DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Iman ta tashi, kinga bakinta Hajiya?”
Yace yana mika mata ita, dariya suka saka baki daya kafin ta miko min ita tana faɗin, maza karbe ki sake gwada mata mu gani.” Da sauri na sauke kaina kasa saboda kunyar data kamani, juyawa yayi da sauri ya bar dakin, sai a sannan Hajiya ya ankara, dariya kawai tayi ta cigaba da gwada min yadda zanyi, cikin sa’a kuwa aka samu sai dai babu yawa ga wani irin zafi, yarfe hannu na nake kawai ina cije baki Hajiya namun dariya.
Bayan ta koma bacci na kwantar da ita ina kwanciya a gefen ta, bacci ne ya dauke ni ba tare da na shirya ba.
Na jima sosai ina baccin har sai da mai dakin ta dawo, motsin tane ya data ni, muna hada ido ta sakar min murmushi, murmushi nayi mata kamin na mike ina gyara zama na.
“Sannu da tashi.”
“Yawwa.” Nace ina yar hamma,
Altine ce ta shigo dauke da Kaskon wuta, ta ajiye ta koma ta kawo kayan wanka, komai sabo hatta bawon wankan da dangin su sabulu, daukar ta tayi, tayi mata wanka hade da gashin cibiya, kafin ta gama dakin ya dau dumi, turaren wuta Ramlah tasa mana ta zauna tana cin abinci tana yi min hira.
★★★
Harira na zaune rike da d’an karamin mudubi tana duba fuskarta, shirya take tsaf daga gani fita zatayi, ajiye komai tayi a gefe ta yafa sabon mayafin ta, tana yan wak’e wakenta cikin farin ciki ta fito, turus tayi ganin yan sanda a tsakiyar gidan nasu, kowa ganin abinda ya kawo su, bata kawo komai akanta ba tayi wajen su, cikin son nuna ita din wayayyace tace
“Lafiya dai?”
Maganar da tayi yasa Farouk juyowa, da sauri yace
“Arrest her.”
Babu wani bata lokaci suka damke ta, tana ihu tana komai suka tusa ta cikin bayan motar, sai a sannan ta lura da Inno kanta a sunkuye ta rufe fuskar ta da mayafin kanta. Wani irin amsawa kirjin Harira yayi, cikin tsananin tashin hankali tace
“Innaro?”
“Ko ba ita bace?” Ta maimaita jin ta mata banza, bata amsa mata ba, har suka isa charge office, fito dasu akayi aka watsa su cikin wani ɗan karamin cell kafin ya tura Garbati a cikin nasa shi kadai.
“Zan dawo, kar kuma ku bawa uban kowa belin su har sai sun bqyyana inda suka kai min matata da jariri na.
Da sauri suka amsa ya juya ya bar wajen, Ja’afar na bin sa haka suka koma gida, be kula takan maganar da Ja’afar din yake ta masa ba ya fada daki da sauri ya saka key, misscals ɗin Dadah ya tarar, sai yaji zuciyar sa ta karye, yasan yadda ta damu da Aminatu idan taji labarin nan hankalin ta ba karamin tashi zai ba, fasa kiran ta yayi ya ma kashe wayar baki daya yana bin dakin nasu da kallo, dakin da sukayi rayuwa a ciki, rayuwar da yake ganin ta cikin wasu muhimman lokutan da yayi masa matukar muhimmanci a rayuwar sa. Ji yayi zuciyar ta ta bushe, ta k’ek’ashe, ba zai taba kyale duk wanda yake da hannu ba, ko da kuwa mutanen dake da kusanci mafi rinjaye dashi. So yake yayi kuka da idanun sa, ko yaji dadi a zuciyar sa, sai dai yasan abu ne me matukar wuya a yanzu, lallai zubar da hawaye idan kana cikin damuwa ma Rahma ne.
Sai yamma likis ya tashi daga inda yake, istigfari yayi hade da dauro alwala ya gabatar da sallar azahar da la’asar. Jawo wayar sa yayi ya kuna, ya danna kiran wayar Dadah don yasan tabbas tana cikin son jin abinda yake faruwa. Bugu daya ta daga, da sauri tace
“Babana me yake faruwa? Kun barni cikin tashin hankali.”
