ya durk’usa zai d’auka ko me ya tuna ,kuma sai ya fasa ya juya ya fice daga d’akin kamar kullum ya rufe k’ofar yayi waje……

    A hankali take sulale wa a jikin bango har ta kai ‘kasa duk tayi gumi gashin ta ya mammanne a fuskarta ,doguwar rigar jikinta kuwa tayi duku’n-duku’n dalilin fad’uwar da tayi, domin d’akin kura ne kawai da datti . zazzafan kuka me sauti irin na ban tausayi take yi na takaicin irin mugun yanayin da suka saka ta take yi, bakinta addua kawai ya iya furtawa a wannan lokacin ,domin tasan Allah ba azzalumin kowa bane sai wanda ya zalunci kansa…………..

????????Jeeddah ja’o????????
[5/4, 2:35 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 2
Episode ????1⃣5⃣1⃣〰1⃣5⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

        Zaune yake cikin wata mota yana danna wayarsa,ya toshe da bak’in gilashi hannun sa guda yana buga jikin stirring motar, ” hey Wai ya haka ne??? Tun d’azu nake jiranka shiru pls let’s settle this once and for all!!” Yana kai wannan ya katse wayar gami da yin tsaki.
   Sanye yake da bak’ar vest da wando 3quater yana wasa da key d’in motar shi da yayi parking a chan gefe yana tafiya irin na bosawa????. Kai tsaye motar da khaleel ke jiranshi ya shiga ya zauna gami da rufe k’ofar ba tare da ya furta magana ba.
     Khaleel yayi wannan shu’umin murmushin da ya saba sannan ya zare glashin fuskar shi yace ” Yousuf!! Nasan by now you are fed up by yanda nake treating naku for not paying you guys properly amma ba haka bane ,I have double your money but sai ka min wannan last aikin da zan saka ,duk da ma dai nasan this is not the right time but ina so ka zama ready domin ina suspecting  wani abu ne , for now kayi manage da wannan kafin in waiwaye ka ” ya mik’a masa bunch ba dubu d’ari d’ari guda uku (dubu d’ari uku) da kyar Yousuf ya karb’a sannan yayi masa sallama ya fice daga motar rik’e da ledar kudin……..

   motace k’arar Mercedes Benz a chan gefe suka yi parking suna kallon isowar Yousuf domin gaba da baya suka tafi ,basu gaza ba bayan ya fita suka bi bayan shi har ya isa k’ofar wani Bar a nan duk y’an iskan abokanan shi suke chilling. Rasheed ya juya yana kallon Al’amin yace ” yanzu ne ya kamata kayi making first step naka, ka tabbatar lallai lallai ka samu connection da shi , kayi acting wise har ya yarda ya biyoka make sure you work this step with charisma da kuma brain naka ,coz nasan gayen mugun d’an air ne!! In har ya biyoka shikenan zamu yi duk yadda zamuyi mu samu information daga gareshi” Al’amin yayi murmushi gami da dafa kafad’ar Rasheed yace ” You can count on me bro!!” Ya fice daga motar shigar da yayi ma da ka ganshi kaga shigar y’an air:D.

        Mata da maza kowa kawai sai sha’anin gaban shi yake da masu rawa da masu shan giya babu ruwansu , Al’amin na d’aga kai ya ya hango Yousuf d’in tare da abokan sa guda biyu suna zaune kan kujeru table d’in gaban su kuwa babu kwalbar da babu sai fama suke. Da gangan Al’amin ya zo wucewa ya banke wani daga cikin waiters d’in gidan duk na cikin glasses din da ya d’auko suka kware a jikin Yousuf, kafin su ankara  Al’amin ya chukume waitern.” Kai wane irin kidahumi ne ! Gara dalla chan baka gani ne ,kana tafiya kai a sama kamar mai tallen hayak’i!!! Baka ga oga Yousuf bane a nan ,dubi fa yadda ka zuba masa giyar nan a jiki eh? Wai kai tukunna ma me kake ji da shi ne ??! ” yana magana ne irin na y’an iskan y’an daba d’in nan ,Hakan yayi impressing d’in Yousuf ya wani baje yana murmushi yaran shi ma haka, da gangan ya d’aga hannu zai kai punch a wannan waitern sai Yousuf ya hana shi” dakata!! Kyaleshi ya tafi !! ” Al’amin ya sake yin fuskar y’an duniya yace ” hey oga ai da da ka barni na gyara mar zama ai!! Ni ba’a yi wa oga na wulak’anci in kyale ehe!!”

