HAJNA 15-16

♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 15-16
A kwance ta samu Hajna, tada ta, ta fara yi “ke tashi yarinya ga abun arziki “, tashi Hajna tayi, ba tayi mamakin ganin Fahna ba dan dama sunyi Fahna zata dawo, “har kin dawo kenan” Hajna ta faɗa tans ɗaura ɗan kwalin ta, “ba dole ba, Alhaji Qaseem yace dole sai na kawo Miki waya yau “, “waya! Hajna ta faɗa tana zare ido, “eh fa waya, ko baki so ne in mai da mishi”, Fahna ta faɗa, Hajna tace “yanzu ya zanyi da wannan wayar me zan cema su Umma”, Fahna tace “yanzu ki tashi ki nuna wa Umma”, “in ce mata me? “Hajna ta faɗa tana dafe ƙirji, “ce mata zaki yi ni na siyo miki, ni kuma sai ince kar ta gayawa Baffa, ai umma bata da matsala”, murmushi Hajna tayi dan ko babu komai zata riƙa jin muryar Qaseem, tashi tayi ta fita.
A ɗaki suka sami Umma, da gudu Hajna ta shiga tana murna, “minene ya faru Hajna, naga kin shigo kina murna” Umma ta tambaya, “Umma kin ga fa, waya Fahna ta kawo min “, “ahhh madallah kin gode”, “Umma amma karki gayawa Baffa “Fahna ta faɗa, “to shikenan Fahna, amma ina kika samo ta?”, “wanda zai auri Fateema ƴar aunty Kareema ne ya kawo min ita, ni kuma ban daɗe da siyen wata ba shine nace bari na ba Hajna ko gaisawa ba sai mu riƙa yi ba”, murmushi Umma tayi tace “eh gaskiya kin yi dubara, amfanin abota kenan, ku taimaki juna, Allah ya daɗa shirya min ku “, “Ameen”, suka faɗa a tare, tashi suka yi suka fita. Umma kuma ta cigaba da gyara kayan ta dan dama ita bata cika tsaurarawa yara ba.
Rungume juna suka yi suna murna, Hajna tace “good idea”, nan take suka kunna wayar, kiran shi suka yi sai da ta kusa katsewa ya ɗauka, “Hello ‘Fahna ta faɗa, “hey”ya faɗa cikin salon yaudara, Fahna tace “da fatan ka gane mai magana”, “eh me zai hana, Fahna right? “ya faɗa yana gyara kwance, “eh nice, ga number Hajna nan, na cika nawa aikin”, murmushi yayi yace “ na ƙara miki da gida “, Fahna sai washe haƙori ake yi 5mil, ga gida ga mota, miƙawa Hajna wayar tayi “karɓi kuyi magana”, “Hello” Hajna ta faɗa cikin sanyi murya, wani yarrrrrr yaji a jikin shi, cikin kasalalliyar muryar shi yace “hey baby “, lumshe ido tayi a hankali tana jin son shi har jikin ɓargon ƙashin ta, tabbas Qaseem shine namiji na farko da ta fara so a rayuwar ta, murmushi tayi mai sauti, jin sautin murmushin ta ya ƙara narkar da shi, ji yake ina ma tana gaban shi ya rungume ta, ko ya samu sauƙi, “ina wuni “yaji ta faɗa can ƙasan maƙoshin ta,ohh my good ya faɗa a ranshi, amma a zahiri yace “ alhamdulillah, love kefa”, wani fari tayi da ido jin yace mata love tace “ina lafiya “bayan sun gama gaisawa yace mata zai kira ta da daddare.
Bayan sunyi sallama, Fahna ta koya mata yadda ake operating wayar ba abunda bata koya mata ba, da yake Hajna na da basira nan take ta gane duk abunda aka koya mata.
