MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

Cikin ‘bacin rai yace.”Kiyi min shuru nace! wato har wani fuffuka kike kina maganar yarinya yarki ce bayan kin gama azabtar da ita ashe akwai ranar da zata zo kiyi wannan maganar to ki daina cika baki idan nayi niyya wallahi zan dauke yarinyar daga hannuki na kaita duk inda raina yake so sai naga k’aryar so.” Shuru tayi gabanta na bugawa jin abinda yake fada.

Yace”Anjima ki shiga gurin Halisa Yaya Ramlatun nan ki bata hakuri kan abinda ya faru kinji ko.” Murya na rawa tace “To.”

Kwanciya yay kan bed din tare da tsirawa rufin dakin ido, Zainab hijabin jikinta ta cire taje ta kwanta kusa dashi, itafa tunda taga Najaatu da ciki to itama sai ta samu hankalinta zai kwanta, jikinsa ta shiga tana shashshafa kirjinsa tare da sumbatar fuskarsa, duk da yasan wuya zata bashi hakan be hanashi kar’bar tayin ta ba rungumeta yay a jikinsa yana mayar mata da martanin abinda take masa.

  Najaatu da Yaya Ramlatu na zaune suna karyawa suka shigo tare, Tinda tayi musu kallo daya ta dauke kanta, Zainab ta nemi guri ta zauna shi kuma ya tsaya suna gaisawa da ‘yar uwarsa, Najaatu ba tare ta kallesa ba ta gaisheshi cikin kulawa ya amsa yana tambayarta Halisa tace”Tana bandaki…. Bakin bed din ya zauna yace “Bani yarinyar.” Babyn dake hannuta ta bashi kamar yanda ya bukata ta juya ta cigaba dayin break dinta.

Zainab a sanyaye tace”Yaya Ramlatu dan Allah kiyi hakuri akan abinda ya faru jiya.” Yaya Ramlatu tace”Haba ai ni bani da ri’ko ‘yar nan magana ta wuce a gurina.” Zainab tace”Nagode insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba kema Najaatu ki gafarce ni ban san maganata zata ‘bata miki rai ba.”

Najaatu murmushin takaici tayi tace”Babu komai magana ta wuce.”

Abbah yaji dadi sosai ganin yanda Zainab ta dauki nasihar sa dan baiyi tsammanin zata nemi afuwar Najaatu ba sai gashi tayi masa bazata, sosai yaji dadin abinda tayi…….Sai da halisa ta fito daga toilet suka gaisa sannan yay musu sallama ya tafi kasuwa.

Zainab kuwa zama tayi tana ta kokarin wanke kanta ita lallai sai sun manta abinda ya faru, Halisa dai da Ramlatu suna sata a maganarsu amma Najaatu idan tana magana tasa mata baki shuru takeyi dan bata son abinda zai sake had’asu suyi ta hayaniya sai kace wasu karnuka a ganinta yanzu duk an daina irin wannan kishin jahilcin.

Bayan sallar la’asar ya kirata a waya tare da sheda mata cewar yanzu yay magana da Dan Azimi zai zo ya dauketa ya mayar da ita gida.” Tace.”Da kabari idan kazo sai mu tafi tare.” Yace.”Aa ki dai zauna a shirye Dan Azimi zai zo ya dauke ki shawarar dana yanke kenan.” shuru tayi bacin rai ya hanata cewa komai dan ma kada ta kashe masa waya yaji haushi da tuni ta kashe, tana jinsa yana magana ta dinga umm eh da ya gaji da abinda take masa sai kawai ya kashe wayarsa ransa a ‘bace

Najaatu dauke masa wuta tayi lokacin daya shigo gidan ma tuni ta bar falo ta shige daki tayi kwanciyarta tasan abinda yasa yace ta dawo gida sabida yana so yazo ya haye kanta yay abinda yake so, ita da take biya masa bukatarsa ta kowane fanni itace abar wulakantawa a gurinsa aikuwa zata nuna masa tasan abinda take sai tayi sati bata amincewa bukatarsa ba in yaso yaje can gurun Zainab din ya ‘karata 

Abbah babu yanda beyi da ita ba akan ta tashi taci abincin daya shigo dashi tace ta koshi alhalin data dawo ba tayi girki ba tunda ta cika cikinta da abincin mejego take jinta a koshe!

A kammala cin abincinsa yaje yayi wanka kamar koda yaushe turare ya shafa a jikinsa sannan ya kwanta kusa da ita……………Matsawa tayi can karshen gado tana takure jikinta, ganin abinda tayi yasa ransa ya ‘baci sha’awarsa ya danne ya juya mata baya tare da jan bargo ya rufe kafafunsa.

A haka sukayi bacci ita tana gabas shi yana yamma!

