DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

BAKAR RANA!
Tana kwance ta bubbbude curtains din dakin ta saboda yanayin da ake ciki na zafi, gashi ranar babu wuta sai zafin ya kara yawa. Motsi taji kamar ana taba kofar ta, ta dan cire kanta ta dubi kofar na dan wani lokaci, maida kanta tayi ta rufe idon ta dan yadda baccin ke fizgar ta, ba zata iya hakura ba.
Yamma ce wajen karfe hudu da rabi, a ka’ida ba’a son baccin na rana, sai dai ita ta rasa dalilin jin nasa yau sosai, shiyasa ma ta kora Farouk da Ja’afar wajen Dadah tayi kwanciyar ta. Nan da nan bacci ya dauke ta me karfin gaske.
***Yau ranar daban take da dukkan ranakun da yake zuwa ganin gida, yau yana jin shi cike da son kasancewa da ita, yadda yayi kewar ta ba kadan bace shiyasa ma bai sanar da kowa zuwan nasa ba. A matukar gajiye ya shigo gidan, ya kalle bangaren Dadah sai ya wuce kai tsaye zuwa nasu bangaren, ta sallama ciki ciki ya tura kofar, yana son bata mamaki, shiru ko ina baka jin motsin komai. Ajiye kayan hannun sa yayi kai tsaye ya nufi dakin baccin su, da karsashi ya tura kofar ba tare da tunanin komai ba.
Runtse idon sa yayi ganin komai na dawo masa a ƙwaƙwalwar sa, hoton da ya riga ya zama permanent a cikin zuciyar sa ya shiga dawo masa, numfashi ya soma ja cikin fitar hayyaci jikin sa ya soma rawa, kokarin tashi yake daga wajen bayan ya saki diary din hannun sa ya kasa, sai ya koma yaraf ya zauna yana kokarin saita kansa yana bawa kansa k’warin guiwar tsayawa yabi komai.
Mugun gani kamar yadda ya kamata ya kira wannan rana, Abidan sa da kaninsa, a dakin sa na sunna cikin yanayin da zuciya da ruhi ba zasu iya dauka ba, da wani irin tashin hankali ya hau dukan su a tare dukka su biyun, duka irin na wanda yake jin kamar za’a zare masa numfashi ya bar duniyar.
Kallon cikin ido Adam ke yi masa, kwatankwacin kallon tsanar da Daddyn ke masa, jifa yayi dashi ya bugu da bango kansa ya fashe, a take jini ya shiga malala a wajen babu alamun rai a jikin sa.
Daidai lokacin ta kwalla ƙara tana kokarin neman abun da zata kare jikin ta, nufo ta yayi bayan ta samu nasarar jan dogon Hijabi ta zura ya shak’e ta, kakare ta hau yi kamar zata mutu, da kyar ta bude baki cikin galabaita tace
“Ka… Tsaya.. ka saurare ni, wallahi ba abinda kake tunani bane.”
Wurgi yayi da ita ta fada a saman drower ya shiga kokarin zare belt din jikin sa, daidai lokacin Dadah ta fado dakin a hargitse, abinda ta gani ya firgita ta, bata san sanda tayi kan shi tana kiran sunan sa ba
“Kabir!!! Zaka yi kisa, innalillah wa inna ilaihi raji’un.”
Sakin belt din hannun sa yayi yana ja da baya ya fita daga dakin da sauri, rudewa Hajiya tayi ganin jinin dake fita akan Adam, da sauri ta yo waje tana kiran Kabir ɗin. Chak ya tsaya lokacin har ya kusa fita daga gida, a gaban sa ta tsaya tana kuka sosai
“Dan Allah karka tafi, kar ya mutu ka taimaka wa uwar da bata san komai ba sai lafiyar d’an ta, dan Allah.”
Hannun ta ya kama, ya rike gam yana sauke ajiyar zuciya, sakin ta yayi ya koma ciki da sauri, yana zuwa ya daga shi ya fito dashi, ya saka shi a mota yaja ya fita daga gidan.
***Da rarrafe ta isa gaban ta muryar ta ta dashe saboda tsabar kuka, ta rike kafarta
“Dadah dan Allah kiyi min rai, ban aikata ba wallahi bansan komai ba, bansan mai ya faru ba, nasan kin yarda dani, nasan zaki fahimce ni.”
Ga mamakin ta sai gani tayi ta janye kafarta, ta bar wajen da sauri ba tare da tace komai ba.