   Yusouf yayi wata muguwar dariya yace ” I like that charisma and courage in you!! Kai d’in namu ne! Pls join us kai a kawo masa kwalba d’aya!!!” Sadiq sanye da kayan waiters d’in gurin ya tunkaro gurin d’auke da kwalba guda amma saidai ba giya bane a ciki ,sannan Yousuf bai san Sadiq ba shiyasa ya shigo freely. Al’amin ya d’aga kwalbar a take ya kafa kai bai sauk’e ba saida ya shanye tas, hakan yaja hankalin jama’a sai tafa mishi ake shi basu san ba giya yake sha ba ,su kuwa sai dirkar giya suke yi duk sun bugu ,shima yana ta biye musu sai Marisa suke yi. Da wayo ya jawo su duka hud’un suka kai cikin motar su sannan Al’amin ya k’ira Sadiq shima ya fito gami da wurgar da kayan aikin gurin da ya saka a cikin shara????……..

????????Jeeddah ja’o????????
[5/5, 9:04 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 3
Episode ????1⃣5⃣6⃣〰1⃣6⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

 “Sweetheart Ilham I didn’t expect pity from you to that bloody bitch!! Amma kin bata rawar ki da tsalle, kar ki manta ni fa ba yaro bane !! Kin barni babu wani zab’i da ya wuce in aikata hakan!!”
 “Khaleel pls!! Wallahy ni bazan iya bane ,I promise you bazan tab’a fallasa ka ba ,amma ni na ajiye makaman yak’i na!! I realize I have no reason to be jealous of Imtihaal, Allah ne bai yi ba cewa Rasheed nawane saboda haka I quit!! ” Ilham ta katse wayar ta yayinda shi kuwa khaleel yayi wurgi da tashi wayar a fusace duk ta tarwatse a k’asa ya dauki glass d’in giya ya kurba sannan ya dauko wata wayar daga aljihun shi ya yi dialling numbern Yousuf don suyi magana amma kwata kwata a kashe take, haka ma na sauran yaran nashi, ya buga tsaki tare da buge glass cup din da ke gefen shi ya tashi ya nufi d’akin da Imtihaal ke kulle.

     Mik’ewa tayi cikin sauri ganin yadda ya shigo yana Marisa da ka ganshi kasan ya bugu, Gadan-gadan ya nufota tare da wanketa da wani mari ya mak’ure ta a bango ” ke!!! In the first place Kinsan dalilin da yasa na kawo ki nan?? Toh in baki sani ba kisani!! Na kawoki nan don in razanar da ke daga k’arshe kuma in kashe ki kuma babu wanda zai ceceki!!!” Murya k’asa ‘kasa tace ” toh me nai maka kake son ka kashe ni?” Ya yi wurgi da ita gefe guda sannan yace ” baki yi min komai ba Imtihaal!! Hasalima baki san komai da yake faruwa ba ko da abun ya faru baki nan a k’asar!! Ya juyo a fusace ya nufi inda take gami da durkusawa gabanta yana waina y’ar k’aramar wuk’ar hannunshi yace ” baby bakida laifi , kuskuren ki d’aya ne da kika kasance kece farin cikin me laifin! Rasheed !!”
     A fusace ta mik’e zuciyarta na dukan uku uku tana girgiza kai tana ja da baya” A’a…… A’a!!! Wannan ba mai yiwu wa bane! Rasheed ba mai fitina bane Kaje chan ka nemi wanda yay maka laifi ba shiba kuma in ma shine yay maka laifin wannan wane irin laifi ne da zai sa ka d’auki mataki da kanka ina kabar hukuma??