Ta dauka da safe zai sanja mata fuska sai taga bai nuna mata komai ba yace tayi maza ta shirya da wuri zai fita, a gurguje tayi wanka ta shirya ko beak fast ba suyi ba suka fita………Can babban gidan nasa suka nufa tare. A tsaitsaye ya duba maijegon da ‘yarta ya nufi gurin Zainab itama suka gaisa kana ya wuce kasuwa…..Haka suka dinga yi har akayi suna duk ranar girkinta tare suke fitowa da daddare su tafi tsayin sati guda babu wata mu’amula da ta shiga tsakaninsu, ya daure ne yana so ya nuna mata cewar bafa lallai sai da jima’i ne zai rayu ba idan dan saboda yana jin dad’i da ita take masa iskanci to taje ta huta…..Bangaranta ta dinga mamakin dauriyarsa a yanda tasan shi da rashin hakuri bata ta’ba tsammanin zai iya yin sati daya ba ba tare daya kusance ta ba…….Ranar nan tana bacci kawai ta farka taga baya kusa da ita sai ta dauka ko toilet ya shiga kofar toilet din ta tsirawa ido tana jiran fitowarsa, shuru be fito ba, mikewa zaune tayi da sauri sabida jin maganarsa k’asa-‘kasa a falo.” Ta sauko daga bed din ta bude kofa ta fita….Samun sa tayi cikin duhu maqale da waya a kannensa, jin yana kiran sunan Saadatu yasa taji gabanta ya fad’i!…….”Inaso in aureki mutukar kina sona kuma zaki iya zama da iyalina lafiya.” Abinda kunnuwanta suka jiye mata kenan, ta sake kasa kunne tana sauraransa….”To nagode sosai dama nasan ke nutststsiya ce kina da ilimi daidai gwargwado dalilin daya sanya ma kenan naji ina sha’awar auranki saboda haka insha Allahu cikin satin nan zan turo da sadaki bana so aja dogon lokaci tunda ni dake duka ba yara bane.” Najaatu jin tana neman faduwa a gurin yasa tayi saurin tura kofar dakinta ta shiga, wanda motsinta yasa yay saurin kallon bakin kofar….A nutse ya cigaba da maganar da yake yi da Dr Saadatu a waya ba tare da ya nuna wata damuwa ba

Sai da ya gama wayarsa tsaf sannan ya koma dakin, samunta yay a zaune yayi saurin d’auke kansa daga kanta yaje ya kwanta inda yake kwanciya baya ya juya mata kamar koda yaushe yaja bargo ya rufe jikinsa, Najaatu taji kamar tayi masa magana sai dai ta daure zuciyarta ta kwanta hawaye na zubo mata lallai dama ashe duk wannan abun soyayya ce a tsakaninsu Amma matar ta bata mamaki wallahi sai da ta gama sanin sirrinsu sannan zata zo ta aure musu miji hummm aikuwa ba ita kadai zata shaqi takaici ba dole ta sanarwa dasu Halisa halin da ake ciki dan ta lura kamar ‘boyewa yake sai ranar daurin aure suji labari to yau dai Allah ya tona masa asiri 

Washe gari da safe kadaran kadahan suka gaisa da juna har ya zauna yayi break fast a gidan, amma babu wata mu’amular arziki a tsakaninsu ita dashi dai duk daurewa suke amma suna galabaita kansu 

Koda Halisa taji maganar mamaki tayi sosai tace”Amma Dr Sa’adatu ta bani mamaki wallahi wato shiyasa ta’ki aure ashe shi take so ta aura to Allah ya sanya alkairi.” Najaat cikin takaici tace”Abinda zaki ce kenan aunty Halisa.”? Tace”To me zance in ba haka ba ni dake da zainab babu wacce ta isa ta hanashi abinda yayi niyya saboda haka sai mu taru muyi hakuri Allah yasa abokiyar arziki ce, itama zainab zan sameta nayi mata magana dan na santa da rashin hankali zata iya tada husuma abin yazo ya shafe mu.”

Najaatu dai shuru tayi tana jajanta al’amarin.

To koda Halisa tayi masa maganar kai tsaye yace.”Gaskiya ne maganar da taji zai auri Dr Sa’adatu a matsayin matarsa ta hud’u kamar yanda Allah ya hallata masa.” Saboda gudun ‘bacin rai yasa tace” To Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar arziki ce.” Cikin jin dadi ya amsa da ameen…….Zainab kuwa ai haukane kawai ba tayi ba dan shi da kansa ya fad’a mata halin da ake ciki ta rasa inda zata tsoma ranta taji dad’i! hankali a tashe ta samu Halisa wai su tattauna maganar, Halisa tace”Kije ki kwantar da hankalinki kawai aure babu fashi! dan haka tayar da hankalinki na banza ne watakila ma ki janyowa kanki bacin rai! idan ta shigo zata zama daidai dake ai ba budurwa bace bazawara ce mu kuwa kinga da budurcinmu duk ya aure mu ai magana ta kare.” Zainab tayi zukud’um fargaba da damuwa duk sun dameta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button