DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Idan kai kana shaye-shaye toh ni garau nake, kuma da hankali na idan kai mahaukaci ne, idan baka gane maganar fatar baki ba, ai zaka gane rubutu ko?”

Da sauri ya dauki takardar ya hau budewa, bakin sa na karanto duk addu’ar da tazo masa, takardar shaidar cikin dake dauke jikin ta ya fara budewa, a take wani matsanancin farin ciki ya lullubeshi, wanda ba zai iya kwatanta shi ba, da k’warin guiwar sa ya bude dayar yana cike da yakinin abinda yace karo dashi a ta farkon na da alaƙa da ta biyu, a wani irin yanayi ya dago hade da mik’ewa tsaye.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ya furta da karfi yana nuna wa Daddy hannu ba tare da ya iya furta kalma daya ba

“Sannan bayan ka cimin mutunci ta hanyar sakin ta, ka kuma ƙaryata cikin dake jikin ta, shine har kake da gut din takowa inda nake, bansan kuma me kake so ka sanar dani ba.”

Da sauri ya dire akan ƙafarsa, yace

“Ban aikata ba, ban aikata daya daga cikin abinda ake tuhuma ta dashi ba a karo na biyu wallahi ban aikata ba, bani da masaniyar komai..”

“Rubutun jiki fa? Ko shima zaka ce min ba naka bane?”

Ya watso masa tambayar yana masa kallon banza, sake kalla yayi da kyau, tabbas rubutun sa ne, me hakan ke nufi? Kira ne ya shigo wayar Daddyn, ya daga yana amsawa kafin yayi hanyar waje kawai ba tare da ya kalli jerin abinci da aka ajiye masa.
  Kamar mahaukacin zaki haka ya fito daga shashen, da sassarfa ya isa bangaren su yana kwala wa Ja’afar kira. A zaune ya tarar dashi yana karin kumallo cikin kwanciyar hankali. Watsa masa takardun yayi a hargitse yace

“Kayi min bayanin me ya faru, bayan tafiya ta, ina amanar dana bar maka?”

“Ya Farouk calm down, nayi maka bayani.”

“Wanne irin calm down, kasan me kake fada kuwa?” Ya fada a hargitse

“Owk, bayan tafiyar ka, ranar da ka fada min zasu gama exams, muka dau hanya, mun yi nisa sosai har mun wuce Kano ma amma da kadan, motar mu ta samu matsala, abinda yayi delay dinmu kenan gashi yamma tayi and wajen da muke babu abin hawa balle me gyara, da kyar muka sami wani bawan Allah ya juyo damu Kano, muka bar motar a can, washegari Daddy yazo da maganar sakin, bansan me ya faru ba naji dai suna magana da Dadah, the following day muka tafi Shagari tare da Dadah.”

Dafe kansa yayi cikin tsananin tashin hankali yace

“Ja’afar, Saki ni? Na sake ta? When, how? Mesa bana tuna komai? Ka yarda zan sake ta kaima kamar Daddy?”

Girgiza masa kai yayi

“Ban yarda ba Ya Farouk, sai dai rubutun da ya zama naka, shi yafi bani mamaki, ya akayi hakan ta faru?”

“Someone is behind this, WallAhi sharri aka kulla min, wani ke son ganin bayana.”

“Amma Ya Farouk…”

Ƙarar shigowar messages wayar yasa yayi saurin kallon ta, ta saman notification bar ya ga alamun video aka turo masa ta whatspp, whatspp ɗin ma da ya manta rabon sa dashi, hankalin sa ne ya tafi zuwa son ganin abinda video din ya kunsa, a gaggauce ya danna load, ya zuba wa wayar ido yana jin kamar zuciyar shi zata fashe, cikin kankanin lokaci ya gama loading, videon ya bude. Shine zaune, gaban sa ɗan karamin centre table din dake falon su, rike da papper da biro, rubutun ya kura wa ido, take abinda ke rubuce a takardar hannun sa ya bayyana a faifan video ɗin, shine zaune yana rubuta wa Aminatun sa saki, cikin kwanciyar hankali, jefar da wayar yayi saman kujera yana sakin numfashi da karfi.

“It’s a trap Ja’afar, na shiga uku.”

