Uncategorized

MAKAUNIYAR KADDARA 3

     Babu musu Zinneerah ta zauna duk da ranta fal tsoro.

         Ƙare haɗe fuska Inna tai tana dubanta da ƙyau. A tsawace tace, “Miya maidoki garinga?”.

       Sosai gaban Zinneerah ya ƙara tsananta faɗuwa. Murya na rawa tace, “Inna sune suka koroni. Sunce basa buƙatar baƙauya irina. Kuma saida suka shinhiɗa mani uban bugu da aibantani kahin su bani jikka biyu da rabi su sani a mota….”

      “Munahika, halan wata tsiyar kika ƙulla masu acan? Saboda kina buƙulu da abunda zan samu na hassahi daga kuɗin aikin naki?”.

      “Wlhy Inna ba haka bane. Matar gidance bata sona dai na rantse”.

       “Ruhwa mani baki dan bantan ubanki. Ai hajji Lanti zatazo ne, zanji gaskiyar zance a gareta. Wa billahillazi naji saɓanin abinda kika hiɗi yanzu ina halakaki na halaka banza wohi babu mai sanin yanda akai. Ƴar banza, kinhi son mu zanna ga ƙugunki ga nawa a gida. Sabidda kina kishi dani tunda uwarki bata gida? To mu zanna ga hili ga mai doki ai. Dan uban mutum yayi idan yana iyawa dani ko. Tashi ɓacemin a ido kahin naita tsinarki har se zaman Danya ya gagari ubanki ma bake kaɗai ba”.

       Mikewa Zinneerah tai tana shartar hawaye. Duk da cin zarafi ga inna ba yaune farauba a gareta. Sai na yau ɗin yay mata zafi ainun. Karon farko taji tana kwaɗayin son sanin inda mahaifiyarta ke rayuwa a yanzu.

    Ɗakin kwanansu ta shige, ta faɗa akan yamusashshiyar katifar da Yaya Sa’a da Tinene ke kwana. Dan ita bisa tabarmar karauni take kwana kamar yanda Inna take buƙata. Dauɗaɗɗun kayan dake gefe ta jawo ta shiga rufawa a jikinta saboda sanyi da takeji.

     Sosau ta ringa rawar sanyi tana sambatun zazzaɓi. Har tsahon lokaci babu wanda ya shigo ɗakin. ba kuma ta ƙarajin motsin Inna ba. A haka barci yay gaba da ita mai nauyi.

      “Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”.

     A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa.

       Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya.

      “Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..”

      Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”.

       “Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”.

      Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na haɗa miki wutar tunda ita batajin daɗi. Harma sakin danwaken yau nice zan miki Innarmu kwantar da hankalinki”.

    Baki taɗan taɓe. sai dai batace komaiba. Hakan yasa Gajeje fahimtar taci nasara. Tai murmushi da tura hannu a zaninta ta ciro leda dake a lalitarta ta bujen ciki. Goro ne da alawa da biscuits guda biyu ƴan goma-goma. “Innarmu ga kayan suna”. Tai maganar tana miƙa mata.

      Ɗan sakin fuskarta tayi da miƙa hannu ta amsa. “Yo kuma ƙya bani duka. Su su Rabi’u fa?”.

      “Karki damu na ba Salame ta kai musu nasu suma. Wannan nakine. Nima Agali ya bani shi bayan mun hito”.

      “To, to maddala. Ni bamma sami leƙawaba yau na tashi da ƴar mashashshara ne. Sai zuwa anjima zanje nai masu an raɗa suna. Miye sunan ɗiyar ne?”.

       “Ai Hadiza aka samu, sunan Innar Bilkin aka saka”.

     “Tofa ɗigifi. Shi yanzu duk yawan gidansu ya rasa wazai saka sai sunan uwar matarsa?”.

      Ƴar dariya Gajeje tayi tana yafito Zinneerah dake tsaye rakuɓe jikin bango da hannu. “Inna kenan, ashe babu daɗi Lawal ya sakama Ummita sunanki shima”.

     Shiru tai bata tankaba. Dan an ƙure tsoguminta kenan.

