MADADI Page 111 to 120 (The End)

Shi kuwa gyara tsayuwa yay ba tare da wata Manufa ba yace.”Munira ina mutanan gida ina fatan duk kuna nan lafiya.” Tace.”Kowa lafiya Abbah suna gaisheku da kyau.” Yace.”Muna amsawa .” yana gama maganar ya wuce ciki, Najaatu ajiyar zuciya ta sauke minti biyu tabi bayansa, Yana zaune a gefan gado ta shiga dakin, zama tayi a nutse ta gaisheshi tare da tambayarsa yanayin kasuwa, yace komai alhamdullih….Shuru dakin yay kafin yace.”Naji dadin zuwan Munira ko babu komai sun nuna damuwarsu akan yaron dan dama abin yana damuna ganin daga b’angaransu babu wanda ya ta’ba zuwa da sunanan yazo ganin yaron amma zuwanta ya nuna mana cewar sun san da zaman yaro a hannuki.”
Babu cikakkiyar walwala a tare da ita tace”Munira ba ganin yaro tazo ba hasalima bata san dashi ba sai da hajia ta sheda mata ita dai kawai tazo neman gafara akan abubuwan da suka faru.
Yace.”Allah sarki ai sai ki yafe musu tunda sun gane kuskuransu ko babu komai kun had’u tunda ga Daddy nan a tsakaninku sai suci albarkacinsa……Shuru tayi tana kokarin mayar da kwallar idonta, Ya kalli agogon hannunsa tare da fadin”Yau me kika girka.”
“Abinci ne mai sauki dan zuwan Munira yasa ban shiga kicin da wuri ba…jollop din macaroni nayi.” Girgiza kansa yay yace.”Bana jin zan iya ci.” Ta kalleshi tare da son tayi masa tambayar da ta jima a cikin zuciyarta ” Wai don Allah me yasa baka son cin abincin su Halisa da girkina da banawa ba sai kazo kaci abinci.
Yace.” Babu wani dalili kawai dai inajin dadin duk abinda zai fito daga gurinki sannan kuma suma ba abincinsu ne bana ci ba, ina ci daidai gwargwado amma dai duk kin fisu iya girki shine dalilin daya sa nake so naci naki.” girgiza kanta tayi tace”To yanzu da a guri guda muke haka zaka dinga yi kenan kasan rigima za’ayi.
Yace.”Saboda me.’? kai tsaye tace”Saboda wannan dalilin ba kowace macace zata yarda ba dan Allah ka dinga kamanta adalci Abbah bana so ranar Lahira ka tashi da shanyayyan jiki.”
Shuru yayi yana tunanin maganarta kafin yace.” Dan nazo gidanki kin bani abinci naci hakan ba zai sanya ranar lahira Allah ya tuhume ni ba, nasan akan abinda kike cewa nayi adalci sabida ina neman ki a lokotan da ba girkin ki ba shiyasa kike fadin cewa na dinga adalci to abincin ma na daina zuwa naci kamar yanda kika hanani kanki a lokacin da nake bukata.” Mi’kewa yayi ya kama hanyar fita da fad’in sai da safe ina fatan babu matsala.” Ta mike tana kallonsa sai wani Muzurai yake tace”Daga magana sai ka hasala bani na hanaka abinda kake magana akai ba wanda ya hallice kane yace kayi adalci a tsakanin matanka to me zai saka ka dinga d’aukar kwanan wannan kana kaiwa waccan.”!
Hannu ya d’aga mata a murtuke yace.”Kinga maganar ta isa haka ko kinga nazo miki da wata bukata ne.”? Da sauri ta girgixa kai Yace.”To kada ki sake kawo min hadisai akan wannan maganar.Tace.” Dama ai bani na fara maganar ba kaine.” Tsaki yaja ya kama hanyar fita, ta bishi da kallon mamaki! itakam bata san me yasa zuciyarsa ke saurin hasala ba kwana biyu tunda ta hanashi biyan bukatarsa a ranar da ba girkinta ba yake mata magana sama sama…….A nasa ‘bangaran kuwa haushi da takaici ne yake damunsa dan saboda yasan Zainab ba iyawa za tayi dashi ba, ita kuma Halisa ba cikakkiyar lafiya ba sam be ma fiye matsa mata ba dama Najaatun ce gwanarsa ita kuma ta kasa ta tsare tace bata yarda da wannan tsarin ba, idan ya gama kwana biyunsa a gurinta to haka yake shiga mugun yanayi a tsakanin kwanaki hud’un da zaiyi dasu Halisa ya galabaita mutuka abinka da wanda ya saba da sex duk sai ya fice daga hayaccinsa aikuwa ranar daya dawo gurinta tana raina kanta da farkon dare yayi asubah yayi da safe kafin ya fita kasuwa ma sai yayi, sai kace wani ayu!
