DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Aminatu, zo matso kinji’

Jan jiki nayi na matsa gaban ta, cikin rashin sanin yadda zata dauke abin nace

“Dadah zan dau kayana ne, da abubuwan makaranta.”

“Ba zaki bini ba kenan?” Tayi tambayar tana bata rai

Zanyi magana Daddy ya katse ni

“Kiyi hakuri Dadah, tabbas tana da babban uzurin ta na kin amincewa ɗin, Aminatu, kiyi hakuri kinji, kowacce rayuwa cike take da kalubale, idan kayi hakuri sai kaga kaci riba, tabbas nasan ba’a kyauta miki ba, amma bani da yadda zanyi, kiyi hakuri kinji.”

Ban iya magana ba sai daga kai kawai da nake kamar kadangaruwa, nasiha ya shiga yi min sosai, sannan ya bani tabbacin duk yadda zaiyi zai nemi Farouk, yaji komai sannan magana ciki sun karba, sun tabbata bazan taba yin wani abu da zai bata sunana ba. Ɗorawa tayi

“Zanyi kokarin ganin na kula da komai naki har zuwa lokacin da zaki sauka lafiya, mun riga munyi maganar jiya. Yanzu ki cire duk wata damuwa a ranki, ki fawwala Allah komai.”

“In Sha Allah, Nagode Allah ya kara girma.”

Wayar sa ce tayi kara, ya mike ya bar falon, hawaye naji ya zubo min, nayi saurin maida su ina bawa kaina k’warin guiwar bazan yi kuka ba, musanman a gaban Dadah. Bata ce min kala ba, sai kawai ta maida hankalin ta wajen Yalwati tana mata yan tambayoyi. Mik’ewa nayi tsam, suka bini da ido,a hankali na nufin dakin, cikin tarardadin abinda zan tarar ɗin. Turawa nayi, kamshin turaren sa ya daki kofofin hanci na, babu abu daya na dakin daya chanja, yananan tun ranar da muka bar shi, ba tare da sanin cewa na barshi har abadah ba. Kaina ne ya hau juyawa, nayi saurin dafe wa, na shiga har haɗa duk abubuwan dana san nawa ne, cikin dan kankanin lokaci na hada komai waje daya. Kallon wardrobe d’insa nayi, zuciya ta ta kasa hakuri, hannu nasa na bud’e, babban album din sa ya fado, tsugunawa nayi na dauka a hankali na shiga budewa, daya bayan daya nake bin hotunan da kallo, kwalla na taruwa a ido na. Jin takun tafiya yasa nayi saurin tashi, na ciri guda daya na tura cikin jakata na maida sauran tare da rufe wardrobe din. Juyowa nayi da nufin tafiya muka hada ido, tana tsaye ta zuba min ido tana murmushi, murmushi me dauke da ma’anoni da yawa Dauke kaina nayi na tattare kayana zan bar dakin, ta gefen ta nazo wucewa a hankali nace

“Ina kwana?”

Bata amsa ba, dama nasan ba zata amsa din ba, sai dai har lokacin idon ta na kaina, kallon da na rasa na menene, rab’ewa nayi na wuce kawai ba tare da na sake cewa komai ba. Ina zuwa falon na tarar da Dadah, tana zaune tana juya wayar hannun ta, kasa na tsuguna cikin dakiya nace

“Na gama zan tafi Dadah.” Girgiza kai naga tayi, ta miko min har karamar jakar hannu. Ajiye kayan hannu na nayi na karba ina kallon ta

“Karbi ki ajiye wajen ki, in Sha Allah zan dinga zuwa ina duba ki lokaci zuwa lokaci, ki kula da kanki kinji? Allah yana tare dake.”

“Nagode sosai Dadah, bansan da wanne bakin zan gode miki ba, Ubangiji ya sake miki da mafificin Alkhairi.”

Da sauri ta tashi, ta shige dakin ta ba tare da tace komai ba, jiki na a matukar sanyaye na mike, ina karewa ko ina kallo, Yalwati ta tayani daukar kayan, muka fito. Da sauri ya tare mu, ya karbi kayan hannu na har lokacin idanun sa na kaina.

“Daddy yace na mika ku saboda mutane.”

Ba musu muka bi bayan sa, ya saka kayan a booth muka tafi. Har kofar gida ya kaimu, sannan ya tayamu sauke kayan yara suka dauka muka shige ciki.

