MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

Cikin sati hudu kacal akayi komai aka gama, Halisa da Zainab gida D’aya Najaatu da Dr Sa’adatu a gida d’aya, dan kafin zuwan ranar daurin auran ya siyi wani ‘katon fili dake jikin gidansa wato gidan Najaatu ya shigar dashi gidan ya sanya ma’aikatansa suka tashi aiki abunka da masu abu a hannu kafin zuwan lokacin komai ya kammala, yanda ya zubawa Najaatu kayan daki ita amarya haka ya shirya mata dakinta ita kadai a ka kawo masa gidan………….

Abban ango sai zumudi yake yi matayen nasa suna kallonsa gami da kallon ikon Allah sai kace wanda zai auri budurwa duk ya tayar da hankalinsa…………..Amarya nayin kwana ukunta na musulnci ya dawo zagaye kamar yanda ya saba! Zainab taga al’amarin bana zama bane yasa ta dage da gyara jikinta dan shiryawa tayi tsaf taje gurin wata mata me maganin gargajiya ta fada mata dukkanin abinda ke damunta, matar ta had’a mata maganin sanyi masu kyau tayi mata bayanin yanda zatayi amfanin dashi wai ashe rashin ni’ima da kuma bud’ewar da gabanta yay duk sharrin sanyi ne shiyasa bata gamsar da mijinta, sosai zainab taji dadin maganin dan dama itama al’amarin na damunta tasan kuma maigidan nata yana hakuri da lalurata wannan dalilin ya sanya data koma gida ta mayar da hankalinta sosai gurin amfanin da maganin.

Tsakanin Najaatu da Dr Sa’adatu akwai fahimtar juna dan duk masu hankali da nutsuwa ne Dr Sa’adatu duk sanda zata tafi gurin aiki sai ta shiga gurin Najaatu tayi mata sallama itama Najaatun sa’i da lokaci tana shiga gurinta a cikin ranar ku da bata da aiki su jima suna hira kafin ta koma gurinta, hakika wannan jituwar da suka samu a tsakaninsu ta janyo suka ‘kara martaba a idanun maigidan nasu.

To alhmdullhi Zainab tana ganin amfanin maganin data kar’bo dan tun kafin ya ‘kare kwalliya ta biya kudin sabulu dan duk sanda maigidan nata zai kusance yana samun biyan bukata sosai har ya nemi ‘kari kuma itama a nata ‘bangaran ta daina jin zafin da take ji tana bashi hadin kai dari bisa dari……….Abbah na samun kulawa sosai ta bangaran matayensa guda uku ta bangaran Najaatu ne har yanzu yake da matsala dan kusan sati uku kenan rabon daya had’a shimfida da ita gashi kullum cikin jin sha’awarta yake duk da yana samun biyan bukata a gurin matansa amma yana marmarin ni’imanta mai wahalar samu……Yau dai girkinta ne yana ganin dole ya hakura ya nemi shiri dan yini yay yana tunaninta da yanayin salon soyayyar da take masa idan suna tare.

Tunda ya shiga gurin nata yake ta janta da magana sai wani lalla’bata yake duk inda ta gifta idonsa a kanta tun bata gane komai ba har ta fahimci cewar ya sakko yana neman shiri wato ya gama zagaye zagayen nasa ya dawo dama ai tayi rantsuwar akan ba zata nemeshi ba tunda tasan tana da amfani a gurinsa dole ya kawo kansa……..Mikewa yay ya nufi bedroom tare da cewa tazo ta matsa masa jikinsa ya gaji, tasan fad’a yay amma ba abinda yake nufi ba kenan……Tana sane gurin matsar ta dinga tatta’ba masa inda tasan hankalinsa zai tashi! aikuwa ba’aje ko’ina ba ya janyota rungumeta yay ‘kam! ya shiga marmatsa mata jikinta jikinsa in banda rawa babu abinda yake……..kirjinsa ta tura ya fad’i a bed din ta haye kansa tare da kokarin cire kayan baccin dake jikinta, gabadaya ficewa yay daga hayyancinsa ya dinga sakar mata zafafan kesses tare da murza breast d’inta da mazaunanta, a daran soyayya sukayi irin wacce suka dade basu irinta ba