Share zufar kanshi yayi, murya a ciki-ciki ya soma mata magana, salati kawai take har ya kai karshe, zuwa lokacin gaba daya komai ya fara tsaya mai, yunwa, tashin hankali da wani abu daya tokare masa makoshi ne suke barazanar kaishi kasa, kiran sunan shi take sai dai baya jin komai sai chan a saman kanss, ya gaza amsawa, a hankali idanun sa ke rufewa, kadan-kadan kafin su rufe baki daya yana sakin wayar wadda karar faduwar ta, ta saka Ja’afar tasowa da gudu ya hau dukan kofar. Jin shiru yasa shi firgicewa yayi dakin Dadah da gudu ya nemo spare keys, a gaggauce yazo ya bude shi, da sauri ya k’arasa wajen sa yana jijjigashi, ganin da gaske baya hayyacin sa yayi saurin dauko ruwa ya shafa masa a fuska, ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana bude idon sa da suka rine sosai, taimaka masa yayi ya dora shi saman gadon kafin ya fita don dauko wayar sa. Daddy ya fara kira no answer, sai ya kira Mummy ita din ma babu amsa, shiru yayi yana tunanin wanda zai kira kuma, daga karshe ya yanke shawarar kiran Dadah, a rikice ta daga kiran nasa dan dama suna magana da Farouk din ne taji shiru.
Dakin Ja’afar ya komo bayan sun gama wayar, har lokacin idanun sa na bude ya kura wa saman dakin ido.
“Ya Farouk!” Ya kira sunan shi,
“Dadah tace karka sa damuwa a ranka, da cewa tayi ma xatazo nace a’ah zamu taho ma gobe.”
“Waye aka ce ya kawo takardar nan?” Ya jeho masa tambaya still idanun sa na kallon sama
“Wacce kenan?”
“Takardar dake rubuce da sakin, waye ya kaiwa Aminatu?”
“Ban sani ba gaskiya, a yadda naji,makaranta aka je aka kai mata.”
Shiru yayi cikin dogon nazari kafin yace
“Shikenan, koma waye zan gano ai.”
“Kabi komai a sannu Please.”
“Karka damu, zaka iya wucewa kawai, zan dan zauna anan ko na sati daya ne.”
“Babu matsala idan na Barka? Baka jin dadi naga.”
Girgiza masa kai yayi kafin yace
“Idan ka fita ka jamin kofar Please ina son zama ni kadai.”
Juyawa dayan barin yana sake gyara kwanciyar sa, dan jim Ja’afar din yayi kafin ya ja masa kofar kamar yadda ya bukata
Dare ya tsala sosai, yayi zurfi a cikin tunanin sa,duk kokarin sa nason ganin ya samu ko da wani haske ne a binciken sa abun ya faskara, juyi kawai yake yana tuna halin da Aminatun ke ciki.
Da safe ya shirya sukayi sallama da Ja’afar ya tafi, duk da baya jin dadin jikin sa da zuciyar sa, amma haka ya danne ya nufi station din don yana son magana da Inno. Fito da ita akayi yayi mata yan tambayoyin da suka shige masa duhu, game da wanda ya kawo takardar sakin. Yadda ta sanar masa yasa kansa ya k’ara daurewa, wacece wannan da zatayi masa haka? Menene tsakaninsu? Mutun daya ya ke tunanin zata aikata hakan, Mummy, sai dai ya kara shiga matukar damuwa daya nuna mata hoton Mummyn amma tace ba ita bace.
Gidan Maigari ya nufa, sai dai shima bayanin d’aya ne mata ne su biyu suka zo wajen sa, sai dai shi be nuna masa hoton na Mummy ba ya daiyi godiya kawai ya tafi.
Duk inda yake tunanin zai kai ga neman ta, yayi, ya sare sosai yana jin kamar rayuwar sa zata k’are. Gidajen Radio da talabijin duk ya kai musu cikiya hade da hoton ta, dan baya taba tunanin zatayi nisa da Katsina, duk binciken nasa a iyakar nan din ne.
Tsawon sati guda kenan yana bincike akai hade da neman ta, duk inda yake tunanin zai same ta har gidan principal yaje, gaba daya ya rame ya lalace kamar bashi ba.
Yana zaune kiran Daddy ya riske shi, a kasalance ya daga yana karawa a kunnen sa gami da sallama
“Farouk, me kaje ka aikata a gidan su yarinyar nan, maigari ya kirani akan kaje har gida kasa an kama mahaifiyar yarinya tsawon sati daya kenan, wai kai yaushe zakayi hankali ne ehe?”
“Daddy ba abinda kake tunani bane…”
“Kai kullum abinda zaka sani magana shi kake yi, ya kamat kasan kai ba yaro bane yanzu.”
“Ba haka bane… Ayi hakuri dan Allah.”