Daki ta koma ta fada toilet ta sakar wa kanta ruwa, kuka take a cikin ruwan tana tunanin abinda ya faru, wannan wacce irin bakar rana ce? Waye zai saurare ta ya yarda da abinda zata ce? Tana nan zaune jigum har suka dawo daga asibitin, da sauri ta mike jikin ta na rawa ta yo wajen, tun kafin ta k’arasa ya dakatar da ita
“Karki ƙaraso nan, na sake ki saki uku! Keji ban yafe miki cin amanar da kikayi min ba.”
“Yaya!”
Aliyu ya fada da karfi yana shigowa ciki, da sauri Safiyya tayi wajen ta ganin yadda take layi kamar zata fadi
“Babu ruwan ka Aliyu, ta chanchanci fiye da haka ma, dan dai hakan shine karshen hukuncin da zan mata, taje na barta da Allah!”
“Amma Yaya da ka tsaya kaji uzurin ta, haba yaya, Anty Abidah ce karka manta kafi kowa sanin halin ta, ya ba zaka bata damar kare kanta ba?”
A zafafe Dadah ta kalle shi
“Kayi min shiru Aliyu, babu ruwan ka.”
“Dadah kema baki yarda dani ba? Baki san abinda zan iya aikatawa ba? Iya zaman da mukayi?”
Ta tambaya tana kuka sosai, girgiza kanta tayi
“Bani da sauran zama a inda ba’a san daraja ta ba, ba’a taba tsayawa a saurari uzurin ka balle kasa ran samun sauki, tir daku nayi dana sanin shigowa rayuwar ku, a yau ni Abidah na yanke dukkan wata alaƙa tsakani na daku, babu sauran komai tsakanin mu sai ta yarana guda biyu, dan yar uwata da Farouk, wanda su kuwa kamar dole na ne duk da haka zan tafi na bar su tunda ba dasu nazo ba!”
Tana kaiwa nan taja hannun Safiyya dake kuka sosai ta fita daga dakin fita ta har a abadah.!
*** *DG*
28
Da sauri ya rufa musu baya yana kwala mata kira, bangaren ta suka nufa, tana zuwa ta haɗa dukkan abinda tasan mallakinta ne, Farouk ne da Ja’afar suka shiga kuka ganin yadda iyayen su biyu ke kukan, tsaye uncle Aliyu yayi a dokin kofar ransa na mugun suya, mai yasa sam yayan nasu baya tsaya wa yayi bincike ne? Komai sai ya yanke hukunci a cikin fushi da bacin rai bayan ba haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar damu ba, lallai duk wanda zai biye wa zuciya yayin da ransa ya ɓaci zai iya aikata komai, ciki kuwa har da aikin da mutumin da ya fita daga hayyacin sa.
Gashi yanzu ya aikata abinda har ya bar duniya ba zai taba daina dana sani ba, saki uku, a lokaci daya? Saki da aka ce idan akayi shi al’arshi ce take girgiza. Anty Abidah bata chanchanci hakan daga gare su ba, matar data tsaya da dukkan karfin ta wajen ganin ta kyautata ma kowa.
Zuwa tayi zata wuce ta gefen sa yayi saurin tare kofar yana jin kamar alamun kukan shima
“Anty yanzu tafiya zakiyi? Dan Allah karki tafi.”
“Uncle Aliyu kenan, zamana ya kare a gidan nan, karka manta da babu igiyar auren yayan ka yanzu akaina. Alfarma daya zakayi min, ka taimaka min ka kular min da Farouk da Ja’afar, yayana ne dukkan su saboda haka amanar su na hannun ku ku biyu.”
Girgiza kansa yake ya rasa ina zai tsoma kansa, gaba yayi ya sake baya ganin yadda yaran ke kukan fitar hayyaci, hannu yaga ta bude musu suka tawo jikin ta gaba dayan su. Runtse idon ta tayi hawayen da take kokarin makalewa suka shiga saukowa.
“Allah yayi muku albarka!”
Sai ta janye su tayi hanyar barin gate din Safiyya na take mata baya.
A zafafe ya fada falon, wurga idon sa ya shiga yi har ya sauke su akan Adam dake jingine da kujera kansa na kallon kasa. Da sauri ya isa gareshi ya ci kwalar rigar sa, idon sa daya rine yayi ja ya sauke masa aka cikin matsanancin fushi yace
“Me yasa zakayi mata haka? Me yasa zaka manta alkhairin ta gareka musamman, baka san halacci ba?”
Kwace wa yayi daga rikon daya yi masa, cikin fushin shima ya taso masa
“Just stay out of this idan ba so kake kaima ka shiga lissafi ba.”
“Idan naki fa? Me zakayi?”
Murmushi yayi ta gefen bakin sa ya juyar da kansa