Da sauri Ja’afar ya isa wajen wayar ya dauka yana kallo, rubutun tar hade da fuskar Farouk din sanda yake yinshi a cikin falon nan nasu, girgiza kai yayi yana shirin ajiye wayar sakon audio ya shigo, kunna wa yayi muryar Farouk din ta karade ko ina a lokacin da aka kira shi. Sanda yake ƙaryata maganar cikin, zabura yayi ya fisge wayar yana sake saurara, tabbas shine yake magana, amma yaushe hakan ta faru? Ya kasa tuna daya daga cikin ranakun da hakan ta faru. Da sauri ya fada dakin su, ya hau birkice komai na dakin, babu komai sai tarin kayayyakin su da takardun su na makaranta, a hargitse ya sake fitowa, rike da mukullin motar sa dake hannun Ja’afar tun tafiyar sa, da sauri ya tare shi ganin kamar ba a hayyacin sa yake ba

“Barni Ja’afar, Kano zan tafi, daga can na dau Dadah mu tafi wajen ta, ba zan iya zama ba, idan har lissafin cikin jikinta da date ɗin da akayi daidai ne, toh tabbas ta haihu, ko kuma tana kusa da haihuwa, ya kake tunanin zata iya daukar wannan tension din da ciki.”

“Let me come with you, ba zaka iya driving ba.”

Mika masa car key din yayi ya fada saman kujerar idanun sa sun kada sosai, burin sa daya ya isa gareta, yayi mata bayanin komai. Cikin kankanin lokaci Ja’afar din ya fito bayan ya chanja kaya, suka dauki hanyar Kano.


Dadah na zaune hannun ta rike da waya tana sake gwada kiran, karo na biyar kenan tana kira ba’a dagawa, gashi sam hankalin ta yake kwanciyar.  kanwarta Fatsim tayi wadda suke kira da Umma Fatsim, tace

“Yaya wai kiran ne har yanzu?”

“Kinga har yanzu ba’a daga ba, gashi sam hankali na yaki kwanciya wallahi, Allah yasa lafiya.”

“Toh amin, amma nake ga ai idan ba lafiya ba zasu kiraki su sanar miki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai Alkhairi.”

“Allah yasa, anjima sai na k’ara gwadawa.”

Hira suka cigaba da yi sama-sama, har zuwa lokacin da aka bude gate din gidan, ta window ta zuge labulen ta leka,

“Ja’afar ne.”

Tace tana sakin labulen, da sallama suka shigo, kallo daya zakayi wa Farouk kasan baya hayyacin sa, shine a gaba Ja’afar na take masa baya.

“Babana!”

Da sauri ya karasa gabanta, kamar karamin yaron dake gaban mahaifiyar sa, haka ya dora kansa a saman kafarta yana jujjuya kan kamar wanda ke shirin zaucewa

“Me yake faruwa Ja’afar?”

“Kamar yadda kike tunani ne Dadah.”

“Bani nayi ba wallahi Dadah, bani ne ba, sharri aka kulla min, I’m trapped bansan ya zanyi ba.”

Dago kanshi tayi

“Mik’e Babana, nasan dama ba zaka taba aikata ba.”

“Nasan dama ba zaki yadda ba, ke kadai ce kika yadda dani, amma ni kaina yanzu Dadah ban yarda da kaina ba, na kasa tabbatar wa kaina bani ne na rubuta ba, rubutu na ne, magana tace Dadah, waye zai min wannan? Ko dai ni na aikata ban sani ba? Amma ta yaya? How comes bana iya tuna komai ne?”

“Ba zaka taba aikata abinda zai zama cuta ga Aminatu ba.”

Ciro wayar sa yayi, ya mika mata videon yana girgiza kansa

“Nine a videon nan, da hannu na na rubuta sakin Dadah, da hannu na na rubuta, bansan sanda na fara shaye-shaye ba, amma tabbas bana hayyacina sanda na aikata hakan, tabbas yaudara ta akayi, aka sani na rubuta ba tare da na sani ba, sai dai na kasa tuna komai, bana tuna komai Dadah, kaina kamar zai fashe nakeji, zuciya ta namun zafi, idan har akwai mutumin da yake son ganin bayana a duniyar nan, toh tabbas Aminatu tana cikin matsala, zanje na ganta, zan bata hakuri, nasan zata amince dani ko kowa be yarda ba.”

“Kaje ka ganta, tana bukatar ka fiye da kowanne lokaci, abinda ke cikin ta na bukatar ka.”

Mik’ewa yayi cike da karfin sa, ya juya ya bar falon Ja’afar na take masa baya. Shiru ne ya biyo bayan fitar su, zuciyar Dadah cike da farin cikin dawowar Farouk a lokacin data tabbatar Aminatu na bukatar sa.

★★★★
Tafiya ce mara daɗi musamman gareni, duba da rashin sabo da kuma danyan jegon da nake ciki, kuka yar jaririyar da bansan takamaimai sunan ta ba, ta saka tana wutsul-wutsul da kafarta, dauke kaina nayi daga ɓangaren Hajiyar, ina kallo ta hau jijjigen ta, sai dai bata da alamun yin shiru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button