MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu  babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

 *******Humm! Rayuwa kenan Naja’atu ‘yar gata kuma  ‘yar gaban goshin Abbah Abbas  ita ce kasance a wulakance a lalace a hannun Bash!  shi yaci mutuncinta mahaifiyarsa da ‘Yar uwarsa suci mutuncinta su wulakanta su takata yanda ransu yake so, gabadaya munira ta sanja mata tsakaninsu kallon banxa ne da baqar magana, sosai take   cikin mawuyacin hali da takura  wayarta kuwa dama tuntuni ya ‘kwace dan ranar da zai kwace wayar tana jin mahaifiyarsa na zugashi a kan ya kwace  wayar domin wai barin wayar a hannunta a kwai matsala kada taje ta tona masa asiri a gari…….Aikuwa a ranar ya kar’be wayarsa ya barta cikin halin bakin ciki da damuwa kasancewar wayar na d’ebe   mata kewa  sosai  haka dai cigaba da ta kasance  cikin  damuwa gami  da nemawa kanta mafita domin tana ganin Bash da mahaifiyarsa da ‘Yar uwarsa rayuwarta  kawai suke nema to idan ba hakaba me tayi musu da zafi da zasu dinga  a zabtar da ita! abinci sun daina bata mai kyau wani sa’in ma yini take da yunwa a gidan sai taji tana shirin mutuwa tukkuna za taje ta tsaga billeta tace tana bukatar abinci to nan ma sai anja mata rai za’a sa mai aiki ta kawo mata shima ba wanda zai gamsar da ita ba, hakanan take hakuri ta kar’ba taje taci ta kwanta, sannan komai dare Bash ya dawo daga yawonsa haka zai afka mata yayi ta sasakarta tana ihun wahala saboda gabadaya rashin gamshashshen abinci mai gina jiki yasa ni’imar ta ta dauke kullum a bushe take qamas!  haka bash yake gwada mata rashin imani yayi ta jajjagarta yana kokarin kaita lahira…….Aikuwa kafin kice kwabo ta lalace ta zama tamkar zautacciya kusan kullum cikin firgici take daga ta kwanta bacci za tayi ta muguwayen mafarkai marasa dadi!   rashin abinci da rashin kwanciyar hankali da kulawa ya mayar da Naja’atu shuru shuru kullum tana dakinta a zaune ko a kwance yanzu ta daina wasa da ibadah lokacin sallah nayi za tayi   ta  d’aga   hannunta  sama tana rokon Allah ya kawo mata mafita.

Ranar Lahadi Mommy da Munira tun safe suka fita gidan sai ya kasance shuru kadaici da damuwa ya isheta sai ta shirya tsaf ta fito cikin hijabi ta fito  harbar gidan tana kalle kalle so take ta samu ta fita daga gidan taje ta nemi gidan mmn sajida ko zata taimaketa da shawarwari tunda dai mmn sajida tasan labarin rayuwarta to watakila akwai irin taimakon da za tayi mata.

Maigadin gidan ne taga ya bude gate mota ta shigo gabanta ya yanke ya fad’i dan a tunaninta ko Bash ne har tana mamakin abinda ya dawo dashi kuma! sai taga bashi bane mahaifinsa ne ya fito daga motar yana sanye da ‘kananun kaya shart da  jins da farin gilashi a idonsa, dama bata ta’ba ganinsa ba sai a hoto  kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana jin faduwar gaba! wani irin kallo Alhaji Aminu yake mata, da sauri ta tsuguna har kasa tana gaisheshi.

Yana wani murmushi irin na shegun ‘yan duniya ya amsa yana shafa gemunsa ta mike tana kokarin komawa gurinsu….Yace.”Doghtar  zo muje akwai muhimiyar maganar da nake so nayi dake.” A sanyaye ta kalleshi  tana mamakin maganarsa wace irin magana zaiyi da ita, cikin zuciyarta tace ko dai ya samu labarin bakar wahalar da muta nan gidan suke baki zai rarrasheki! A jiyar zuciya ta sauke tabi bayansa cikin gidan tana jin faduwar gaba  kad’an.

