DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL


Tashi Ammi tayi da kyar bayan ta gama bawa kanta k’warin guiwar tunkarar ta, tashi Farouk yayi ya bata wajen yana komawa gefen Kamal.
  Da k’yar ta d’aga hannayen ta, ta ɗora su a saman kan Aminatun, kuka ya kuma kwace mata,

“Wacce irin rayuwa ‘yata tayi, wacce irin wahala tasha? Wannan wacce irin ƙaddara ce.”

Dago fuskar ta tayi wadda ta cika da hawaye ta rungume Ammin da dukkan sauran karfin ta, abinda take jira kenan itama tayi saurin sa hannu ta zagaye ta tana shafa bayan ta

“Ki yafe min, ki yafe min dan Allah, an cuci rayuwar ki, an saki maraicin karfi da yaji tun a karancin shekarun ki bayan baki da hakki akan kuskuren da muka aikata.”

“Ammiiiii….!” Ta ja sunan cikin tsananin kuka da ta kasa tantance na farkin ciki ne ko na akasin haka?

“Shissshh! Karki yi kuka, kukan ki ya kare, ke yar gata ce ta kowanne bangare, ba zan taba yafe wa Adam ba, ya cuce ni cuta mafi muni, akan me zai raba uwa da yarta tun zuwan ta duniya, wannan wanne irin rashin imani ne? Akan kuskure daya? Daya tak? Waye baya kuskure a rayuwa dan Allah?”

Idon Alhaji Marwan ya kada sosai yayi ja, tabbas Adam yayi masa cuta mafi muni, ba zai taba yafe masa ba, ba zai taba kyale wa ba sai ya nuna masa akwai banbanci, matsawa yayi har gaban su ya riko Aminatu ya mikar da ita, girgiza mata kai ya shiga yi alamun tayi shiru, da sauri ta fada jikin sa tana sakin kuka muryar ta ta soma dashewa, murmushin karfin hali kawai yake dan yadda yake jin zuciyar sa zai iya kukan. Ta jima a jikin sa tana kokawa da zuciyar ta.
  Ta gefe Farouk ya rabe ya fita yana jawo musu kofar, kai tsaye gida ya nufa domin dauko Iman, a yau yafi kowa murna. Anty Safiyya ta gama shirya su kenan shirin kwanciya bacci ya shigo, dagowa tayi ta kalle shi

“Kar kace min dauke ta kazo yi.”

“Anty!” Yace yana murmushi

“Naga aalama ne ai, yaran zamani.”

Sosa kansa yayi yana dariya kasa kasa

“Zan kaita ne wajen Ammi da Anty!”

“Auw toh mana, na zata ko rashin ta idon ne ya motsa.”

Murmushi yayi ya kama hannun Iman din suna barin dakin. Yanayin tafiyar sa kadai zata gamsar dakai da irin yadda yake ji,farin cikin sa ya gaza boyuwa kwata-kwata, har ya dangana ta da dakin da suke, yasa hannu kadan ya bude yana nuna mata ciki

“Shiga wajen Ummi kinji?”

Daga mishi kai tayi ta sa kai tana kallon ko ina, duk suka juyo suka zuba mata ido, da sauri Ammi ta tashi ta nufe ta tana goge fuskar ta

“Alhaji kaga, ikon Allah kalli Alhaji,.”

“Alhamdulillah.” Yace yana mika mata hannu ,

“Zo naji ki kusa dani, matso nan sabuwar amarya ta.” Ya karashe cike da barkwanci, duk sukayi dariya har Kamal da yake jin kamar ya gama cika burin sa.


Dakin Ammi ɗin ta jasu, ta rasa ina zata saka su, komai ta dauko sai ta mayar, kamar a mafarki Aminatu take ji, yau itace tare da mahaifiyar ta cikin yanayi me dad’i beyond her imagination.
  Basu samu runtsawa ba, daren ranar ta fayyace mata dukka rayuwar da tayi,ba karamin girgiza Ammin tayi da labarin ba, tayi kuka sosai sannan kuma ta gode Allah da ya sa yarta bata fada mummunan hannu ba har ta samu tayi karatu irin na yanci. Zata so taga Anas, ya tallafi rayuwar yarta, yayi mata gata. A halin yanzu ita zata tsayawa yarta, ta bata kulawar da zata manta radadin abinda ta kunsa.


Duk da bata da tabbacin zai zo kamar yadda yayi mata, sai dai ta gaza aiwatar da dukkan ayyukan ta na ranar tana dakon zuwan sa, ganin da gaske babu alamar shi yasa ta dauki wayar ta kirashi, hakuri ya bata yayi mata alkawarin zuwa gobe da ikon Allah.
   Tashi tayi zata wuce zuwa daki kiran Ja’afar ya shigo, ta so sha’afa da dawowar tasa, sai data ga kiran sannan ta daga a gaggauce

“Son…”

“Mummy yanzu zamu taso, zuwa dare in Sha Allah xamu iso.”