“Hahahahahahhh!!!! Hukuma!! Hukuma ai bazata yi min adalci ba iri wanda na buk’ata!! Wannan alamarin ni ne hukumar kaina!!Husnah ta kasance komai na rayuwata bamuda kowa ita kad’ai ne family na!! Ta nuna min tana k’aunar Rasheed na umarceta da ta sanar da shi amma kafin tayi hakan taji cewar wata ta riga da ta maye wannan gurbin da take nema, hakan yasa ta kashe kanta don taga its the best solution ,again kuma don ta samu relief amma ni har yanzu na kasa samun relief mutumin da dalilin shi na rasa k’anwa shine zai samu farin ciki mai daurewa? NO!! Bazai tab’a faruwa ba!! Na sha alwashin rabashi da duk wani farin ciki na rayuwa!! Sai ya d’and’ana bak’in ciki a rayuwar sa !!!”

      Imtihaal na jin wannan tace “Amma lallai ka cika Mara imani da tunani, duk wannan abubuwan da suke faruwa shi wanda kake yi a kansa bai san cewa kana yi ba! Hasalima bai san wata ta soshi irin haka ba bai kuma san dalilin mutuwar ta ba!! Kai kuma kana wahalar da zuciyar ka ne domin da Husnah tana son Rasheed zata zauna ne tayi winning love dinshi ko ta yaya , ba Wai ta gaza ta kashe kanta ba!! Wannan ya nuna gudun halin da zaka shiga ciki idan har ta rasa abunda take so tayi ta kashe kanta ba Wai gudun halin da zata shiga ba!!” Tass!! Saukar mari ne har guda hud’u Imtihaal taji a fuskar ta wanda yasa ta gigice ta d’auke wuta :idea:bai tsaya bata lokaci ba ya luma mata y’ar wuk’ar nan a ciki ya sake zarewa ya mayar yana gamawa ya zare wuk’ar ya fice ba tare da ya rufe k’ofar ba. Abunda Imtihaal da ni kaina Jeeddah bamu sani ba shine ashe tun tuni ya kunna gas a kitchen d’in wannan tsohon gidan ya mamaye ko ina ,yana ficewa ya wurga ashana ciki kafin kace wani abu har gidan yayi exploding:oops:…………..

????????Jeeddah ja’o????????
[5/5, 9:43 AM] Jeeddah ja’o????: ????☄CAPTAIN RASHEED☄???? Season 3
Episode ????1⃣6⃣1⃣〰1⃣6⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      “What!!  You mean an biya ku million d’aya domin ku kamo ta ?? Meaning mutumin da ya baku aikin nan ba kud’i yake nema ba daga gurin mu, yana da nashi dalilin na daban !!? Al’amin ne yayi wannan tambayar hannun shi rik’e da pliers babba yayinda su Yousuf suke d’aure a jikin kujerun katako salim na zaune shima a gefe yayinda Rasheed yake zaune a gaban Yousuf sun yi facing juna.
 Rasheed yace ” now tell me ! Waye ya aiko Ku ku aikata hakan ga yarinyar da bata da wani aibu me tayi muku? Yousuf yayi wata muguwar dariya yace ” kiss my ass!!! ” Rasheed ya kaure shi da mari yace ” How dare you, now you tell me who assigned you to do such thing or I cut out your finger!! ???? Yousuf ya tofa ma Rasheed miyau a fuska ,a take fuskar Rasheed tayi ja tsabar wani tafarfasa da yaji zuciyar shi na yi ya kama yatsar Yousuf ya fincike ???? cikin tsawa yace “NOW TELL ME !! INA KUKA KAI MIN ITA!!!?” Cikin yanayin firgici da tashin hankali d’aya daga cikin abokan Yousuf yace ” nikam zan fad’a pls kar ku cire min yatsa, ni wannan ba hali na bane dole ce tasa nayi domin ina buk’atar kud’i don kammala karatu na!! Wallahy zan fada amma don Allah ku kyale ni in tafiyata pls !!!

