MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

Shuru tayi tana nazari! da tayi rantsuwar ba zata ‘kara shiga gidan ba saboda abunda ya faru amma dole ta karya rantsuwarta Halisa ta wuce komai a gurinta…….Mayafi ta yafa suka fito tare….Abbah ganinta tare da Yaya Ramlatun yasa shi sauke ajiyar zuciya, ya kama hanyar fita suka bi bayansa.

Sai bayan sun hau titi ya kalleta tana zaune kusa dashi fuskarta babu yabo babu fallasa dan farin cikin haihuwar Halisa yasa ta danji sasaauci a cikin zuciyarta……Sassauta murya yay yace.”Yaran sunyi bacci ko.”? Umm sunyi bacci sai dai da safe Dan Azimi ya kawo su.” Yace.”To shikkenan.” babu wanda ya sake magana a cikinsu har suka isa gidan.

Yaya Ramlatu da Najaatu kai tsaye gurin Halisa suka nufa, ikon Allah suna shiga dakin suka tarar da Zainab zaune a gefan gado da baby a hannunta ita kuma Halisa lokacin tana toilet Zainab saurin sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar had’a ido da Ramlatu addua take Allah yasa Najaatu bata fad’a mata abinda ya faru ba……Ya Ramlatu zama tayi kan sofa tare da cewa bani ‘yar.” Zainab da sauri ta miqa mata babyn tana gaisheta. amsawa tayi hankalinta nakan babyn tana murmushi! Zainab simi simi ta kama hanyar fita! Najaatu ta bita da kallo cike da takaici…….Karo suka ci dashi yazo zai shigo yace.” Kina ciki dama.” Tace”Eh Aunty Halisan ta shiga toilet. ” Nazarinta yay na minti biyu kafin yace.”okey kije gurinki ganin nan zuwa.” Zainab ta wuce shi shi kuma ya shiga dakin Halisan……….

*MADADI!*

*91*******Najaatu kasa tayi da kanta lokacin daya shigo d’akin kallon fuskarsa bata kaunar tayi saboda abinda yayi musu dazu ita da Halisa a ganinta duk wani rashin son zaman lafiya daga gurin Zainab yake fitowa kuma yasan gaskiya amma yake takewa yake goyan bayan Zainab din a duk lokacin da zata kawo masa magana baya tsayawa yayi binkice a kai zai hau ya zauna ya yanke hukuncin da bai dace ba, tabbas Zainab zata iya raba zumuncin dake tsakaninsa da ‘yar uwarsa tunda bata da hakuri! ta tabbata Yaya Ramlatu ba itace bata kauna ba halinta ne bata so yanzu ina laifin wanda ya nuna yana kaunar d’anka a gaban mutane ta kunyata ta nuna ba zata bata ‘yarta ba a gaskiya al’amarin yayi mata ciwo sosai tana rokon Allah ya bata nata itama.

Muryar Ramlatu taji tana fad’in “Au! ashe wuta tazo ta kunna maka a gida anya kuwa Abbas wannan yarinyar baso take ta had’aka da kowa ba, ina tunanin ma zumuncin dake tsakanina da kai zata raba tunda har ta iya zuwa ta kawo maka ‘karata kai kuma kazo ka tsaya a kaina kana tuhumata.”

Sassauta murya yay yace.”Nifa ba hayaniya nace kiyi ba magana muke ta fahimtar juna Zainab tazo tana kuka tana fad’in “Kin tara jamaa kun taru kun ci mutuncinta shine nake so naji dalili amma ni Zainab bata isa ta had’ani da kowa ba.”

Yaya Ramlatu za tayi magana Najaatu ta katseta da fad’in “Yaya kiyi shuru dan Allah ba girmanki bane tunda ita ta raina ki bata ganin kimarki mu muna gani bana so kina sa kanki a cikin sabgar da zata sa girmanki ya zube.

 Ramlatu tace”A’a Najaatu ba zanyi shuru ba tilas nayi masa bayani dan saboda ya daina ganin kamar takurawa matarsa akayi ni da ita daku duk d’aya kuke a gurina abinda yasa na tsaneta mugun halinta kuma har yanzu idan na kalleta sai raina ya baci idan na tuna da marin da tayi min bayan haka tasa dan uwana ya dauko min ‘yan sanda.” Fashewa tayi da kuka tana fyatar majina!

