MAKAUNIYAR KADDARA 3

Murmushi Zinneerah tayi kawai ta fice, dan tasan inhar ta biyema Tinene zama su iya faɗa, itako bata da wannan ƙarfin yanzu kam.
Dai-dai fitowarta ƙofar gidan nasu gabanta ya faɗi. Tai ƙasa da kanta saboda cin karo da fiska mafi daraja a zuciyarta bayan ta iyayenta. Ba kowa bane face saurayinta Babawo wanda a yanzu ya maida akalar neman auren nasa kan yayarta Karima da yaya Sa’a ke bimawa. Babawo ya sota tun bata san kantaba. Da farko matsin rayuwar data tsinci kanta a hannun Inna dalilin rashin mahaifiyarta a gidansu Babawo yake tausaya mata. Shine silar cigaba da karatunta bayan gama firamare , shine ya tsaya tsayin daka harta shiga makarantar gaba da firamare (Secondary), tana aji ɗaya wani kawunsa ya zo ya tafi da shi kaduna. Bai dawo ba sai da ya shekara. Kamar yanda ta ɗokantu da zuwansa haka shima ya ɗokantu da ganinta. Yazo mata da tarin tsaraba, tare da burin iyaye su shiga akan maganar aurensu, a cewarsa data kammala aji uku na sakandire zasuyi aure. zai wuce da ita can kaduna sai ta cigaba a gidansa har sai taga ƙarshen biro. Hakan yama Zinneerah daɗi a zuciya da ruhi, sai dai kuma a kwana biyu da zuwan Babawo labarin ya canja alƙibla. Dan kuwa bai komaba sai da tsuntsun soyayyarsa ya tashi daga kanta ya koma kan yayarta Karima yar wajen Inna ta uku. Ƙiri-ƙiri ta gaza gane kan Babawon ta, ya canja mata gaba ɗaya. Kosan ganinta bayayi. Taci kuka sosai, ta kuma shiga ruɗani, dan har ciwo tayi. Mutane sunta kace nace akan wannan al’amari, wasu na faɗin asiri Inna taima Babawo ɗin, wasu suce kuma shine dai yake ganin Karima ta fiye masa tunda ita babbar budurwace wadda akema surutu akan rashin samun miji. Dan Karima shekararta sha takwas da wasu watanni, a ƙauyen kuma sa’annin su Zinneerah sune dai-dai aure ƴan sha biyu. Amma sai dai ita ƴaƴan Inna dama sukanyi jinkirin samun miji a ƙauyen saboda mugun halinta, shiyyasa ma har yau babu wacce ta taɓa aure a nan cikin Danya. Gajeje na kauyen Sanni, Atine na can Rimaye. Sai yanzu ga Karima da Sa’a waɗanda duk sun zama manyan ƴammata. Karima nada sha takwas Sa’a na sha shida. Sai Tinene sa’ar Zinneerah itace auta.
Bayan wucewar ruɗanin canjawar Babawo da shekara ɗaya da wasu wattani, dan har manya sun shiga maganarsa da Karima sai kuma Inna ta haɗata da hajji Lanti da tai sanadin kaita birnin Katsina da niyyar aikatau, inda ita kuma ta gudo ta dawo gida……..
“K! Wai baƙyaji ana miki magana”.
Tsawar da Babawo ya daka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi batare data farga ba. Saurin haɗiye hawayen da suke neman zubo mata tayi tana girgiza masa kanta.
Ta ɗan risina kaɗan tana faɗin, “Kayi haƙuri Ya Babawo banji bane wlhy”.
Tsaki yaja yana taɓe baki da jifanta da wani irin mummunan kallo na tsana, wanda a da idan wani yay kuskuren yimata irin wannan kallon sai inda ƙarfinsa ya ƙare. A gadarance yace, “Kiramin Karima nace”.
Idonta ƙasa-ƙasa tana mai satar kallon yanda ya ƙara ƙyau da cikar zati tace, “Yaya Kareema bata nan, tana Rimaye wajen Yaya Atine, nima ban dawo na sameta ba”.
Tsaki yaja yay gaba batare da ya sake tanka mataba. Ta bisa da kallo cike da tsananin so da ƙaunar da take masa har yanzun. yayinda ƙamshinsa daya bar mata take jinsa mafi daraja da tsada a cikin iskar da take shaƙa. Duk da ƙarancin shekarunta zuwa yanzu tasan minene soyayya, dan shine ya rene ta akan bigirenta, tun bata fahimta harta fara ganewa da banbancewa, sai gashi rana tsaka rabuwa tazo musu bisa tafarkin MAKAUNIYAR ƘADDARAR da batasan sila ko mafarinta ba, tunda har yanzu bazata iya faɗin dalilin rabuwar tasuba balle dalilin komawar Babawonta kan yayarta.
Hannu tasa ta sharce hawayenta tana gyara riƙon botikin gyaɗa da riɗinta ta cigaba da tafiya ranta na mata zafi da ƙuna………….✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki????????????????.
*_★ AL-ƘIBLA_*????
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*????
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*????
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*????
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*????
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi????????????????????????????????.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????