 Rasheed yayi murmushi yace “Good!! Fad’amin abun da ka sani duk ! Ni kuma na maka alk’awari in har na tabbatar gaskiya ka fad’a toh lallai I will file for your freedom amma in kuwa k’arya kayi toh ka tabbatar zan sheqe ka!!” Mutumin yace “Wani ne mai suna captain khaleel shi ya bamu wannan aikin amma kuma bamu san manufar shi ba akan ta mudai ya bamu hoton ta da kuma duk wani shige da ficen ta ya kuma umarce mu kar mu tunkari inda take sai Mun tabbata babu kowa tattare da ita.”
  “CAPTAIN KHALEEL!!! CAPTAIN KHALEEL!!! Rasheed ya maimaita sunan har sau uku sannan yace Sadiq kunce shi” Sadiq ya kunce mutumin Rasheed ya dubeshi yace ” Muje ka kaimu inda yake Ajiyar yarinyar first!! ” suna fita kenan a bakin hotel d’in da suke suka ci karo da Ilham anan ne ta zayyano musu komai da ya faru sannan ta nuna musu cewa ita ta riga ta yi giving up, ta kuma nemi gafara a gurin Rasheed bawan Allah cikin ruwan sanyi ya yafe mata.

      Suna isowa gidan babu abunda yake fita sai hayak’i ko ina ya k’one. Ilham ta sa ihu ta fice da gudu ta nufi k’ofar suma duk suka dunguma suka yi gurin, wutan kam ya mutu don kanshi amma akwai guraren da basu daina ci da Wutar ba , a rud’e duk suka shiga ciki hayak’i sai tari yake saka su basu zame ko ina ba sai hanyar d’akin da Imtihaal ke amma kuma abunda ya d’aure musu kai shine babu ita babu labarin ta jikin Ilham ya dau rawa ta zube a k’asa tana kuka Rasheed ya tsaya kamar an dasa shi .

      Ilham ta mik’e tsaye da sauri tace ” kuga !! Tayi nuni da hannun ta zuwa floor d’in d’akin duk suka maida dubansu gurin , Jini ne yayi layi har ya isa bakin k’ofa daga nan kuma basu sake ganin inda jinin yayi ba sanadiyyar toka da ya zuba a floor d’in. Rasheed yace ” She’s alive !! Tayi escaping ne ya ruga ya fita suma suka bi bayan su daga k’afar fita kuwa suka fara ganin d’igon jinin yabi wata hanya ta daban haka suka dinga bin hanyar da k’afar su har ta fitar da su bakin titi….

    Daga nan basu san kuma inda tayi ba ,cikin sauri suka koma suka d’auki motar su basu zame ko ina ba sai General hospital domin shine asibitin farko da yake wannan hanyar a tunanin su nan ne first place da duk wanda ya taimake ta zai je  amma ina babu ita babu labarin ta…………..

????????Jeeddah ja’o????????
[5/5, 10:37 AM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED ????☄season 3
Episode ????1⃣6⃣6⃣〰1⃣7⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

   ” Sannu ko? Ni sunana Dr Mufeen daga specialist Hospital a Abuja nazo nan ne don attending wani conference da Association of Nigerian medical doctors ta had’a ,kuma accidentally na sameki helpless a bakin titi ,nasan akwai mysteries a tattare da ke but ina so ki nutsu tukunna ki trying ki matar da kanki komai for now and relax don kina buk’atar Hutu for a while , akwai dinki a jikin ki yanzu haka so pls bakya bukatar kwakwaran motsi.

 Tana magana ne kawai amma Imtihaal ba sauraron ta take ba ,tunanin ta Halin da Rasheed yake ciki da kuma mahaifin ta, a haka har bacci ya saceta…….

     Rasheed na zaune kan kujera Sadiq ya mik’a masa take away na abinci , ba tare da ya kalli ma meye ba ya sa hannu ya ture yayi wani ajiyan numfashi gami da duba tym yace Wai me Al’amin ya tsaya yi ne a waje har yanzu ?? Sadiq yace ” wa ya sani ne kasan shi da son kallon stars maybe yana chan yana fama. Rasheed ya ce ” k bari in dubo shi tun dazu ya kawo min recharge card d’in ya kasa kuma network din is somehow not clear today , na kasa recharging through mobile phone ????. Sadiq de bai ce qala ba Rasheed ya fice abunshi..

       Daidai third to the last step na stairs d’in suka ci karo duk magungunan da ta siyo suka fashe, Dr Mufeen ta ce ” Subhanallah!! Malam ya haka? Ina kake kallo ne ?? I really need this medicines now ,gashi kuma duk sun fashe I have a patient kuma na barta ita kad’ai tun d’azu sannan I have to check on her , yanzu ya zanyi!?? ” Rasheed yace am sorry ,don Allah kiyi hak’uri its just that I was desperate ,ki bani list na magungunan ko a ina ne zan nemo in kawo ,am sorry once again!” Mufeen ta d’an yi Jim sannan tace gashi nan ta mik’a masa list d’in har ya fara tafiya tace ” room number 102″ ya juyo gami da girgiza mata kai ya fice. Kafin kace wani abu masu aikin hotel din har sun gyara gurin da magungunan suka fashe……….

