DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“You!” Sai nayi kamar ban gane shi ba na juya kaina gefe. Gefen dana koma ya dawo ya sake zama yana leken fuska ta.

“Ji mana.”

“Wa kake nema ne Please?” Na watsa mishi wani kallo, dan tsaf na karance shi dan rainin wayo ne na ajin karshe, sosa kansa yayi kafin yace

“Shit! Kin iya rainin wayo wannan beb ɗin wallahi, kece dai ta ranar Exams din nan na gane ki.”

“And so?”

“And so? And so?”

Ya shiga nanatawa kamar karatu , sai kuma ya bigi gefen kujerar yana fitar da yar karamar iska daga bakin sa, sai kuma yayi murmushi m d’an sauti

“Can we be friends?” Yace yana miko min hannun sa,bin hannun nayi da kallo, kafin na girgiza kaina ina sake matsawa kadan

“Bana ƙawance da maza, infact ban ma tab’a ganin ka ba sai yanzu, sai kawai na saki jiki da kai?”

“Kaji matsalar yan matan garin nan kenan, kauyancin masifa. Go to hell!!.”

Yace yana mik’ewa, da ido na rakashi har ya bar wajen cikin tafiyar sa ta ya’yan da suka jiku da hutu, murmushi na saki kadan ina mamakin sa. Gefe na kalla ina sake sakin murmushi, ido na ya sauka a cikin na Ya Anas, yana tsaye ya harde hannun sa, fuskar nan tasa a gimtse, da sauri na dauki tarkacen kaya na na nufi wajen sa, bansan tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ina karasawa yaja dan karamin tsaki yayi gaba, na bishi.
Tada motar yayi muka fita daga makarantar, gefen window nake kallo ina ganin yanayin garin, tsaki yake tayi tun da muka fito, ban kulashi ba, haka ban kalli inda yake ba ma balle na san halin da fuskar sa take ciki. Murya a cunkushe ya soma magana

“Idan har kinsan irin wannan ƙananan yaran zaki tsaya kulawa ba karatu ba, sai ki sanar dani tun farko na daina wahalar da kaina.”

Juyowa nayi da mamaki na kalle shi, idon sa na kan titi ya hade girar sama da ta k’asa, sai nayi shiru kawai na maida kaina waje ina mamakin fushin sa. Har muka isa gida be sake magana ba, fita nayi na barshi a motar don naga bashi da niyyar fitowa.
Ina shiga na tarar da Altine na ta faman zagaye goye da iman, murmushi nayi na gaishe ta, ba karamin girman matar nake gani ba, kunto min ita tayi na karbe ta na shige ciki.
Dakin Hajiya na leka, na sanar da ita mun dawo, kadaran kadahan ta amsa ta cigaba da abinda take, kwana biyu akwai chanji sosai a yadda take min, sai dai na dau hakan a matsayin wani ɓangare na dan adam, ba lallai ne koyaushe ya zama kamar yadda ka san shi ba, idan ma babu wata matsala ai akwai lalura, zata iya yiwuwa bata jin dadi ne. Sai ban wani damu ba, na cigaba da al’amura na yadda na saba su.


Bayan wata biyu

Cikin nasara na soma zuwa makaranta, bani da matsala da iman dan lokacin ta fara shan ceareal, wajen Altine nake barin ta bayan na tabbatar da tasha ta koshi, sauƙin ta ma babu ranar da muke wuni a makarantar, duk inda azahar tayi mun dawo, hakan shi yasa nake jin dadin karatun ina kokarin ganin na samu abinda naje nema.
Bangaren Hajiya bani da wata matsala tun bayan rage shige min ɗin da Anas yake, sai ta sake muka koma kamar da, duk ban kawo komai ba.
Ranar wata talata na sauka a titi na shigo layin namu ina tafiya a nutse, nazo daidai wajen wani me dan kiaosk na saida katin waya naji maganar ta, bazan taba mantawa da muryar ba,muryar da zan iya cewa na daya daga cikin abinda ke makale a raina na yarinta ta, da sauri na isa wajen, ido bude nake kallon ta da tsantsar mamaki, idan har idona ba gizo yake min ba, kunnuwa na ba karya suke min ba,toh tabbas Amal ce. A bayan ta na tsaya cikin tsananin farin ciki ina jiran su gama, juyowa tayi da nufin barin wajen, taci karo dani, da wani irin tashin hankali ta ja baya, kamar zata koma cikin kiaosk ɗin

“Amal.” Na kira sunan ta cike da farin ciki sai naga ta hau jujjuyawa kamar me neman wani abu

“Amal baki gane ni ba? Aminatu ce fa.”

