DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Umar!”
Dada ta kira sunan sa, yanayin Muryar ta kadai yasa ya gane abinda zata ce, kasa juyowa yayi har sa data maimaita kiran nasa.
“Na’am Swthrt.”
“Ba wasa nake maka ba, kasan kuma ni ɗin ba sa’ar tsohon ka bace balle kace zaka maida ni mara hankali ko wata chan daban, wacece yarinyar nan? Menene alakar ka da ita?”
Juyowa yayi yana fuskantar ta, ganin ta bata rai sosai babu alamun wasa yasa shi takowa har gaban ta. Sai da ya daidaita tsayuwar sa a gaban ta sannan ya fara magana cikin son gamsar da ita.
“Kiyi hakuri idan na bata miki rai, hakan da nayi ba wai nayi ne dan na bata miki ba, wallahil azim bani da wata alaƙa da ita,hasalima bansan wacece ita ba, bansan komai game da ita ba.”
“Aina ka samo ta toh idan baka santa ba?”
“A daidai lokacin da Allah ya saukar mana da daya daga cikin ni’imomin sa, a daidai lokacin wani mara imani ya aikata mata wannan aika aikar, babu digon tausayi ko imani a tattare dashi, bansan shi ba, bansan waye ba, ihun ta kadai naji, na taimaka mata.”
Kallon sa take har ya kai karshe, ganin bata ce komai ba yasa shi kama hannun ta
“Ki yarda dani, ba zan taba iya aikata wa wata mace makamancin wannan ba.”
“Naji! Amma menene dalilin ka na amsa wa likitar nan a matsayin kaine mijin ta? Baka tsoron maganar ta fita, bayan kasan waye mahaifin kuma.”
“Hakan shine daidai, karki manta wannan abun babban tabo ne a tattare da duk wata ya mace, da zai iya zama wani babban gibi a rayuwar ta. Banyi hakan da wata manufa ba face don kare mutuncin ta.”
Turo kofar akayi, hakan yasa yayi shiru yana duban su, Dr Iman ce sai wata nurse a bayan ta.
Dan dube duben su sukayi suka juya, har ta kai kofa ta juyo.
“Af na manta, akwai alluran da za’a yi mata da safe gobe, , so ka zama around please.”
“In Sha Allah.”
“Good.”
“Kai zaka kwana kenan?” Dada ta fada tana kura masa ido, har zai ce eh sai kuma yayi wani tunanin daban
“A ah, kece zaki taimaka.”
“Amal fa? Kalli a yadda tayi bacci.”
“Eh zanje na tambaye su idan akwai spare gado sai su bamu mu biya sai ku kwanta akai, dama dare yayi yanzu komawa hanyar nan akwai risk, in yaso ni sai mu kwana a mota.”
Dan jim tayi kadan kamar zatayi magana sai kuma ta girgiza kanta kawai ba tare da tace komai ba ta koma gefen gadon ta zauna tana kura mata ido kamar me karanto wani abu a tattare da ita.
Da safe na bude ido na ina karewa dakin kallo, daidai lokacin aka turo kofar aka shigo hade da sallama, zuba masa ido nayi ina kallon sa har ya iso gaban gadon, shi din ma kallon nawa yake fuskar sa dauke da murmushi. Juyawa yayi yana kallon Amal dake bacci hankalin ta a kwance, karar ruwan da yaji a toilet yasa ya gane Dada na ciki. Sake matsowa yayi gaban gadon ya furta a hankali
“Ya jikin?”
“Da sauki.” Na amsa da sauri ina kallo sa
“Sannu kinji.”
“Toh.” Nace ina sake bin fuskar sa da kallo kamar me son tuno abu. Murmushi ya sake yi yana kallon drip din dake shiga cikin jikina a hankali, file din dake ajiye saman drawer saka magunguna ya dauka yana dubawa har Dada ta fito.
***Yanayin horn din kadai ya tashi kowa na gidan, a firgice su ja’afar suka fito falo kowa ya tsaya, ba sai an fada musu ba sun san kowa ye, tsoron su daya abinda ya kawo shi a irin wannan lokacin, iya sanin su ma baya kasar baki d’aya. Motoci uku ne suka shigo a jere, kai kawo Baba maigadi ya shiga yi har suka daidai ta a harabar gidan. Cikin shigar sa ta Babban sojin kasa ya fito daga motar fuskar sa dauke da yanayi marar misaltuwa.
