DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Awa uku na baka, kaje ka fitar dasu sannan ka baro garin, kayi abu ya dame ka shine zaka je ka huce akan bayin Allah, Awa uku ka bar garin nan ka dai ji na fada ma.”
Bin wayar yayi da ido, ya rasa me yasa har yanzu Daddyn ya gaza aminta dashi balle ya fahimce shi, har yanzu bashi da ikon kansa. Ba ya taba barin sa ya kare kansa, komai yayi bai iya ba, komai yayi sai fada. Mutum daya ke tsayawa ta saurare shi tun yana yaro har zuwa yau, mahaifiyar sa da ita da babu banbancin su kadan ne, bata san komai ba sai kasuwanci ta, bata da lokacin su tun ma kafin rabuwar su da Daddy balle yanzu da take ganin sun girma.
A gurguje ya shiga hada kayan sa, yana yi yana ayyana hukuncin da zai yanke wa kansa, hakan ne kawai mafita a garesa, baya jin zai iya sake zaman wasu awowin a cikin garin. Duk abinda yasan zai bukata ya tattare su, waya kawai ya daga ya kira sifetan yan sandan wajen yace ya sake su, loda koman sa yayi ya rurrufe ko ina ya damka wa Baba maigadi yan mukullayen gidan ya dauki hanyar Kano.
Shigar dare yayi, Dadah na cin tuwo ya turo kofar ya shigo yana jan kafar sa, da kallo ta bishi cike da tausaya wa, har ya zauna gefen ta yana tankwashe kafarsa
“Babu wani labari ko?”
Tace tana tsame hannun ta, girgiza mata kai yayi bakin sa ya gaza furta kalma daya, tashi tayi ta wanko hannun ta tazo ta zauna gefen sa, da sauri ya dora kansa a saman ƙafar ta. Tun yana yaro haka yake mata, idan baya jin dadi ko kuma ransa ya ɓaci, fasa tambayar sa komai tayi. Sai daya gaji dan kansa sannan ya mike ya nufi daki, bata hana shi ba, tasan lallai yana bukatar kadaici, addu’a ta bishi da ita kawai tana fatan komai ya warware cikin sauki.
Ko da ta tashi da safe tuni ya fita, sai gabannin azhar sannan ya dawo gidan, kwana uku yana jeran fita a rana ta hudu yace mata zai je Lagos, bai sanar da ita abinda zai je yayi ba, haka ya tattara ya tafi, a ranar ne ita kuma ta dauki hanyar Shagari don samun magana da Inno.
Satin sa biyu a Lagos ya dawo ya wuce Kaduna gidan Mummyn su, duk ya sake ramewa kamar ba Farouk ba, ita kanta data ganshi sai data ji babu dadi, ta shiga tambayar shi abinda ya same shi. Wanka yayi ya shirya kafin ya same ta a zaune a falon ta na alfarma. Tana zaune kafarta saman tuntu tana hutawa.
Maimakon ya zauna a kujerar data ke nuna masa sai ya zauna a k’asa, cikin yanayin da ta kasa ganewa ya soma mata magana
“Kiyi wa girman Allah Mummy, ki sanar dani gaskiya, ba zargin ki nake ba, sai dai zuciya ta, ta kasa nutsuwa, ina son sanin da hannun ki a duk wani abu daya danganci Aminatu? Dan Allah ki taimaka ki fadan gaskiya, kaina ya kule, na rasa waye zai aikata min hakan? Iya sani na ban sake ta ba, amma me yasa na kasa wanke kaina daga daurin da akayi min?”
Murmushi tayi kafin tace
“Farouk kenan, bani da masaniyar komai, haka zalika ban aikata abinda kake tunani ba, mesa zan boye kaina idan har ni ce na raba ku? Karka manta ni mahaifiyar ka ce, tsarin rayuwa ba zai sa na manta matsayi na ba, idan har ina son na raba ku, kai tsaye zan sa ka sake ta, bisa karfin iko na da matsayi na wajen ka.”
“Kiyi hakuri, ba ina zargin ki bane, kiyi hakuri dan ALLAH.”
“Karka damu, bani da masaniya akan ba kaine ka sake ta ba, bayan na samu labarin a wajen Ja’afar, ban yi niyyar zuwa ba, sai dai text message dana samu ne yasa ni zuwa dole, tun da sakon na nuna cewa ka saki yarinyar sannan Daddyn ku yaje domin ya maida auren, bayan kuma kace kai bakaa so, hakan yasa na tafi, a ganina hakan zai sa na hana abinda yake shirin aikata maka karo na biyu.”
“Text?Waye ya aiko shi?”