    K’arfe tara dai dai ya dawo d’auke da maganin kai tsaye ya wuce room 102 kamar yadda ta sanar da shi ya Kwankwasa k’ofar in no time ta bud’e k’ofar ,ya mik’a mata tayi murmushi ta karb’a yace ” I just hope ban yi latti ba?” Maganar nan da ya furta ya doki kunnen Imtihaal da ke Kwance ta firgita ta fad’o daga kan gadon tana neman hanyar k’ofa, Mufeen tayi murmushi tace you are just in tym ,suka yi sallama ya juya kafin ta rufe k’ofar Imtihaal tace Ccc.. Aaaa… Ptain.. Wannan Kalmar captain d’in ta doki kunnen shi amma sai bai kawo wani abu a ranshi ba ya wuce abunsa amma tun da ya dawo d’aki ya kasa samun sukuni gaba d’aya.

  Sati biyu kenan cir Rasheed bai ji wani improvement ba ,yau kamar kullum sun fito zasu fita neman ta kamar yadda suka saba ,chan ma Abuja an samu labarin khaleel sun kuma yi nasarar chafke shi amma yana nan a rufe ne , domin ya ki confessing komai kuma ya nuna bai san komai ba.
       Tana tafe tana Jan k’afa a hankali hannunta kuma guda d’aya na cikinta d’ayan kuma Dr Mufeen ta rik’e ta ” kar ki damu Imtihaal ai if am not mistaken yanda kika bani labarin ki ,na tabbatar it was your captains that I treated a asibiti , kwanan shi d’aya ya tafi neman ki ,look nasan duk yadda akayi yana nan yana ta neman ki kum……. Kafin ta k’arasa Ilham tace ” Imtihaal!! Imtihaal stop !!! A rikice ta juyo tana kallon Ilham wanda tun tuni ta riga ta k’araso inda suke tsaye..

   Tun yaushe muke neman ki da captain munje  har haunted house din nan bamu same ki ba ina kika shiga ne pls???? Imtihaal pls forgive Me I was so selfish that I couldn’t even think about others!! Amma na gane kuskure na ! Don Allah ki yafe min pls ???????? Imtihaal cikin kuka tace ” babu komai ai ya wuce ,its good kin yi realising mistakes naki before its too late babu komai na yafe miki:'(

  Mufeen tayi murmushi tace ” yanzu ina su captain d’in suke? Ilham cikin sauri ta mik’e tace ,sun fita neman ta ne bari nayi musu waya kuzo muje d’akin da suke, a d’an tsorace Imtihaal tace ” Me zai hana mu jira su a nan kawai?” Ilham ta juyo da d’an guntun murmushi tace “I know baza ki tab’a trusting d’ina ba right?” Imtihaal tayi murmushi jiki a sanyaye suka bi bayanta har d’akin da su Rasheed suka kama…….

????????Jeeddah ja’o????????
[5/5, 5:56 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 3
Episode ????1⃣7⃣1⃣〰1⃣7⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

          Kusan mintina talatin sannan suka k’araso hotel d’in kai tsaye suka shigo d’akin ba tare da wata wata ba.
  MY PRECIOUS!!! Ya fad’a yayinda ya k’arasa jikin gadon da take jingine ya zauna gabanta cikin kuka tace ” Hanny !! I’ve missed you a lot!! I have been tortured by him so much that I can never ever forget!! ” ta rik’e kwalar rigarshi tace ” where have you been?? Na jira zuwanka, da yanzu bani da sauran numfashi a doron k’asa Hanny !! Ya cutar da ni sosai ba a kan laifi na ba! Kuma ya zarge ka da cewar Kaine silar mutuwar k’anwar shi Husnah ,saboda Wannan ya k’udiri niyyar raba ka da farin ciki! Hanny I tried to convince him that baka da masaniya akan soyayyar  Husnah but he couldn’t believe me! Ya sokeni da wuk’a sannan ya yi setting house din on fire, saboda rashin tausayi ,yayi tafiyarsa ya kyale ni, da Jan ciki na samu na fito ,ga k’unar wuta ga ciwo , Captain ina kuka tsaya ne ????!!!

