DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL


Tun da ya koma gidan yaki yarda sam su hadu da Mummy, rufe kansa yayi a daki ya cigaba da aikin da yake na neman admission din sa tun wajen sati biyu da ya wuce, be samu gama wa shi yasa yau ya dage ya gama. Baya so ya kara bata wani zangon karatun a banza kamar yadda yayi wannan karon, shiyasa ya yanke shawarar chanja akalar karatun nasa zuwa abinda yake da tabbacin zai taimaka masa matuka wajen hukunta mutane irin Garbati.

Knocking din dayaji a kofa yasa gaban sa ya fadi, kin magana yayi aka cigaba da knocking din, ya zata zata hakura ta tafi, ganin da gaske take yasa ya kashe komai ya mayar waje daya, ya nufi kofar cikin tafiya irin ta masu bacci. Budewa yayi tana tsaye ta harde hannun ta. Kallon da tayi masa ne yasa cikin sa murdawa, takardar hannun ta ta ware ta wurga masa.

“Tun da kaki yarda muyi magana, sai ka duba wannan, kuma dole cikin biyu kayi daya, idan kuma ba haka ba, abinda da biyo baya ba zai maka dadi ba, dan na lura sam baka da hankali baka san ciwon kanka ba.”

“Mummy…” Juyawa tayi ta bar wajen bata ko sake kallon sa ba. Kasa ya tsugunna ya dau takardar hannun sa na rawa, layi cikin layi ya fara bin rubutun, gaban sa yayi wani mummunan faduwa, a take ya juya da mugun gudu ya nufi dakin da take, yana zuwa tana rufe kofar, bugawa ya hau yi yana kiran sunan ta da sauri

“Mummy dan Allah karki fara, dan Allah Mummy, nasan me nake da hankali na wallahi, zanyi ko menene kika ce amma dan Allah karki min haka.”

Babu alamun zata saurare shi, zamewa yayi a wajen ya zauna kansa na juya masa.

Manage ????????©️®️HafsatRano

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                    (9)

***Fitowar ta kenan zata dan taka kafarta ta hange shi a durkushe a kofar dakin sa, da dan saurin ta ta k’arasa

“Babana?”

Dagowa yayi idon sa sun kada sunyi ja ya kalle ta

“Tashi muje daki na.”

Ta fada tana mika masa hannu, mik’ewa yayi cikin sanyi jiki yabi bayan ta, Mummy na jinsu ta tabe baki, babu wanda ya isa ya sata ta sauya ra’ayin ta akan abinda ta haifa, ba zata bari tana kallo a lalata masa rayuwa ba dan shi yafi kowa sauƙin kai.

Suna isa dakin ya zame ya zauna kasan carpet din dakin yana jin zuciyar sa na tafasa.

“Menene matsalar?” Ta saka masa ido, tana kallon yadda kirjin sa ke kaiwa da komowa. Shiru yayi ba tare da yayi magana ba ya mika mata takardar Mummy. Murmushi kawai tayi bayan ta gama karantawa ta mika masa, tasan zata aikata fiye da abinda tace ɗin, dan bata shakka ko kokonton hakan, sai dai babu yadda ta iya, musamman da babu wata alaƙa yanzu dake tsakaninsu da ita sai ta ya’ya, amma tana jan girman ta, bata so kuma wani abu ya shiga tsakanin shi da mahaifiyar sa.

“Kayi mata abin da take so kawai Babana, shine zaman lafiyar kowa.”

“Dadah….?”

“Shine maslaha, abu ne me sauki, kuma tabbas kayi kokari ma ladan ka yana wajen wanda kayi domin sa.”

Matsawa yayi jikin kafarta ya dora kansa a saman, zuciyar sa tayi rauni sosai, ba ya jin zai iya aikata abinda Mummyn tace, ya kuma rasa dalilin sa na son kin amincewa bukatar ta. Shafa kansa ta shiga yi tana ayyana yadda komai yake tafiya.

“Babana…” Ta sake kiran sunan sa

“Kana son Aminatu ko.?” Da sauri ya dago kansa jin tambayar a bazata, abinda yake ta kokawa da zuciyar sa kenan, ya rasa dalilin da yasa yake jin yarinyar har cikin ransa, komai nata yana jin kamar an haɗe shi da rayuwar sa ne, yanzu da Mummy ta kawo zancen rabuwa sai yaji kamar zare wani abu me muhimmanci ne a cikin rayuwar sa. Be san me haka yake nufi ba, sai dai yana daukar ta a matsayin wata babbar ƙaddarar sa.