“Ban sani ba, dan nima tun a ranar na kirkira number ba,tq shiga.”
“Zan iya ganin number.”
“Ok bari na duba, ina tunanin ban goge message ɗin ba ai.”
Gyara zaman sa yayi ta dubo masa number, da sauri ya dauki Number ya kira, ringing daya biyu aka daga, sai dai muryar data bayyana a wayar ta sake sashi a wani rudanin, bayerabe ne ya daga, cikin harshen sa na yarabawa, dole ya kashe yana jingina da kujerar dakin.
Kwana ɗaya yayi mata yace zai tafi, taso ya d’an kara zama sai dai yace mata zai dawo nan kusa, haka ya tattara ya wuce Kano, nan dinma kwanan sa biyu, ya komo abuja.
Jiran Daddy yayi har ya dawo ya same shi a falon sa, gaishe shi yayi a mutunce ya amsa kafin ya nemi izinin sanar dashi abinda ya kawo shi.
“Na yanke shawarar ajiye aikina, zan koma karatu a karo na biyu, na nemi izinin ajiye aike, sai dai sam shugaban mu ya ki amince wa, shine nake rokon ka saka baki dan Allah.”
“A wanne dalilin zaka ajiye aikin ka?”
“Akwai matsi da takura sosai, sannan ina son chanja akalar rayuwa ta ne, zuwa mutumin da zaka yi alfahari dashi a gaba.”
Da sauri ya kalle shi, sai kuma yayi murmushi
“Kana tunanin yanzu bana alfahari da kai?”
Be ce komai ba, ya sunkuyar da kansa kasa,
“Shikenan, zan yi magana, duk abinda ka zaba wa rayuwar ka, ina fatan hakan ya zamo Alkhairi a gareka.”
Sosai yaji dakin maganar, da sauri ya amsa da amin yana jaddada kansa a k’asa cikin tsananin farin ciki
“Sai dai akwai sharadi guda daya…”
“Ina so ka amince da auren kanwar ka Amal, hakan shine kadai buri na akan ka yanzu, idan kayi min shi nasan ka cika d’a nagari.”
Da wani irin shock Farouk din yake kallon shi, daga mishi kai yayi cikin gasgata abinda yace ya dora
“Idan har kana son ka samu damar barin aikin ka, ka tafi duk inda kake son tafiya tun da nasan kudurin ka na barin k’asar ne, toh tabbas sai ka auri Amal, idan yaso sai ku tafi tare, daga nan har karshen duniya bani da matsala da kai.”
Juyawa kansa ya hau yi, idan har shawarar sa ta kauracewa kowa na nufin auren sa da Amal, da kuwa ya sani be dauki wannan shawarar ba, sai dai ya sani Daddy ba zai taba kyale maganar ba, tun da har ya riga ya furta, idanun sa ne suka shiga dauko masa hoton Amal, duk da yana son ta, yana jin ta sosai a ransa, amma ba hakan na nufin zai iya auren ta ba, aure a irin wannan lokacin da bashi da nutsuwar zuciya, idan yayi haka be wa Aminatu adalci ba.
“Zaka iya zuwa kayi shawara sosai, zuwa nan da lokacin da zuciya ka zata zaba maka abu daya, sai dai ka sani, abu daya tak zan iya yi maka, in ma ka hakura da kudurin ka naa son nisanta kanka damu, ko kuma ka yarda da auren yar uwarka, zabin ya rage naka.”
Tirkashi!!!
Shin za’a yi auren nan?
Yaya rayuwar Aminatu zata kasance a gidan data samu kanta?
Sai yaushe zasu hadu da Farouk?
Waye yake ma Farouk makarkashiya?
Ina labarin d’an Inno ne wai?
Yaushe a kuma wanne irin yanayi Aminatu zata hadu da iyayenta?
Leggo????????????????????????????????????????????????????????????????????Hansatu R
20
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
★★★★
Kasa tashi yayi har zuwa sanda Mama ta shigo, da kyar ya ja kafafun sa ba tare da yace komai ba ya fito. Amal na tsaye a gaban part din su kunnen ta sakale da waya tana amsawa, tsayawa yayi chak yana kallon ta daga nesan, ya sani sarai Amal bata da matsala, zai iya cewa ma rainon sa ce, amma ya gaza gano dalili d’aya da zai iya bashi damar auren ta, takawa yayi har wajen da take, ya tsaya daga bayan ta yana son ya gano wani abu, cire wayar tayi daga kunnenta cikin farin ciki ta juyo, ganin sa tsaye yasa ta dan yi sak, sai kuma ta fadada fara’ar ta