  Rasheed cikin hawaye yace ” relax my precious am here now ! Ya gyara mata pillown ta koma ta jingina sannan ya kwashe labarin komai ya sanar da ita. Da kyar ta runtsa a daren ranan domin ji take yi kamar zaa zo a sake d’auke ta duk da ma bayan Ilham tana tare da Dr Mufeen.

       Karfe takwas na safe jirgin su ya tashi daga Lagos zuwa Abuja ,tafiyar da bata wuce 45 minutes ba by air. Kowa da kowa an hallara domin tarbar su kama daga iyayen da y’an uwa har ma da wasu tight friends na Rasheed da Imtihaal , hand bag dake hannun ta ta wurgar kamar ance dole sai tayi gudu ta ruga , Dr Mufeen tace ,kar kiyi gudu mana !! Ko a jikinta domin a lokacin bata jin komai a tare da ita ,Inna ta rungume tana kuka itama Innar haka , ranar de Mufeen  taga reunion mai ban tausayi ????. Tana cikin haka ta hango nata ogan ???? tare da wata nanny ta rik’e wani handsome baby boy da bai wuce two years ba , da fara’ar ta tanufi gurin su ta karb’i Yaron yayinda Nanny ta karb’i luggage d’in nata.” Oh I missed you my Little Areef! Mummy loves you much more!!???? tayi kissing kumatun shi yayinda shi kuwa yake ta kyalkyata dariya , Oga na daga gefe yayi folding hannayen shi yace ,hala baby Areef kad’ai kika gani Abban Areef kuma ko oho!???? da sauri ta juyo tace ” Oh look at you !! Ai ka girma da oyoyo???? but don’t worry I’ve something special for you !! Yanzu de mu tafi Wollah ni a gajiye nake sosai!! Murmushi yayi ya mata nuni da hanya yayinda ta shige yana biye da su a baya.

   A wajen airport d’in ne ,su Imtihaal suka gabatar da Dr Mufeen and her family yayinda Areef ya mak’ale ma Inna da kyar ya koma gun momyn shi a nan suka yi sallama ,motar su Mufeen na tafiya suma suka shige tasu suka bar gurin basu zame ko ina ba sai main house d’in su Rasheed wanda yake Asokoro domin nan ne zai iya d’aukan guests d’in su gaba d’aya Abba ya umarci Dad d’in Imtihaal da ya zauna a other side na gidan kawai domin it will be more safe than ayi bikin a chan main House na su Imtihaal da ke Maitama haka ya hak’ura aka ci gaba da shiri ,nan da sati ,yayin da aka saka ranar da za’a gurfanar da khaleel Ranar Monday wato bayan sati da auren su Imtihaal. Su Yousuf kuwa suma an dawo dasu nan Abuja ,anan za’a ci gaba da tsaron su har ranar da za’a yanke musu hukunci daidai da abun da suka aikata!! Domin Rasheed ya ce is better kar suyi ido hud’u da khaleel kafin a yanke mishi hukunci don za’a iya kifar da shi………….

✍????????Jeeddah ja’o????✍????
[5/5, 7:25 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 3
Episode ????1⃣7⃣6⃣〰1⃣8⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      Kwance take a kan darduma ta yi rigingine da 3quater a jikinta da kuma wata bak’ar top ,da alama ta saka ne don kar lallen ta ya tab’u, sai hira suke da k’awayen ta Serdy Maskara ne da Hersna suka shigo da shopping bags nik’i nik’i suka zuba a gurin ba tare da kowannen su ya tanka ba , Zeetu ta bisu da kallo tace ” hehehe an yo halin kenan tun daga hanya:D ! Serdy Maskara ta watso mata wani kallo tace ,kin jita fa !! Se kace kema bakisan halin Hersna ba???? she always take the first step Wai kinji daga cewa takalmin yayi min kyau tay karaf ta d’auke kuma shine last piece a mall din Wollah ko ki bani ko in hana ki sawa a bikin ehe:roll:. Ruky kaxs da ke gefe ta ce wallahy kun ban wata yar bakauyiyar dariya ???? ni na zaci ma har kun yi settling issue d’in takalmin ,toh yanzu dai ba wannan ba kuzo muje karb’o sauran dinkin amaryar haute couture tukunna! Hersna ta zaro idanuwa waje tace ” Ku tausaya min in k’ara hutawa Wollah a gajiye nake dazu tafiya nake amma kamar yar giya ???? duk suka bushe da dariya Ruky tace Haba mana pls kunsan fa gobe ba tym zamu samu ba , nan ma de da rikicin suka tashi Ruky na musu dariya ,Imtihaal kam in da sabo ta saba da halin su tun suna boarding school lokacin a Queen Amina college.

