MADADI Page 111 to 120 (The End)

*MADADI!*
******89 Najaatu zubawa Munira ido kawai tayi tana kallonta sai kuka takeyi ta kasa cewa komai gashi ta matse yaro a jikinta yana ta kuka gami da son zuwa gurin uwarsa ta ri’keshi tsam a jikinta taki sakinsa.
Kawai sai taji itama zuciyarta ta karye hawaye suka shiga zubowa daga idonta……Sun jima cikin wannan yanayi kafin Munira ta sassauta kukan da takeyi tasa hannu ta goge hawayen fuskarta ta d’ago fuskar Daddy ta tsira masa ido sai kawai wasu hawayen suka sake kwace mata…..Najaatu a sanyaye tace”Haba Munira wannan kukan da kikeyi ya isa haka dan Allah ki daina komai kikaga ya faru dama can rubutaccene daga Allah.
Munira murya na rawa tace”Najaatu dole nayi kuka domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda zuciyata hakika nayi nadamar rayuwa nayi dana sanin abinda na aikata hakika na cutar dake gashi da yake baki da hakki Allah ya musanya miki da alkairi Najaatu rayuwata data iyayena ta zama abin tausayi da kyama kowa gudunmu yake dalili kenan da yasa muka tarkata kayanmu muka koma kauyen zaria da zama, yanzu haka acan muke rayuwarmu, Mommy itace ta bani umarnin zuwa na sameki domin neman afuwarki abisa abubuwan da suka faru a baya, kai tsaye gidan Alhaji na sauka Hajia tayi min kar’bar mutunci tasa aka kawo min abinci naci na koshi, Itace take sheda min haihuwar wannan yaron nayi mamaki sosai kuma alokacin naji sake jin tsoron Allah ya kama ni hakika Ubangiji babu yanda baya tsara lamarinsa tsorona Allah da Annabi yaron nan ya girma ya mallaki hankalin kansa ya samu labarin abunda ya faru a baya dole yayi mana kallon lalatattun iyaye marasa nagarta domin mun cutar da rayuwarsa tun kafin yazo duniya mun ruguza farin ciki gami jin dad’in rayuwarsa saboda son zuciyarmu wannan dalilin ne yasa ki kaga tunda na shigo nayi tozali dashi nake kuka saboda nasan mun riga munyiwa rayuwarsa illah.”
Najaatu shuru tayi tana tunanin abubuwan da suka wuce, ta goge k’wallar dake kokarin zubowa daga idonta tace”Munira a lokotan baya na dauki abunda ya faru da rayuwata na d’ora a matsayin kece sanadi sai daga baya kuma nagane cewa bake kadai keda laifi ba har dani dan da nabi umarnin iyayena ban kuma bi son zuciyata ba to na tabbata haka ba zata faruwa ba, to dukkaninmu muna aikata abune a duhu domin bamu san abinda Allah ya lullu’be ba, hakika aurana da ‘Dan uwanki kaddara ce da kuma tsananin rabo gashi nan a hannuki rabon Wannan yaron ne yasa duk abubuwan da suka faru a baya suka kasance saboda haka ki daina kuka da damuwa wallahi tuntuni na yafe miki kuma na tausayawa rayuwar da kuke ciki keda iyayenki ina rokon Ubangiji Allah ya sassauta muku……Munira a sanyaye ta amsa da ameen ameen Najaatu nagode sosai da karamcin ki kema inayi miki fatan alkairi a rayuwarki Allah kuma ya tabbatar da zaman lafiya a tsakaninki da mijinta.” Najaatu ta amsa da ameen ameen nagode kwarai da adduarki.” Falon yay shuru na minti uku kafin tace”Ina Muktar ina fata kunyi aure.”? Munira tayi wani irin murmushi kai kana ganinsa kasan na takaici ne tace”Najaatu Muktar ya yaudare ni ko kuma nace na cuci kaina na amince masa yana mu’amulanta ta kamar matar auransa sai da yayi min ciki tukkuna yayi min korar kare tare dayi min gargadi da cewar naje na nemi uban d’ana sannan kuma idan na sake na sake zuwa nace cikina nasa ne sai ya d’aure ni, a takaice dai yanzu haka yaron dana haifa yana nan yay wayo shekaransa daya da wata hud’u.
Najaatu ta dinga girgiza kanta cikin alhini da damuwa tace” Munira kinga irin abinda nake fad’a miki ko? Yanzu meye ribar abinda kuka aikata keda muktar ashe kenan ba Daddy ne abin tausayi ba tunda shi kowa yasan sai da aka shafa fatiha aka haifeshi wannan yaron da kika haifa shine abin tausayi idan ya tashi yasan hanyar da akabi aka samar dashi dole ya shiga halin damuwa da tashin hankali.
