DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Inno mutum ce wadda tasan darajar nema, bata taba zama haka nan, yau ta buga nan gobe ta buga chan, bayan sana’ar saida abinci har kiwon akuyoyi take yi da kaji, ga sana’ar abin kad’i dangin su kuka da su kubewa, da sauran abubuwa, sai ya zama ma a kaf kauyen namu babu wanda zai kama kafa da ita Indai a samu ne, shiyasa kaf gidan mu suke shakkar ta, babu wanda ya isa ya daga mata yatsa balle Baba da Yalwati da suka zama kamar yaranta, sai abinda tace musu ake aiwatar wa.
Kiran da Karime ke kwala min yasa na ajiye kibiyar hannu na na fito, riko ni tayi da sauri tana haki
“Lafiya dai?” Nace ina kallon yanayin ta
“Ina fa, dalla kowa yana chan kallon bak’in gidan Bature sun zo ke kina nan kina tsifa.”
“Dan Allah!” Nace ina fad’ad’a fara’ar fuska ta
“Wallahi ana chan duk ana ta kallon su abin sha’awa, na duba ban ganki ba shine nazo kirankii, kinga motar da suka zo acikin ta, har da wata yarinya kamar girman mu, kinga kayan jikin ta kuwa? Wayyo yan gayu sun ji dadi wallah”
Ta fada tana rik’e haba, da sauri na koma ciki na dauko dankwali na na daura muka fice da gudu, dukkannin mu sirara ne babu kibar arziki, yadda muke gudun kadai zaka tabbatar da yarintar mu, dudu du a lokacin ba bazan bi shekaru goma sha biyu ba, tsiran mu da karime shekara daya ne saboda haka ba zaka gane wani banbanci me yawa a tsakanin mu ba.
Tun kan mu karasa muka ga ana juyowa, hanne ce ta tsaida mu tana dariya
“Ina zaku wai, kallo ya barku ai sun koma gida, sai wani jikon kuma.”
Haushi ne ya kamani, duk zuwan da zasuyi ban taba samu na gansu ba har su tafi, a take na kudurce a raina wannan karon babu abin da zai hanani ganin su, ko nima na samu na dorar da labarin su.
Kullum da safe idan na tashi ta kofar gidan nake bi, haka ma idan na dawo, ban taba samun nasarar ganin ko da cikin gidan bane. Gida ne me girman gaske, hade da babban gidan gona da tsayawa fasalta yanayin girman sa ba mai yiwu wa bane. Duk da karancin shekaru a lokacin da kuma yanayi na duhun kai da kauyanci na gane cewa ba karamin masu kudi bane mamallaka wannan wajen, duk a irin wannan lokacin suka zo gaba d’ayan su su jima sosai, idan suka tafi kuma shikenan sai wani lokacin me tsawo.
Gidan Bature kamar yadda mukayi wa gidan da lakabi, sai dai a zahiri ba haka sunan me gidan yake ba, tsari da yanayin gidan da bamu taba ganin kamar sa ba yasa muke kiran gidan da gidan Bature.
Tun gabanin magriba garin yake ta hadewa, alamun za’a iya samun ruwa a kowanne lokaci, muna daga kofar dakin mu dasu hanne muna hira da karad’i Inno ta kwala min kira, tashi nayi na karasa wajen ta ina kallon hannun ta
“Yi maza kije shagon Umaru ki siyo min maganin sauro yanayin garin za’a iya ruwa kowanne lokacin.”
Karba nayi na juya da niyyar kiran me rakani, dakatar da ni tayi ta hanyar cewa
“Ina kuma zaki koma?”
“Su karime zan kira su rakani Inna.”
“Saboda ku tsaya min shiririta a hanya ko? Kin wuce da sauri ko sai na bugo ki?”
Da sauri na juya nayi hanyar waje zuciya ta duk babu dadi, duk yawanmu na rasa dalilin da yasa ni kadai Inno take takurawa.
Sanda na isa shagon ya riga ya rufe, juyawa nayi ina tunanin yadda zanyi, sama na sake kalla naga yadda hadarin ke sake hadewa nayi saurin daga kafata na kara sauri don zuwa shagon dake chan kasa kadan.
Sauri sauri nake nabi ta wani lungu ina kokarin ganin na isa kafin ruwan ya sakko, cikin sa’a na samu shagon yana bude shima yana kokarin rufewa, da sauri na bashi kudin na karbi maganin sauran na juya na kamo hanyar gida a lokacin garin ya kara hadewa.