“Barka da zuwa.” Kawai kake ji kowa na kawo gaisuwa. Jiki a sanyaye su Ja’afar suka dunguma zuwa harabar gidan kowa tsoro fal zuciyar sa.
A daidai lokacin aka fara bugo da mugun karfi kamar za’a balla gate din gidan, hayaniyar mutane ke tashi da alama ba mutane ne kadan ba. Da sauri ya kalli Baba maigadi Yana neman karin bayani.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????
2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863
GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????
09032345899
Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????
Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN????????????????
DG
©️Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
ALKALAMI TV
https://youtu.be/LxY42ErBf_8
(4)
Babu wanda yayi kwakwaran motsi a cikin su, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa. Jin bugun na sake karfi ne yasa shi juyawa da kansa ba tare da yayi magana ba ya nufi hanyar gate din. Budewa yayi yana kallon mutane dake tsaye, wasu dauke da makami, ganin haka yasa sojojin sa suka yo wajen da sauri. Hannu yasa ya dakatar dasu yana bin mutanen daya bayan daya cikin tsananin tashin hankali, sai dai duk da hakan ba zaka tantance yanayin da yake ciki ba, fuskar sa tana nan kamar ko da yaushe.
“A fito mana da yar mu!” Muryar daya daga ciki ta bakunci jin sa, daya bayan daya ya hau kokarin fassara kalmomin acikin yan sakanni.
Take wajen ya kaure da ihun kalmar da yake da bukatar amsar ta cikin gaggawa. Sake daidaita kansa yayi, ya kuma saka dukkan jikin sa ya fito waje sosai yana sake duban su, mutane ne yawancin matasa sai wasu dattijai guda uku daga gefe, kai tsaye ya nufi wajen su, yana me sake daidai ta kansa. Yana isa ya mika musu hannu daya bayan daya, kwarjinin sa ya cika wajen baki daya. Lawan dake niyyar rashin kirki ya ji ba zai iya ba, girma da cikar haibar sa kadai ta isa ka girmama shi. Balle kuma da shigar sa ta nuna ainihin shi din waye ne. A nutse ya kai duban shi wajen sauran yaran kana ya maida kansa garesu
“Me yake faruwa?”
Ya tambaya yana nuna su Garbati,
“Yar mu wadda take cikin gidan nan muka zo tafiya da ita.”
“Yar ku? Kuyi hakuri ban gane kan maganar ba, zuwa na kenan.”
“Alhaji jiya daya daga cikin yaran gidan nan ya dauke mana yar mu, bayan mun gaji da neman ta muke samun labari ta wajen daya da ga cikin matasan garin da abin ya faru akan idon sa, toh jiya munzo a daren bamu samu ganin kowa na gidan ba sai Maigadi, shiyasa muka shiryo muka zo yanzu, dan har mun sanar wa maigari ma.”
Hannu yasa yana shafa kansa, be tsinci komai a bayanin ba, sai dai ya fuskanci suna zargin batan yar su ne a gidan sa, a gidan nasa ma kuma cikin yaran sa, dan jim yayi kadan yana nazari kafin yace
“Ku bani mintina biyu dan Allah ina zuwa.”
Juyawa yayi ya nufi cikin gidan, ya zo shiga Garbati ya daga murya yadda zaiji sosai yace
“Wallahi sai an fito da ita, ga Fyade ga sata, haba ai abin yayi yawa.”
Chak ya tsaya da tafiyar da yake, wani irin bugu zuciyar sa tayi, babu abu daya daya ki jinin ji kamar kalmar fyade. Maganganun da suka cigaba ne suka shiga maimaita kansu a cikin kwanyar sa, da sauri ya fada gidan, suna nan tsaye duk a in da ya barsu, daya bayan daya ya shiga binsu da kallo kamar me lissafa su, duk sun tsure iya kar tsurewa sun gama sanin me hakan ke nufi.