Munira na kuka tace” Hakane maganarki Najaatu wallahi naso tun yaron na ciki ya mutu ko kuma na haifeshi babu rai, ke har fatan mutuwa nake wa kaina a lokacin dana nake da cikin amma duk hakan bata samu ba.”
“Ki daina wannan maganar Munira dan shi Ubangiji babu ruwansa saboda kune kuka sa’bawa dokokinsa ba yaro ba Allah na iya raya shi kodan ya nuna muku ishara daku da masu irin halin ku.” Amma yana da kyau ki sake neman Muktar din idan da hali ki kaishi koton musulunci.”
Munira girgiza kai tayi tace”A’ina zanga Muktar? yau watansa uku da aure yana can legos tare matarsa amma kowa yaga Ahmad yasan d’ansa ne saboda suna kama sosai.
Najaatu tace”Kin sanya masa suna mai ma’ana kuwa to Ubangiji Allah ya raya shi tafarkin addinin musulunci Allah kuma ya karkato da hankalin mahaifinsa kansa yazo ya dube shi da idon rahama.” A sanyaye munira ta amsa da ameen ya Allah…….Haka suka kasance har yamma suna hirar yaushe gamo gami da jajantawa junansu, Najaatu ganin biyar ta wuce yasa ta shiga kicin domin d’ora girki duk da ba itake da girki ba a ranar watarana idan yazo yakan ci abinci a gurinta kafin ya tafi………Munira ta dinga sha’awar gidan Najaatu tana ta ‘kiyasta abubuwa da yawa a zuciyarta hakika Allah ya musanyawa k’awarta da nagartaccan miji irin wanda yake da wahalar samu a duniya tana rokon Allah ya bata kwatankacinsa.
Najaatu wanka tayi ta kintsa jikinta tsaf ta fito falon ta zauna suna hira kafin lokacin sallar magariba yayi………Bayan sunyi sallar ishai sai suka ci abinci tare, bayan sun gama Najaatu tace yana da kyau tayi wanka ko taji dadin jikinta, wani bedroom ta bude mata tace ta shiga akwai komai na bukata a ciki, a cikin kayan sawarta ta daukar mata riga da zani na atamfa ta kai mata dakin ta ajiye mata kan gado, ta fito ta zauna kan kujera tana sa’ke sa’ke gaskiya bata kaunar zaman Munira a gidanta saboda hausawa nacewa ruwan da ya dake ka shine ruwa Tsoron wani abu takeyi gashi tana jin nauyin tace mata ta koma gidan hajia ta kwana a can.
Tana can cikin tunanin mafita Munira ta fito cikin atamfar data ajiye mata, Najaatu saurin gyara fuskarta tayi tana kallonta har ta karaso kusa da ita ta zauna, a sanyaye tace”Najaatu da zan samu aikin aikatau dana zauna nayi na tara kudi kafin na tafi.”
Gabanta ne ya fad’i jin abinda Munirar ke fad’a! Tace” A gaskiya da kamar wuya ki sami aikatau anan area ki bari zan baki jari idan zaki tafi sai kije can ki kama sanaa har Allah ya fito miki da mijin aure….Munira tace”Nagode sosai Najaatu hakika ina alfaharin kasancewar ki a matsayin aminiyata Allah ya ‘kara miki rufin asiri da wadata.”
A hankali ta amsa da amin gefe guda tana nazarin maganarta shin wai har kwana nawa za tayi mata a gida itafa Munira tsoro take bata bata bukatar zamanta a gidanta to amma yanda za tayi ta fad’a mata ne bata sani ba …..Hira sukeyi sama sama Munira na sake bata labarin irin wuyar da tasha a hannun kanwar mamanta, ita dai jinta kawai take tana tunanin mafita.
Cikin wannan yanayi ya shigo gidan, Najaatu ta miqe da sauri tana masa barka da zuwa. ………. Amsawa yayi ya tsaya yana kallon Munira da fad’in “Bakuwa kikayi ne.”?
Munira ta zube har kasa tana gaisheshi, Yace.” Wannan fuskar kamar na santa.”? Munira sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, Ita kuwa Najaatu a cunkushe tace”Kawata ce Munira ‘kanwar Marigayi.” Yayi jim yana kallonta kafin yace “Tazo ganin Daddy kenan.”? ” Umm.” Tace ba tare data kalleshi ba babban burinta ya bar gurin dan ita ba taga amfanin tsayuwarsa a gurin ba.