      “Sadiq I told you am tired pls ku bari na huta mana!!!” Al’amin da ke gefe yace ” ka huta a ina?? Ai kai da Hutu sai nan da bayan two weeks lokacin am sure daga kai se sister in-law ????! Rasheed ya jefa masa pillow yayinda Al’amin ya kauce yana dariya  Rasheed ya mik’e gamida zira rigar shi half jumper ya kafa hula sannan ya kwashi wayoyin shi suka fita.

      Yau take jumma’a !! An d’aura auren Imtihaal Major Ali da Rasheed Abubakar Rasheed (General). Taro yayi taro kowa ya shaida jama’a an yi murna babu abunda ke bakin yan uwa da abokan arziki sai fatan alkhairi. Bangaren angwaye kuwa ba’a misalta farin cikin da suke ciki a wannan lokacin haka ma 6angaren amaren????????.

Dr Mufeen na zaune bakin gado tana gyara wa amarya zaman dankunnen ta wanda da ka ganshi kasan asalin silver ne K’arar dubai pink lace ne gown a jikinta dankwalin kuwa launin satin ne ash colour kamar takalman k’afarta ,tasha kyau iya kyau ba’a magana domin idan guri akwai Ruky babu bukatar wata professional makeup artist!!
   Biki yayi biki ,daga kamu da akayi ran Alhamis, walima da dai sauransu komai ya tafi yadda ake so Alhamdulillah.

Ana shirin kai amarya abokan ango wad’anda ya had’a harda soji suka yi escorting bride yayinda Rasheed na chan side nashi tare da Al’amin, Sadiq, da Mujaheed, sai faman zolayan shi suke yi, k’arfe takwas na dare Abban Areef yazo d’aukan Dr Mufeen , tayi sallama da k’awayen amarya kan cewa gobe zata yi attending Honouring ceremony da Yan uwan Rasheed wato military personnel suka shirya musu don nuna murnan auren nasu ☺

    Gidan me kyau ne 3 bedroom ga babban palour da kuma kitchen wannan ba wani gida bane illa gidan da Rasheed ya taso a ciki kuma yayi wayo ,wannan ya tabbatar ma Imtihaal cewa rumours da taji cewa Abban Rasheed zai yi resigning gaskiya ne ,renovation kawai aka yi a gidan amma kamar ba a Nigeria ba don in ka shiga kamar kar ka fita ko nan da kofa!

      Ceremony yayi ba k’arya ,anyi parading ba kad’an ba ,a gurguje har Mr President yayi attending , a nan ne General yayi announcing resignation date nashi wato ranar Monday bayan an saurari karar su  khaleel wanda a yanzu haka an yi striping nashi off his ranks!

Stadium d’in ya cika iya ba k’arya kuma bikin ya kawayar! K’arfe hud’u na yamma kowa ya watse an gama komai abubuwa sun tafi yadda ya kamata sai godiyar Allah!

     “Ilham baki bani amsa ta ba har yanzu, kar fa ki manta da Rasheed da kuma Sadiq duk tafiyar d’aya ne ” Rasheed kenan yayi wannan maganar idon sa cikin na Ilham……..

  Nawaooooo readers kunji fa !! Nima dai JEEDDAH nayi mamaki ,ashe  Sadiq ma yana ciki kawai de ya basar ne , hehehe!!am surprised!!

 ✍????????Jeeddah ja’o????✍????