Da dare yayi sai Hajna ta shige ɗaki tayi kwanciyar ta kamar yadda ta saba, rufe ɗaki tayi, kwanciyar ta ke da wuya Alhaji Qaseem ya kira ta, bugu biyu ta ɗaga kiran, sai da suka raba dare suna waya, bayan sun gama waya ne ta yi barci, yau kam tayi lattin sallah, Baffa mamaki ya kama shi ganin Hajna na arwala da rana tsaka,“ ke bakiyi sallah bane ” ya tambaya, “eh baffa jiya kwana nayi ciwon ciki”Hajna ta faɗa tana yamutsa fuska, “sannu Allah ya yaye miki wannan ciwon”, dama Hajna tana da matsakar ciwon mara, wanda yake na sha’awa ne, sha’awar ta na da ƙarfi sosai.
Sallah tayi sannan ta yi aikin gida kamar yadda ta saba, gyara ko ina tayi sannan ta koma ɗaki, kunna data tayi ta fara chart dan dama Fahna ta buɗe mata WhatsApp, ganin Qaseem tayi online, gyara zama tayi suka fara chart, video call ya kira ta, sun jima suna chart har sai da aka yi sallar azahar, fitowa tayi waje tayi arwala, ɗakin Umma tayi sallah, sannan suka shinfiɗa tabarma suka zauna dan kamar kullum yau ma basu da abinci a gidan, fira sukayi, da la’asar Baffa ya shigo da dawo da nono yace a dama fura su sha ita ta samu, Umma ba tayi musu ba suka dama, Baffa suka zuba ma a kofi Hajna ta kai mishi ita waje, sannan suka sha suka yi hamdala, dan ita Umma macece me haƙuri da godiya da duk abunda ya samu.
******************************************************
Kwanaki tafiya suke yi, yau wata uku kenan da haɗuwar Hajna da Qaseem, wanda yanzu Hajna ta cire tsoro, ta ware ranakun da Qaseem ke zuwa gurin ta, a bayan makarantar su inda gurin ya kasance gurin ɓuyan su da Fahna, nan yake zuwa su sha soyayyar su.
Yau ta kasance ranar Alhamis inda ba makaranta, dan haka Hajna tana gida zaune, kuma yau kusan kwana biyu kenan da bata samu sunyi waya da Qaseem ba, wanda take jin haka kamar barazana ne ga rayuwar ta.
Zaune take a ƙofar ɗakin ta, yadda zata samu Qaseem take tunani, dan bata ma jin daɗi jikin ta, yau zazzaɓi take fama dashi, ji tayi wani yaro shigo, “salamu alaikum, ana sallama da malam Ibrahim, cewa da mahaifin Hajna, fitowa yayi daga ɗaki, fita yayi waje , wata dan ƙareriyar mota ya gani wadda be taɓa ganin irin ta ba, wani kyakkyawan saurayi ya fito daga ciki, gaisawa suka yi Baffa yace “sai dai ban gane ba “, sai yace “eh bazaka gane ba da farko dai ni sunana Muhammad, na zo nan ne domin na taimaka maka saboda ranar naganka kana neman taimako”, murmushi Baffa yayi yace “Allah sarki to na gode “, nan driver da Muhammad yazo da su suka buɗe boot aka dinga kwasar kayan abinci ana shiga dashi cikin gida, buhun shinkafa guda 10,kwalin taliya 5,macroni kwali biyar, indomie kwali 5, galam ɗin man gyaɗa 3,na manja biyu, sannan da dubu ɗari yayi cefane, Baffa ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin yadda aka taimaka musu, Baffa yasa aka kira mishi Hajna da Umma su mishi godiya, fitowa suka yi, kamar ance Hajna ta ɗaga ido ta kalla, wa zata gani Qaseem, wani sanyi taji a ranta, ni kuma mamaki ya cika ni, miyasa ya canza sunan shi daga Qaseem zuwa Muhammad.
Anan zan dasa aya.
Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️❤️❤️❤️❤️❤️