Hankalinsa ne ya tashi shifa baya tayar da maganar bane dan rai ya ‘baci yana so su fahimci juna da ‘yar uwarsa dan baya son irin bambamcin da take nunawa a tsakanin matansa amma ba dan ya ‘bata mata rai ya tayar da maganar ba, Najaatu ganin Yaya Ramlatu na kuka sai itama ta fara, Halisa ta fito daga toilet ta tarar dasu suna kuka shi kuma sai magana yake musu…..Tace”Yanzu ashe Abbah Mufida maganar nan bata mutu ba nifa tashin hankalin nan ya tayar min da nakuda wallahi.” Yace.”Halisa magana ta mutu tuntuni tambayarta nake akan abinda ya faru shine take kuka sabida rashin fahinta.”

Halisa ta samu guri ta zauna tare da fad’in “Yaya dan Allah ki daina kuka Zainab fa karya take ta shiga tsakaninki da Dan uwanki kome za tayi kuwa ki daina damuwa.”

Yaya Ramlatu ta goge hawaye tare da kallonsa tace”Kace kana so kaji abinda yasa matarka kasa zama a gidan biki ta dawo gida ko.” Yace.”Eh.” Tace”To Najaatu tayi sha’awar ‘yarta sai ta nuna ta bata aro tayi mata kwana biyu kai tsaye tace ba zata bayar ba, haushin haka yasa nayi mata fad’a saboda raina ya ‘baci sosai da yanda ta nuna rashin kwaicinta a kan ‘yar uwarta amma babu wanda ya zage ta ko yaci mutuncin iyayenta duk wata magana da tazo ta fad’a maka karya take.”

Shuru yay yana nazarin maganar…….Abinda yasa yay saurin yarda da maganar Zainab din sabida yasan akwai rashin jituwa a tsakaninsu sannan Halisa da Najaatu sun nuna masa kansu a had’e yake ma’ana sun cire Zainab daga cikin su shiyasa ya yarda da cewar za’a iya had’a baki dasu aci mutuncinta tunda kishiyarsu, sai kuma yanzu da yaji farkon al’amarin ya fahimci furucin Zainab din ya janyo duk hatsaniyar shima yaji rashin dad’in abinda tayi ina laifin wanda ya nuna yana son naka, a zamansa da Zainab ya fahimci halinta na rashin iya magana da rashin kawaici da hakuri mutukar akan hakkinta ne bata iya yin shuru shiyasa yake tsoron wani abu na sa’bani ya shiga tsakaninsa da ita sabida hanashi bacci take da daddare, ya lura su kuma su Halisan suna ganin kamar tsoro ne yasa yake biyewa Zainab din da duk abinda tazo masa dashi wanda kwata kwata ba haka bane a gurinsa kawai yana jin tsoron rashin hakurin ta da mitar ta dan kwata kwata abu naya wucewa a gurinta ta dinga nanata magana kenan…………Ya jima a tsaye a dakin yana nazarin al’amarin kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Halisa dake kokarin sawa babynta nono yace.”Ina fata babu wata matsala ko.”? Tace”Babu matsala.” Yace.”To sai kiyi kokari kici abinci kamar yanda Dr Saadatu ta fad’a miki kisha magani kafin ki kwanta.” Tace.”Insha Allahu.” Sallama yayi musu ya juya da niyyar fita daga dakin….’Yar uwarsa ce kawai tayi masa magana Halisa da Najaatu shuru sukayi suka bishi da kallo har ya fice daga dakin.

 Bayan ya dawo daga sallar asubahi ya sameta ta idar da sallah zama yay gefan gado had’e da kiran sunanta” Zainab” amsawa tayi tare da juyowa tana kallonsa, yace.” zo nan.” Jiki a sanyaye ta miqe taje ta zauna kusa dashi.” kallonta yayi a nutse yace.”Jiya Yaya Ramlatu dik ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku wanda har yanjo ta kasa hakuri tayi miki fad’a kan abinda kikayi wanda ke kika daukeshi da wata manufa, banji dadin abinda kikayiwa Najaatu ba ina laifin wanda ya nuna yana son naka.” Shuru tayi tana zumbura bakinta ita yama za’ayi ta dauki ‘yarta ta bawa ma’kiyarta ai ba zai yiwu ba.”

Yace.”Koda ba zaki bata ba ai bai kamata ki fito ki fad’a mata gaban jamaa ba kin nuna mata iyakarta akan abinda take da iko dashi koda bana auranta zan iya bata d’ana ta ri’ke sabida cancantarta to ballanata a matsayin uwa take a gurin Ummi tabbas nasan kamar yanda zata kula da d’an cikinta haka zata kula da Ummi amma meye na nuna mata iyakarta.”

“Abbah Mufida nifa koda ba ita taba ba zan iya bada d’ana yaje wani guri ya kwana bs kuma ni ban fad’i maganar da wata manufa ba dan da nasan zasu dauki zafi to da nayi shuru da bakina yarinya dai ‘yata ce sai nayi niyya zan bayar.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button