Gidan Bature
Dukkanin su suna zaune a babban falon gidan, kallo suke suna hira gwanin sha’awa, sun kusa a ƙalla su goma maza da mata, Ja’afar ne ya kalli Farouk da tun da aka fara hirar yana rike da waya be tanka musu ba, magana suke akan fitar da zasuyi gobe dan zaga gari.
“Ya Farouk.” Ya kira sunan shi yana kallon sa
“Uhum?” Ya amsa yana yin kasa da wayar dake hannun sa
“Maganar fita gobe, U haven’t said anything bayan kuma kai kadai ne zakayi convincing Dada ta yadda.”
Be tanka ba ya sake maida kansa kan wayar kamar ba zai ce komai ba, ganin haka yasa Ja’afar zungurar Amal ya nuna mata bangaren Farouk din, duk ciki tasu tafi zuwa d’aya, babu wani abu da zata nema beyi mata ba sai dai idan bashi dashi din.
Tashi tayi tsam ta isa gefen sa ta zauna ta marairaice murya
“Dan Allah Yah.” Hade hannayenta tayi waje d’aya tana sake kallon sa, hararar Ja’afar yayi kafin ya mike yana ware hannayen sa, duk sun maida hankalin su kansa suna jiran su ji me zai ce, takawa yayi a nutse har gaban window dake makale a falon ya zuge curtains din, sama ya kalla yaga yadda garin yayi, murmushi yayi ya tura hannun sa gaba daya waje yana kama sanyayyiyar iska dake kadawa a hankali. Wajen mintinan biyu yayi a haka kafin ya zaro hannayen nasa ya juyo ciki yana kallon su.
“Zan yi magana da Dada, shikenan?”
Ihu suka sa gaba daya cikin murna, yana jin su ya juya da sauri ya fada dakin su, ƙatuwar rigar ruwa ya dauka ya saka hade da takalmin sa na ruwa ya fito ya fice daga gidan gaba daya.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????
2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863
GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????
09032345899
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
DG
Shafi na biyu (2)
Lokaci daya iska me karfin gaske ta taso, gaba daya bana ganin gaba na, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ni, na sani sarai idan har na bari ruwan nan ya taba lafiyar jiki na kashi na ya bushe, ganin da gaske bana ko ganin hanya yasa na makale gefen wani shago na kudundune kaina ina jin matukar tsoro. Ina nan makale yayyafi ya fara sauka a hankali, tsoro na ya dadu, zuciya ta tayi rauni sosai, kamar daga sama naji an dafa kafada ta, cikin tashin hankali na dago kaina,ban samu nasarar ganin fuskar kowaye ba, saboda tsananin hasken torch light din da aka sa aka haske ni. Cikin muryar tsoro na furta
“Waye!”
Be amsa ba, ba shi kuma da niyyar amsawar, illa sake dalle ni da yayi, take hasken yayi tasiri rage kaso tamanin cikin dari na gani na, baya da ƙurar da ta riga ta cika min idon nawa, da sauri na mike ina kokarin daidai ta zaman riga ta, na fara alamun barin wajen, hannu naji an saka an riko ni, cikin wata iriyar murya mara fasali ya furta
“Gidan uban wa zaki? Ai wallahi kinyi kadan tsuntsu daga sama gashashshe.”
Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskata jin muryar Garbati, mutumin da ko a mafarki bana fatan hada hanya dashi, waye be san shi ba kaf kauyen nan namu, tantirin dan iska ne, lamba daya, gashi babu wanda ya isa dashi kaf kauyen. Da sauri na ja da baya ina kokarin sake shiga cikin ruwan sosai, damko ni ya sake yi nayi kara da karfi jin zafin rikon da yayi min, ja na ya shiga yi yana kokarin turani cikin shagon da tun zuwa na wajen na lura da yar kofar dake bude, amma banyi tunanin akwai mutum ciki ba, da karfin gaske na hau kokarin kwatar kaina, sai dai ko kusa da hakan ban kai ba , duba da yanayin karfin ba daya ba. Tuni na hau kuka ina magiyar bashi hakuri, tunda ayi ƙarancin shekaru na nasan hakan da yake me yake shirin aikata min. Be saurara ba, ko ma nuna alamun yaji abinda nace, haka ya tura ni ta karfi ya maida kofar ya tura yana sakin wani shu’umin murmushi.