MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

Naburago ya share fuska da hankici ya shiga fada masa abubuwan da suka faru, Abbah ya dinga mamakin al’amarin kafin ya kalleshi a nutse yace.”Babu komai na yafe maka insha Allah magana ta wuce Allah ya kiyaye gaba.

Naburago godiya yayi masa sosai ya miqe da niyyar tafiya, Yace.”Yanzu wace Sanaa kake.”? Naburago yace.”Bani da sanaa Alhaji sai buge buge nake.” Yace.” Gobe kazo kasuwa zan sama maka gurbin zama sai ka cigaba da taimakawa kanka da mahaifiyarka .”

Naburogo ya rasa wace irin godiya zaiyi masa, Abbah yace.”Daina gode min ka godewa Allah domin shine ya nufe ni dana taimaka maka Allah yasa ka zama alkairi a tare dani.” Naburago ya daga hannu sama yana godewa Allah tare da adduar Allah ya daga darajar wanda ya taimakeshi……Tun daga wannan rana Naburago ya zama dan kasuwa. Allah kenan babu yanda baya shirya al’amuransa (Babu laifi idan mutum yayi maka sharri kayi masa alkairi kafi shi a gurin Allah)

*BAYAN SATI BIYU*

Ya kasance yau saura kwanaki biyu su tafi kasa mai tsarki kamar yanda ya fad’a mata duk wani shirye shirye ya gama ya kuma shedawa matayensa, Halisa dai bata nuna wata damuwa ba, Zainab ce dai ya rasa inda ta dosa, kuka takeyi mai wai itama tana so yaje da ita, yace ta bari da azimi sai suje gabad’ayansu, K’in yarda tayi ta dinga kawo masa hujjojinta na cewar ai itama daya aureta be je da itaba dan haka idan umara zashi to kawai yayi tafiyarsa shi kad’ai ba sai yaje da kowa ba…..Gajiya yay ya kyaleta dan baya so ya fad’a mata maganar da zata sake hargitsa ta dan ya lura yarinyar nada masifar kishin tsiya.

Ana ya gobe zasu tafi Najaatu taje tayi sallama iyayenta suka saka mata albarka tare da fatan zuwa da dawowa lafiya ……Hajia da Alhaji ma adduar da sukayi kenan Yaya Ramlatu ta dauki Daddy ta goya shi a bayanta dama yaron ya saba da ita shiyasa baiyi wani kuka ba da zata tafi ma tayi tai ta d’aukeshi ya’ki! Hajia tace” Koda kin tafi ba zai damu ba tunda ya saba damu kuma yana cin abincinsa ai babu abunda zai sameshi har kuje ku dawo.”…….Wannan maganar ta hajia yasa hankalinta ya kwanta dan dama tana ta tunanin yanda za’ayi ta tafi ta bar yaron sai kuma gashi yayi mata bazata.

Kamar jira ake su tafi Halisa ta kama ciwo zazzabi da mura kwana biyu data gaza gane abinda ke damunta sai kawai ta tafi asibiti Dr Sa’adatu ta dubata tsaf ta fito da kyakkyawan result ciki na sati uku….Halisa ta dinga mamaki da ikon Allah, Ashe dai tana da rabon wata haihuwar wallahi ita har ta fitar da rai addua ta shiga yi kan Allah ya bar mata cikin kada ya zube 

Ta koma gida cike da murna da farin ciki amma bata tunanin zata fad’awa maigidan sai cikin yayi kwari tukkuna dan saboda bata so yasa rai yazo ya zube….Abinda bata sani ba kuwa shine tuni Dr Sa’adatu ta kirashi a waya ta sheda masa.

Abbah ya kasa ‘boye farin cikinsa Ya shedawa Najaatu samuwar cikin Halisan, murna ta dingayi da fad’in Ya kirata ya waya ya fad’a mata cewar ya samu labari tunda boye masa takeyi, Yace.”Kyaleta ai zamu koma ne sai naji hujjarta na ‘boye min kyautar da Allah yayi min”

Najaatu na dariya tace”Watakila ko kunya takeji.” Yace “Wace irin kunya kuma? Halisa ba yarinya ba zataji kunyar fad’a min tana da ciki akwai manufarta na ‘boyewa.”

Tace”To Ubangiji Allah ya sauketa lafiya.” Ya amsa da amin ‘kasa-‘kasa yace”Kema tashi muje na sa miki na ‘yan tagwaye dan na lura kece zaki iya d’aukarsu saboda jarumtarki.”