“Kana son ta ko?” Ta sake maimaitawa

“Nima ban sani ba Dadah, kawai ina jin tausayin ta ne, She’s too young for that, sannan na mata plan na good future,.”

“Shikenan, Ina da shawara, amma dole sai da taimakon mahaifiyar ta, kaga ni yanzu mahaifin ku ya matsa lallai sai na tafi saboda ciwon kafar nan tawa daya matsa min, da babu irin taimakon da ba zan baka ba, toh mahaifiyar ta ita kadai ce zata taimaka mana, wajen ganin mun samu abinda muke so.”

“Ta yaya kenan Dadah?”

“Ka kai ta boarding school, ka damka amanar ta wajen mahaifiyar ta, ka sanar mata da kudurin ka nason ganin ta zama wani abu,nasan babu mahaifiyar da zata ki cigaban yar ta, kai kuma kaga sai ka dawo kayi wa mahaifiyar ka biyayya, kayi karatun ka, ka kara mallakar hankalin kanka, lokacin babu wanda zai fada maka yadda zaka yi da rayuwar ka, a lokacin sai ka dawo, ka cika burin ka.”

Da sauri ya tashi ya rungume Dadah,

“Shisa nake sonki Granny, wallahi you are the best.”

“Ja’iri.” Tace tana kai masa duka

“Allah kuwa, gashi kin kawo solution cikin sauki, idan Daddy yaji labari sai nace masa makaranta na maida ita nima zan koma tawa, kinga ba zai ce komai ba.”

Daga masa kai tayi tana murmushi.

Tashi yayi da karfi da kuzarin sa ba kamar dazun da ya shigo ba.

“Bari naje na sanar wa Mummy na amince da komai data ce, sai na fara shiri.” Ya fada cike da farin ciki.

Fita yayi da sauri, a kofar dakin sukayi kicibis, basarwa tayi kamar bata gama jin komai ba tayi gaba ya bi bayan ta. Zama tai kawai ya shiga tsara mata zance.

“Mom na amince da bukatar ki, amma dan Allah karki yi mata komai, bata da laifin komai bata san komai ba, idan ma hukuncin ne ni zakiyi wa, amma yanzu zan rabu da ita, zan biki mu tafin idan hakan zai saki farin ciki.”

Murmushi ta k’ak’alo wanda ya tsaya a iya saman fuskar ta tace

“Madallah da kai, ka kyautawa kanka, ka kyauta mata, sai ka fara shirin tafiya dan bazan tsaya bata lokaci ba.”

“Kiyi gaba dan Allah, zan biyo bayan ki wallahi nayi Alk’awari, ki bari na dan karasa wani abu dana fara, ba zan dau lokaci ba.”

Dan jim tayi tana tunanin amince wa, kamar tace a’ah sai kuma tayi wani tunani.

“Shikenan ni zan koma gobe, saura kaki abinda nace, kasan dai sauran ba sai na fada ba.”

“In Sha Allah hakan ma ba zata faru ba.”

“Jeka toh zan dan kwanta.”

Fita yayi ya ja mata dakin, ya wuce dakin Aminatu, budewa yayi ya haye saman gadon nata yana lumshe ido, tunanin yadda komai ya fara ya shiga yi, daga san da ya fita daga gidan zuwa yanzu da yake shirin daukar wani babban tsani a rayuwar su. Yadda komai ya zama kamar a film haka ya dinga bin komai daki-daki. Murmushi yayi ya mirgina gefe yana sake duban komai daya zama mamallakin ta a dakin sai yan abubuwan Amal.

“My Destiny.” Ya furta a hankali kamar me rada.

Eh dole ya kira ta da Destiny dan shine kadai sunan da yake ganin ya dace da ita, ƙaddarar sa ce, wadda a yanzu yake jin babu wani abu da zai iya raba shi da wannan ƙaddarar. Haka ya jima a dakin har gabanin magriba kafin ya mike a kasalance ya fada toilet din dake manne a dakin. Alwala yayi ya fito ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar sa.

“A yau shafin rayuwar mu zai fara Aminatu, daga yau ba zan sake barin wani abun ki, ko cutarwa yazo kusa dake ba, nayi alkawarin zame miki babban tsanin cikar farin cikin ki ko da kuwa hakan na nufin… Ko da kuwa hakan yankewar nawa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button