Daki na wuce kai tsaye, na ajiye kayan na jawo jakar Dadah na bude, waya ce yar karama, sai kudi masu yawa, murmushi nayi na ciri wayar na ajiye jakar ina kokarin kunna wayar.
Numbobi biyu na gani akai, daya an saka my number, sai dayar dake rubuce da babban baki, BABANA zuba wa number ido nayi ina kallo, babu shakka number Ya Farouk ce, shiru nayi ina tunanin abinda zanyi da ita da Dadah tayi min saving dinta akai, sai dai bani da amsar hakan. Ajiye wa nayi kawai na shiga wata sabgar ina kokarin ganin na manta da damuwa ta.
   Kwana uku da tafiyar su Dadah sai ga kiran ta, da murna na daga muka gaisa ta tambayi ni idan akwai matsala, hira muka danyi sannan ta kashe bayan ta kara jaddada min kalmar nan ta hakuri ta na riga na gama haddace ta. Tun daga lokacin muke waya sosai, wani lokacin naga shiru nakan kirata muyi hira sosai. Wata rana muna waya take min maganar Jamb, tabbas nima dama ina son yi ɗin,sai dai idan na duba yanayin da nake ciki sai nace na jira wata shekarar, ko dana fada mata uzuri na bata amince ba, a wannan shekarar take so nayi, babu inda raino ko ciki ke hana karatu. Dole na amince na shiga tunanin yadda komai zai kasance.
  


Bayan wata biyu

Ba tare da dogon nazari ba, tabbas yan watannin nan a cikin waha’a nayi su, wahalar rainon karamin ciki zuwa kokarin mantawa da dukkan rayuwa ta ta baya, bani da matsala da Inno, dan babu abun da yake hada ni da ita, iya kar kokari na ina yi ganin na kyautata mata, ita dinma a bangaren ta hakan ne, duk abinda tasan zan nema tana kokarin bani shi.  Ranar muna zaune muna hira da Yalwati, wadda yanzu ta zama abokiysr hira ta tun bayan tafiyar Karime, dan Inno ba kasafai take doguwar hira dani ba, kasuwancin ta da ya kusa durk’ushewa ta jajirce ganin ta farfaɗo dashi, dan hakan ya zama ma kowanne lokacin ta me tsada ne a wajen ta.
   Nura ne ya shigo, kansa dauke da hular gini, ya zauna daga gefen tabarmar da nake zaune yana jingina da bango cikin matukar gajiya. Cikin tausaya wa nace masa “Sannu.” ruwan dake gefe cikin kofi na mika nasa, karba yayi yasha ya ajiye sannan ya ciro takarda daga aljihun sa

“Gashi Aminatu, dukkan bayanin yana ciki tace, ki shirya gobe sai na rakaki ki cike dan tace befi sauran kwana uku a rufe ba, Allah ne ma yasa aka danyi jinkiri wannan karon da sai dai wata shekarar.”

Da farin ciki na karba na duba, sannan nace

“Kai amma naji dadi, nagode sosai Yaya Nura, Allah ya kaimu goben .”

“Amin.” Yace yana mik’ewa.
“Bari na watsa ruwa a gajiye nake.”

“Gaskiya dai, ai da gajiya.”

Gyara zama nayi ina juya takardar principal din tamu cike da farin ciki.
Ina shirin kwanciya Inno ta shigo, tsayawa tayi a kaina tace

“Naji kuna waya ina tace miki ki saka?”

Na gane Dadah take nufi, kai tsaye nace mata

“Cewa tayi wai nasa Kano.”

Shiru tayi, sai chan kuma tace

“Shikenan Allah taimaka.” Daga haka ta fice tana jawo min kofar, ni kuma na gyara na kwanta ina fatan wayewar gari saboda tsananin farin cikin da nake ciki.
Washegari da sassafe na shirya muka dau hanyar zuwa cikin gari dan cike jamb. Bamu sha wuya ba muka gama muka dawo. Ranar jarabawar tazo naje na zana cike da addu’ar samun abinda naje nema. Haka muka dawo gida zaman jiran tsammani. Kwana uku kuwa tsakani sakamakon ya fito, sosai hankali na ya tashi, haka dai na daure nasa aka dubo min. Ban taba zaton zanci haka ba, hamdala nayi ta wa Ubangiji dan nasan ba iyawa ta bace. Dana kira Dadah ma na faɗa mata sai ta hau murna, saura jiran post Utme kuma.
A hankali cika na yana girma, ina kara tunanin yadda zata kasance min idan na haifi abinda yake ciki na, duk da yanzu bana shan wuya sosai sai dan abinda ba’a rasa ba.
  Ranar dana gaji da zaman nayi gidan Karime, chan na wuni sai wajen magriba na dawo gida, washegari kuma nayi gidan Hanne. Sosai suke bani sha’awa, yadda suke zaune a dakin su, da dadi babu dadi, suna tare da mazajen su, hakan ba karamin sani tunawa da Ya Farouk yake ba. Haka dai nake bawa kaina k’warin guiwar komai zai wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button