Dariya take tana kallonsa ya ‘kankance idonsa had’e da kai hannunsa kan le’bunanta yana shafawa yace.”Da gaske nake wallahi duk cikin matana ba wai ina kushe kokarinsu ba har Halisan kin fita juriya da kokarin daukar lalurata.” Dan murmushi tayi tana masa wani sihirtaccan kallo tace”Bana so kana fasa min kai kana sawa kaina yana girma.” Yasa dariya da fad’in “Shikkenan tunda bakya so na yaba bajintarki sai nayi shuru da bakina.” Kasa ‘kasa tace”Ai baka iya shuru ka dinga sambatu kenan jiya ma har kuka sai da naji kana yi.” Cike da mamaki

Ya bud’e baki yana kallonta.Ta fashe da dariya tana nuna shi da hannu, fuska ya ‘bata yace.”Ke nifa duk yanayin da nake ciki bana shashancin nan sharri kawai kikayi min.” Dariya ta dinga kyalkyala masa tace”Habawa ai duk abinda kake yi ina jinka sai dai kawai na kalleka.” Murmushi yay yana girgiza kansa yace”To naji ina sambatu amma bana kuka saboda haka abar maganar.” Ta gyara fuskarta tare da fad’in “To shikkenan an bar maganar amma tunda kace baka kuka yau sai nasa kayi.” 

Yace”Haka kika ce dai.” Hannunsa ta ri’ke tana masa kallon k’asan ido tace “Tashi muje to.” Mi’kewa yay kamar ra’kumi da akala yabi bayanta.

*Lol Bazance komai ba ku ‘kiyasta abinda zai faru????*

*Nono Hallita ne akwai matan da suke dashi har yaso yayi musu yawa, akwai kuma wa’inda suke dashi daidai misali, sannan akwai wa’inda zaku ga nasu cibir cibir su kansu baya cika musu hannu! To dan Allah duk wacce take da irin wannan hallitar ta nutsu kada ta tayar da hankalinta akan haukan shaye shayen maganin da dole sai sun girma wallahi zaki bawa kanki wahala dan ko sun girma kika haihu yaro na tsotsa sai yamutse idan kinyi yaye ya dawo kamar silifas shaye shayen maganin karin nono beda amfani mutukar bana hausa bane kiyi hattara kada garin neman gira ki rasa ido, nononki ba zai tashi lalacewa ba sai kin haihu kinyi yaye sannan zakisha mamaki!*

*Masu tambaya ta meye maganin girman nono na hausa ga wannan a saukake. Ki samu ‘ya’yan hulba kina had’iyar bakwai da safe bakwai da yamma….Sannan kina dama garin hulbar da madara kina sha sau biyu a rana, insha Allahu ba nonowanki kawai ne zasu girma ba har sharf din’ki zai sake bud’ewa sannan zakiyi ki’ba ki murmure hulba tana magani sosai…….

*MADADI*

******87 Rayuwar aure mai tsafta suke gudanarwa a k’asar saudia sannan kuma kusan kullum suna harami suna kad’aita kansu ga Allah anan suke yinu sai daf da magariba suke komawa masaukinsu, cikin satikan da sukayi a ‘kasar ita dashi sunyi wani freesh kana ganinsu kaga ma’aurantar dake mutukar kaunar junansu sosai suke kula da junansu tare da rokon Allah ya dawwamar musu da zaman lafiya a zamantakewar auransu.

Abbah yayi wa iyalinsa tsaraba sosai mussaman Zainab da kullum cikin yi masa ‘korafi take a rana sai ta kira wayarsa sau uku tana tambayarsa yaushe zai dawo kasuwa suka shiga domun siye siyen daba’a rasa ba, Najaatu ganin kamar yafi d’aukarwa Zainab abu yasa taji rashin dadi a zuciyarta tace”Ita aunty Halisan ba mutum bace kenan.”? yana duba wata abaya yace.” saboda me kika fadi haka.”? Tabe baki tayi tace”Naga Zainab kakewa siyayya ita kadai.” shuru yay na minti biyu yace.” A gabanki fa take damuna da kiran waya akan sautun da ta bani itama Halisan wanda take bukata na siya mata.

Shuru tayi masa tayi gaba tana dube dube ta lura kamar tsoron Zainab din yake dan watarana idan ta kira wayarsa fakar idonta yake yaje ya la’be a wani gurun ya jima yana waya sai ya shigo ya dinga wani muzurai.

Tana kallonsa sai da ya daukar mata dogwayen riguna manya guda biyar ga kayan kwalliya da takalma hade da fashion masu kyau da tsada…..Sai bayan ya gama yace mata wai ta dubawa su Saddiqa kayan da suka dace, sharesa tayi ta cigaba da duba abunda take bukata , gefan gold ta nufa ta tsaya tana dubasu gasu nan reras a cikin glass wannan yana wane wannan, wani abu ta latsa gurin ya bude! Wasu guda biyu tagani masu iri d’aya set ne a cikin akwatinsu wato sar’ka da d’ankunne sai zobe guda biyu acikin ko wane akwati, ita da Halisa ta daukarwa duk da ta duba kudin sar’kar ta gani hakan be dameta ba, sai ya siya musu tunda ita Zainab nada ita……sosai tayiwa su Saddiqa siyayyar data dace aka had’a kayan guri guda kafin ayi total Abbah ba tare da damuwar komai ba ya biya kudin da’aka cajeshi, yaran dake gurin suka sa musu kayan a mota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button