Gaba tayi da sauri har kamar zata fadi, nabi ta da sauri na cimmata ina kwala kiran sunan ta, ja tayi ta tsaya tana juyowa a fusace tace

“Wai lafiya kike bina?”

“Nice fa Amal, baki gane ni ba?”

“Na gane ki, sai akayi yaya?”

Washe baki na nayi ina tunanin matsala ta tazo karshe nace

“Nasan dama zaki gane ni ai, ina su Dadah da Ya Farouk, Allah Nagode ma daka hada mu.”

Dariya ta tuntsire da, kafin ta hade fuskar ta cikin isa tace

“Ke wai har yanzu baki manta da su ba, bayan sun manta da kina existing a duniyar nan, kinga karki takura min dan Allah, kar ma ki kuma nuna kinsan ni wallahi, ke da su kuma sai dai idan ana haduwa a lahira.”

“Me kike cewa Amal, kina nufin Ya Farouk ya manta dani, Dadah ma haka, idan kowa zai manta dani nasan su ba zasu taba mantawa dani ba,dan Allah ina Ya Farouk ina son haduwa dashi ko dan yar sa dake tsakaninmu?”

Na fada murya ta na rawa, daga min kai tayi, sosai naga yanayin fuskar ta ya sake sauyawa, ambaton yar sa da nayi, ja baya tayi

“Ya manta dake mana, tun da har ya aure ni, nice matar sa a yanzu saboda haka bana bukatar ki kusa da mijina da yan’uwa na, batun ya kuwa ke da kanki kinsan ya ƙaryata tun lokacin rabuwar ku, sai kije can ki nemi uban yar ki, idan kuma shegiya ce sai mu sani.”

Jiri ne ya soma dauka ta, na kalle ta ido na na ciccikowa nace

“Amal?”

“Abinda kunnuwanki suka ji haka yake, saboda haka karki bata min lokaci, kinga tafiya ta.”

Ina kallon ta ta juya tayi hanyar fita daga layin, kuka nasa sosai, na kasa daga kafata daga wajen, ina kallo ta haura daga layin, tun ina hango ta har na daina, durkushe wa nayi a wajen na saki kuka sosai kamar raina zai fita.

Rano
8a: DG
             24

★★★

Da kyar na mike kafata da tayi nauyi na karasa gida, a waja na tsaya na goge hawayen fuskata na shiga gidan, da kallo Altine ta bini tana karantar yanayin fuskar tawa, ciki nayi ba tare da na tsaya yar hirar dana saba mata ba.
   Ina shiga daki na sake sakin kuka, kuka me cike da ma’anoni da yawa, a yau komai ya dawo min sabo, ina ji kamar a yanzu komai yake faruwa dani, idan har da gaske Amal take, Farouk ya aure ta, to tabbas ya manta dani, ya rufe ni a cikin babin rayuwar sa kenan, idan ko haka ne bai kyauta min ba, bai min adalci ba, bayan ya koyo min yadda zan rayu da son sa, ya tafi ya barni a sanda nafi bukatar sa.
   Amal yar uwar sa ce, nasan shakuwar da ke tsakanin su, ban taba kawo hakan a nufin soyayya suke ba, sai yanzu nake hango wasu abubuwan da suka dangance ta din, ta yadda yake yake bata lokacin sa.
   Har Ramlah ta dawo daga makaranta ban bar kukan da nake ba, ina ji a raina ina bukatar nayi kukan, ko naji sauƙin zuciya ta, yadda ta tarar dani ne ya sa duk ta rikice, a dan zamana da ita na shaku da ita da har bana iya boye mata damuwa ta, ko ba haka ba ma ina bukatar wanda zai fada ma kuka na ko da ba da nufin a share min kukan ba, sai dai ko yaya na zanji sauƙin abinda ke damuna.
   Yanzun ma ban boye mata ba, na sanar da ita komai, girgiza kanta ta hau yi tana dawowa kusa sani sosai kafin tace

“Aminatu har yanzu baki san wasu matan ba, ya zaki yanke masa hukunci da abinda ta fada miki, ina kyautata zaton babu masaniyar sa a komai, a yaya kika ganta? A nutse take alamar wadda take cikin kwanciyar hankali tayi sabon aure, ko kuwa? Kuma baki yi tunanin abinda yasa ta yi miki haka ba? Bayan ko ni nasan yadda kika daukake ta a zuciyar ki? Abu daya ne, kishi take ko dai tayi kokarin samun abinda yake mallakinki bata samu din ba, ko kuma ta samu amma babu kwanciyar hankali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button