“Ok dear, Allah ya kawo ku lafiya, karka manta da kun sauka ka sanar dani, Idris zai jira ka ku taho direct nan Farouk ma zaizo.”

“Shikenan, sai mun zo.”

“Owk bye.”

Ta ajiye wayar tana dan bubbuga bayan ta da ke dan mata ciwo. Tun bayan gano in da yar uwata take ta hau shirye shiryen zuwa takanas wajen ta, bata sanar da kowa ba har dan gaban goshin nata, so take ta basu mamaki kawai, shiyasa ta gama shirya komai take so su je su hudu, ita, Ja’afar, Farouk da babbar yayarsu Anty Lami.
    
    

****Kwanan tsananin wuya Adam yayi, basu raga masa ba ko kaɗan dan Daddy yace kar su saurara masa bayan abinda Alhaji Marwan ɗin ya sanar dashi ya kara tunzura da lamarin Adam ɗin, tabbas babu digon tausayi ko rahma a zuciyar sa, dan haka suma ba zasu raga masa ba.
    A gajiye Daddyn ya tashi kamar wanda aka yi wa duka, kwana yayi yana tunane tunanen yadda abubuwan suka dinga faruwa a karkashin ikon shi, rainin hankalin da adam yayin masa yafi komai taba shi, sai kuma rashin bincike kwakkwara da beyi ba akan case ɗin Mummy, a yanzu babu wadda yake so kusa dashi sama da ita, sai dai yasan taurin kan ta da kafiyar ta ba lallai ta sauko da wuri ba, idan ma ta sakko ɗin, dole ana bukatar ta a yau, ta zama tana wajen komai zai bayyana, amma waye zai kira ta ta yarda tazo? Babu shi. Shiru yayi cikin tunani kafin ya mike da sauri, Safiyya ce kadai zata sata zuwan dole. A gaggauce ya shirya ya fito, Mama na ganin shi ta mike da sauri

“Alhaji, yau lafiya ka shige ciki tun wuri ka rufe kanka, duk hankali na ya tashi ban iya baccin kirki ba.”

“Baki da hurumin sanin abinda nake.”

Yace yana rabe wa ta gefen ta, baki ta rike cikin tsananin mamaki take kallon sa, sai daya kai kofa sannan yace

“Akwai meeting na gaggawa karfe sha biyu, idan lokacin ya cika ki same mu a gidan MD.”

Yasa kai ya karasa fita yana jin kamar ya dawo da baya ya faffasa mata baki da hanci yadda yake jin haushin ta.
   A harabar gidan ya tarar da su a tsaye suna jiran sa, duk suka sara masa da sauri, dakin ya nufa  suna take masa baya daya daga ciki yayi saurin bude masa kofar, kansa ya tura ciki yana kare ma ko ina kallo, yana kwance d’ai-d’ai yana fitar da numfashin wahala, fuskar sa ta haye tayi sumtum kamar bashi ba, babu mask din da yake sawa sai ainihin fuskar sa. Dagowa yayi ya zuba wa Daddyn ido har ya ƙaraso gaban sa, babu digo na sassauci a fuskar tasa

“Iya kar abinda zaka yi min kenan?” Adam ɗin yace yana murmushin karfin hali,

“Damage din da nayi muku kadai aka barku dashi nayi winning, na lalata maka dukiya na kuma cire hakki na daga ciki, sannan na raba ka da matar ka da kafi so, na hada ka danka tillo a duniya na kuma sauya masa tunani akan ka, yana maka kallon mara tausayi, na raba shi da matar sa, abubuwan da na aikata maka suna da yawa, kana tunanin Wannan hukuncin kadai ya ishe ka ramawa?”

Wuya Daddyn ya riko masa ransa a matukar bace

“Menene haɗin ka da Hajara!””

“Matar mu ce da mukayi tarayya akan ta!”

Da wani irin karfi Daddyn yasa hannu ya hankad’a shi, ya bugu da bango ya bishi ya take yana nuna masa hannu

“Sai na kashe ka!”

“Kuna ina!” Ya fada cikin k’araji

Da sauri suka shigo

“Karku raga masa ko kadan, kuyi masa dukan da zai kasa magana, but i want him alive har sai yayi confessing dukkan laifukan sa.”

“Yes sir.” Suka amsa a tare suna yin kan sa.


A yadda ya shigo kadai yasa suka sha jinin jikin su, zama yayi yana dafe kansa da hannu bibbiyu, matsowa Dadah tayi gaban sa ta riko hannun sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button