 *BAYAN WATA BIYAR*

Lokacin cikin Najaatu yayi wata tara haihuwa ko yau ko gobe, girman cikin ya sanya babu abinda take iyawa sai dai komai Dr Sa’adatu tayi mata tun cikin na da wata bakwai Dr Sa’adatu ta dauki dawainiyar yi mata girki tsaf ta shirya mata daining kuma miji ya kwana da ita, Dr Sa’adatu nada mutunci da kyawun hali ta dauki ragamar kula da Najaatu hannu bibbiyu abunda take yi akan Najaatun yasa ta kara martaba da daraja a idon mijinta ya dinga alfaharin auranta dan ganin yanda take bada gudumawa a rayuwarsa data iyalinsa kwata kwata bata d nuna kishi ko ganin kyashi a kan abinda take……………..Wannan karon ma Najaatu a gida ta haihu tare da taimakon Dr Sa’adatu Allah ya sauketa lafiya inda ta haifi ‘yan tagwaye duk maza lafiyayyu dasu, sai dai bayan haihuwarsu mahaifa tayi gaddamar fitowa kamar dai lokacin haihuwar Daddy Dr Sa’adatu ta dinga fama tana dabaru irin nasu al’amarin yaci tura dan Najaatun tuni ta durkushe a gurin kanta yana juyawa! Da sauri tacewa mijin nasu ya fito da mota suje asibiti itama al’amarin yafi karfinta Abbah bai ta’ba sanin haka mata suke shan wuya gurin haihuwa ba sai akan Najaatu tsabar tausayi sai da ya zubar mata da hawaye, ga dai ‘ya’yansa tsaf yana ganinsu da rai da lafiya amma Najaatunsa na halin rai da rayuwa…….Tare da ita dashi suka sata a mota Dr Sa’adatu ta goya d’aya ta rungume daya a kirjinta ta shiga motar yaja suka tafi asibitin nasarawa inda take aik….Ko kafin su isa ya kira Halisa a waya ya sheda mata tare da bata umarnin ta biyo bayansu asibitin domin ta taimakawa Dr din da wani abu, Halisa bata tafi ba sai da ta sanar da zainab Halin da ake ciki Zainab jikinta yay sanyi ta nemi guri ta zauna gabanta na fad’uwa hankalinta ya kwanta ta samu ciki zuwan wannan ranar itace garari gadai Najaatu ta haihu amma rayuwarta na cikin k’ila wa’kala! Jiki a sanyaye ta shirya ta nufi asibitin itama.

Najaatu ta galabaita mutuka kafin mahaifar twins d’in ta fito ko bayan ta fito ma jini ne ya tsinke mata hankalin narses din yay masifar tashi, itakam Dr Saadatu duk kwarewar ta akan aikinta kasa katabus tayi tsabar fargaba da tashin hankali! (Ubangiji Allah kasa muga da ita lafiya had’arin haihuwa nada yawa)

Da kyar aka samu nasarar tsayar da jinin dake fita, aikuwa ba’aja da nisa ba aka sa mata wani gudun abunda ka iya zuwa ya dawo………..Sai bayan hankali ya kwanta ne ya samu damar kiran wayar ‘Yar uwarsa Ramlatu ya fad’a mata haihuwar yace ta fad’awa su Hajia suna asibiti, Yaya ramlatu ta tambayeshi lafiyar maijego da yaran yace suna nan lafiya lau be fada mata abinda ya faru da Najaatun ba…..

Naja’atu sai data kwana uku a kwance a asibiti sannan ta dawo daidai ta fahimci abinda ta haifa da kuma jamaar dake zuwa dubata! Alhaji da Baba Malam zuwansu biyu asibitin dubata, Baba Talatu kuwa tunda tazo sau daya bata sake zuwa ba tana ganin kamar zuwan nata bashi da amfani tunda ba itake bada lafiya ba bayan haka kuma Mutanan na iya bakin kokarin su akan Yarinyar shiyasa ta zauna a gida ta cigaba dayin addua akan ‘yar tata. Aunty Maryam kuwa kullum da ita ake yini a asibitin sai yamma tayi take tafiya……Koda suka koma gida ma haka ‘yan uwa da abokanan arziki suka dinga zuwa dubata tare da ganin yaran har bayan kwana bakwai ‘kafa bata dauke a gidan ba.

Abbah kudi ya fitar masu yawa yayi hidimar haihuwa dasu maijego da ‘ya’yanta yay musu hidima sosai hakanan suma sauran matansa da ‘ya’yansa yayi musu daidai gwargwado ranar da suka ware domin suna kowa ya fito gwanin ban sha’awa, haihuwar Hassan da Husaini tayi albarka sosai dan gidan ma’kil yayi da jamaa ta kowanne fanni kowa yazo nuna farin cikinsa, Zainab ta sauko ta mayar da komai ba komai ba har ‘yan uwanta sai da suka zo bikin sunan, Itama Halisa nata ‘yan uwan sunzo kamar yanda itama Dr ta gayyato nata dangin dukkaninsu har yaran suka had’u a falon Dr Sa’adatu suka sashi a tsakiya suna ta daukar hotunan tarihi! Abbah Abbas sai murmushi yake duk ya rasa inda zai saka kansa sabida farin ciki duk inda ya waiga sai yaga iyalinsa cikin walwala da farin ciki sai kawai ya shige godewa Allah a bisa ni’imar da yayi masa burinsa ya cika ya had’a mata hud’u gashi sun fara tara masa zuria abinda yake mutukar so a rayuwarsa yanzu ‘ya’yansa bakwai bayan d’an da Halisa ta haifa babu rai yana rokon Allah ya cigaba da azurta shi da ‘ya’ya masu albarka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button