[5/6, 12:12 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ Season 3
Episode ????1⃣8⃣1⃣〰1⃣8⃣5⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

     Dariya kawai tayi ta dukad da kai ‘kasa ,shikuwa Sadiq na zaune cikin mota gurin driver ya kallesu yace ” a tsaya dai b’ata lokaci mu makara kaga dai gwara mu kai mata abunta ko ya kuka ce frndz? “Duk cikin raha suka ce dats right! Gwara kam a rakashi kar mu yi latti amarya tayi maganin mu ????..

     Rasheed dai kawai kai ya girgiza musu ya shiga motar Sadiq na tafiya yana tuk’i a hankali kamar ba tafiya suke ba duk don neman tsokana.” Oooooohhh!!! Dude in ka kasa driving d’in ne sai kabawa wani ko ni ka bani in yi kayana???? ni har na gaji da zaman motar!!” A tare suka bushe da dariya Sadiq ya juyo ya kalleshi ta gefen ido yace ” Haba bro !! Me kake ji na baka na zuba !! After all gidan ka zamu kai ka fa ba wani waje ba ,have patience naga ma wataran sai ka gaji da gidan ;)!” What !! In gaji da gidan bayan my precious na cikin gidan? Kaima kasan its way too impossible!! ” haka dai sukayi ta yi har aka kai gidan……….

   Yau lahadi ne ,kuma gobe Monday shine ranar da za’a gurfanar da su khaleel a gaban kuliya, kasantuwar weekend ne Rasheed na gida yana shanawa da amarsu.
 “My precious tashi ki bani rigana mana pls ???????? Imtihaal da ke Kwance sanye da rigar khaki d’in shi ta d’ago manyan idanuwan ta tana kallon shi, take ya durk’uso jikin gadon yace pls pls☹. Ta tashi zaune hannunta rungume da pillow tace ” shikenan weekend d’in ma sai a saka wani meeting me yasa baza a bari Monday ba , ni bazan bada rigar nan ba saidai Kaje a haka” Rasheed yayi murmushi yace ” Oooo Hanny !! You are acting as if bakisan fitinan mutanen nan ba! I really have to be there ,kuma d’aya uniform din na kai laundromat da safe, pls ki bani wannan d’in na saka.
   Da ‘kyar ya karb’i rigar don gudun rigimar ta ma a palour ya saka rigar don yasan in yayi sake zata wafce ya gano so take ta b’ata masa lokaci yayi latti ,dama tun asalin shi ma babu aure ma ya saba latti balle kuma yanzu:D

  Cikin sati d’ayan nan Sadiq da Ilham sun daidaita kansu sosai kamar wanda sun dade suna tare abun dai se godiyar Allah………

✍????????Jeeddah ja’o????✍????
[5/6, 3:26 PM] Jeeddah ja’o????: ☄????CAPTAIN RASHEED????☄ season 3
Episode ????1⃣8⃣6⃣〰1⃣9⃣0⃣????
Na ????Jeeddah ja’o????

      “Bayan kotu ta saurari shaidu da kotu ta gabatar ,da kuma amsa laifi da shi wanda ake tuhuma da laifin sace Mrs Imtihaal A. Rasheed da sace ta tare da tsananta mata horo da kuma niyyar kisan kai da ya yi ,ga Imtihaal , kotu ta yanke wa Mr Khaleel hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso tare da mukarraban as wato Yousuf Adewonmi, Zak ,Bolaji. Captain Ilham kuma dalilin had’a kai da tayi aka yi wannan aika aikan da ita kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata uku a gidan kaso!! ”

     Ilham ta d’aga ido ta dubi Sadiq yayinda ya sakar mata murmushi sannan yayi Mata nuni da hannu cewa ta kwantar da hankalin ta yana tare da ita ,anan ta samu relief


    Alhamdulillah komai ya tafi daidai yadda ya kamata ,khaleel ya yi getting even better than abunda yayi deserving amma duk da haka sun tausaya mishi domin ba laifin shi bane amma kuma ba laifin kowa bane, kuma its good that ya amsa laifin shi da kanshi ba tareda an jaa abun da nisa ba. Rasheed da su Imtihaal suna fita kenan shima aka fito da shi ya nemi a bashi yan mintina yayi maga!

Previous page 1 2 3

Leave a Reply

Back to top button