Kasa nutsuwa tayi a palon sanin da tayi cewar babu kowa hatta da mai aiki bata zauna ba itama ta tafi sabgoginta tunda tasan da cewar masu gidan basa nan tayi tafiyar ta sai da yamma zata dawo tayi aikace aikacenta.

Tana zaune a inda take taji muryarsa yana kiranta daga cikin dakinsa…Ta amsa da sauri ta mike ta nufi dakin….Gabanta ne yayi wani irin faduwa ganinsa daga shi sai gajeran wando a tsaye a bakin kofar dakin…Da sauri ta juya zata fita kawai taji ya ri’ki hannunta ya janyota ta fad’o jikinsa! taji yana kici kicin kulle kofar….”Innalillahi wa’ina ilahi raji’un! Abinda ta ambata kenan tayi kukan kura ta bangaje shi da mugun gudu ta fita daga dakin tana gyaran hijabinta daya tattare! A sukwane ta fito a harabar gidan tana rarrabawa idonta sai haki! take tana waige waige! can ta nufi bakin gate gabanta na dukan uku uku! tana kokarin bude karamar kofa maigadi ya fito daga dakinsa ai kafin ma ya karaso ta bude ta fice daga gidan….maigadi daya fuskanci cewa itace sai ya mayar da kofar ya rufe ya koma ya zauna hankalinsa kwance dan baiyi tunanin guduwa tayi ba…

Hanya ta kama ta dingi tafiya tanayi tana goge hawaye gami da nanata kalmar innalilihi wa’ina ilaihi raji’un! jama’a wane irin gida Allah ya kaita Ashe shima maigidan d’an busuru ne? wai shin to da yake kokarin kulleta a dakinsa me yake shirin yi mata.

Tsayin wata uku da tayi a gidan bata ta’ba ganinsa ba saboda washe garin daurin su yayi tafiya, a tunaninta dawowarsa kenan! amma saboda tsabar shi mara mutunci ne  zai haike mata a matsayinta na matar d’ansa! Babu shakka rayuwarta na cikin gagarimin had’ari! dole ne ta nemawa kanta mafita tun kafin wata mummunar qaddara ta afka mata.

Taci bakar wuya kafin ta kai kanta gidan mmn sajida, lokacin ma da taje bata nan ta tafi kasuwa cefena, sai ta samu rumfar kwanon da jama’a ke zama ta zauna tana wani irin nishi mai wahalar gaske……..Duk wanda zai wuce sai ya kalleta kai wasu ma har tsayawa suke suyi mata magana, ganin haka yasa tayi shahadar shiga gidan mmn ladi! tana shiga soron gidan ta soma jin  muryar mmn ladi sai zage zage takeyi! kafin tayi wani yunkuri taga mutum ya fito yana gyara kwalar rigarsa sai zabga tsaki yake, da yake Saleh ba a cikin hayyacinsa yake ba bai ma ganta ba yasa kai ya fita daga gidan….Naja’atu tayi kasaqe tana jiyo mmn ladi na fad’in “Shege tsinanne wallahi na daina yarda kana yi min hawan qawara kullum sai kazo kana cikani da dad’in baki  da daddare ka haye kaina kayi ta suburbudata amma washe gari idan na tambayi kudin cefane kace baka dashi to wallahi na daina yarda da kai  tunda abun ya zama rashin mutunci to  kwanan auran ma siyarwa zanyi idan kana bukata sai ka biya kudin zan barka kayi aikin banza kawai.”!!

Naja’atu gabanta ya tsananta fad’uwa shin wane irin zaman aure mmn ladi takeyi da mijinta? idan akwai matsala su rabu ai babu dole mai zai sanya kullum su dinga tsinewa junansu….Gidan ta shiga da sallama a bakinta, mmn ladi na huci! tace” Ke kuma daga ina? dama baki tafi garinku ba.”? a sanyaye tace”Na tafi qaddara ta sake dawo dani.”

Mmn ladi taja tsaki mai qarfi tace”Ke! kowa da kika gani yana da matsala dan Allah kada kice zaki fad’a min matsalarki ki rabu dani naji da matsalar da ta dameni.

Zama tayi kan tabarma tace”Mmn ladi dan Allah zauna mu fuskanci juna.” Mmmn ladi tayi mata wani irin kallo kafin ta zauna tana kallonta tace me kike shirin fad’a min ne.”?

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button