    Zinneerah ta zauna tana gaida Gajeje. Cike da kulawa ta amsa mata da kai hannu a jikinta. Jin uban zafin ya sata ambaton, “Ya subahana. Zinni ai masassara ce a jikinki sosai. Kin karya dai ko?”.

      Ƙasa Zinneerah tai da kanta tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata. Dan harga ALLAH yunwarma tanajinta mai tsananima kuwa. Saboda Inna batai mata tayin abinciba yasa ta haƙura.

     Shirunta yasa Yaya Gajeje fahimtar bataciba ɗin. Tasan za’a rina. Dan innarsu lamarinta sai du’ai. Bata sake cewa komaiba kamar yanda itama Innar bata tanka musu ba. ta dai miƙe zuwa gindin murhun inda tukunya ke aje saman duwatsun murhun. Tuwone a ciki na dawa da aka yanka aka ɗumama. Duk ma ya zama gutsatstsari alamar masu gidan sunci. Yaya Gajeje da ranta ke mata ƙuna ta ɗauka kwano ta zubama Zinneerah, tare da koriyar miyar kukar dake gefe. Har gabanta takai ta dire tana fadin, “Maza ci na samu mai sayo miki magani nan gidan Rahine idan bata fita tallar kayan koli ba”.

      Jan kwanon Zinneerah tayi gabanta, babu musu ta hau ci dan yunwa takeji sosai..

     Inna dai bata sake tankawaba har Zinneerah ta gama cin tuwon nan. Yayinda Yaya Gajeje ta koma can wajen murhu tana haɗama Inna wutar ɗanwake da ƙoƙarin saka ƙatuwar tukunyar da take amfani da shi.      

            Kasancewar Yaya Gajeje a gidan yau sai ta samu ƴar salama. Dan har Baba daya shigo shima ya ɗan samu sakewar bata kulawa, harda siya mata awara. 

     Washe gari kam Inna bata saurareta ba. Duk da ta fahimci har yanzun bata da lafiya, dan ba’a ƙulla awa biyu Zinneerah bata raɓe gefe tana riƙe cika ba alamar dai cikin na mata ciwo. 

      Sai dai tsabar rashin tausayi ko’a fuska Inna bata nuna ta fahimtaba, daga ƙarshema tallar riɗi da gyaɗa ta sakata ɗauka. Da Sa’a tayi magana kuwa ta hayayyaƙo mata da masifa kamar zata daketa. Dole tai shiru tana maijin babu daɗi da halin mahaifiyar tasu.

★★★

            Yau satin Zinneerah ɗaya kenan da dawowa da ga Katsina. Tun Inna na zuba idon ganin Hajji Lanti ta biyo bayan Zinneerah harta fara sarewa. Dan har ranta ta ɗauki alwashin sai Zinneerah ta koma, bazata taɓa yarda kuɗin data ƙwallafa ran samu su wuceta a banza ba.

       A ɓangaren Zinneerah kam a kwanakin nan daka kalleta kasan bata da lafiya. Musamman yanda ta wani rame sosai. Gashi sam bata da kuzari a jikinta. Yanda ta saba aiki ada da kazar-kazar yanzu sam bata iya hakan. Komai zakaga tana yinsane da sanyin jiki kamar mara ƙashi. Inna tayi masifar harta gaji ta barta, sai dai zagi da tsina ne tana shansa, dan ranar har marinta tayi.

       Yau ma kamar kullum tana gama ɗibar ruwa da dukkan aikinta na gidan tai shirin ɗaukar tallar riɗi da gyaɗa. Tinene kaɗai ta samu a tsakar gida tana suyar wainar fulawa. Inna kuwa ta fice barka wai. 

      Ɗakin Inna ta shiga ta ɗakko ƙaton farin botikin da aka cika da gyaɗa da riɗi, ta sake fitowa tsakar gidan. Cike da sanyin murya tace, “Tinene idan Inna ta dawo ki hiɗi mata na wuce”.

      Kallon banza Tinene tai mata ta ɗauke kanta. Cike da rashin mutunci tace, “Inma wannan allagiran kike mawa kima cire rai yarinya, dan aradu baki cin ko ranyo anan”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button