Koda ta fito falon gani tayi yana sallama da Munira cikin sakin fuska kamar bashi ba yasa kai ya fita daga falon ba tare daya kalleta, danne damuwarta tayi ta zauna suka cigaba da hira da Munirar kafin dare ya shiga sukayi sallama kowa ya shiga daki domin kwanciya……..Wanka tayi kamar koda yaushe ta shirya cikin shirin kwanciya, wayarta ta dauka tana dube dube gabadaya bata cikin nutsuwarta na farko zaman Munira a gidanta ya tsaya mata a rai na biyu kuma wannan matsalar da take fuskanta a gurin maigidan nata, tasan yasan gaskiya amma yake takewa yanzu meye laifinta dan ta tunasar dashi abinda ya dace, ashe shi ‘kullatarta yayi a cikin zuciyarsa gaskiya al’amarin ya bata mamaki sosai………..Washe gari da safe da yazo take fad’a masa bukatarta naso ya bata kudi zata taimakawa da Munira idan zata tafi….Kai tsaye yace bashi dasu.” Ta saki bakinta tana kallonsa har ya gama abinda yake a dakin ya tafi….Da wannan takaicin ta yini dan har sai da Munirar taso ta fahimci wani abun na faruwa……..Da daddare da yazo bai bukaci cin abincinta ba ita tayi masa tayi tare da fad’a masa abinda yake so ta dafa……….Yace.”A ‘koshe yake da zai tafi ta dakatar dashi tare da fadin tana so tayi magana dashi, yace sai dai ta bari sai da safe dan yanzu sauri yake…..Koda ta fito falo samunsa tayi yana magana da Munira tana fad’a masa cewar gobe zata tafi da safe. Yace.”To kada ki tafi sai nazo.” Najaatu gabanta ya dinga bugawa ta tsirawa bayansa ido har ya fita daga falon, kasa zama a falon tayi ta shiga daki ta kwanta, to itama Munirar ganin matar gidan na cikin damuwa yasa ta kashe tv taje ta kwanta…..Najaatu kasa hakuri tayi ta dauki wayarta ta kirasa, ya dauka sama sama take jin muryarsa.”
Hawaye ta share tana kokarin aro dauriya tace”Da kace kada ta tafi sai ta jira ka me za kayi mata idan sonta kake sai ka fad’a min ni zan baka goyon baya.”
Murmushi yayi dan ya bata haushi yace.”Ai ba raham bane dan nace ina sonta nace kada ta tafi sabida akwai sirri a tsakanina da ita.” Sai kawai ya kashe wayarsa yana murmushin jin dadi shi dai yana so yaga ana kishi a kansa, Halisa ta gama yanzu Zainab da Najaatu ne keyi aure sai ya cikashe hud’u idan ma zasu hakura su hakura…..Najaatu ta dinga jin kamar taje dakin Munirar ta tuhumeta abinda ke tsakaninta da mijinta sai dai ta daure ta dinga nanata kalmar innalilihi wa’ina ilaihi raji”un. Da kyar bacci ya dauketa……Da safe Munira kasa gane kanta tayi sai tasha jinin jikinta tayi sanyi ta dinga Allah Allah maigidan ya shigo ya sallameta ta tafi dan ta lura zamanta a gidan na nema ya haifar da matsala.
Cikin galleliyar shaddarsa (wagambari) ya shigo gidan yay kyau har ya gaji kana kallonsa zaka gane bai da damuwa dan har wani ‘kiba da haske ya ‘kara matsalarsa kawai rashin samun abunda yake so ranakun kwanan Halisa da Zainab, kamshin turaransa ya cika falon….Munira ta gaishe shi tana sunkuyar da kanta wani abu take rayawa a ranta, inama inama! sake dago fuskarta tayi ta kalleshi tay saurin sunkuyar da kanta kasa tabbas ruwa ba sa’an kwando bane….Yace.”Ina matar gidan take ta barki ke daya a falo.”tace”Tana ciki bata fito ba.” Kai tsaye dakinta ya nufa…….Najaatu na sane tasa k’ananun kayan da suka matseta wando iya gwiwa da rigar da bata rufe mata cibiya ba, kayan sun mata kyau sosai kuma dole su rikita wanda akayi dominsa……..Ganin irin shigar dake jikinta yasa ya tsaya daga bakin kofa sabida tsaro, kallonsa tayi tace”Ina kwana.”? Cikin basarwa ya amsa, yana wani kauda kansa, Yace ina fata baku da wata matsala ko.”?