MADADI Page 111 to 120 (The End)

”Uhm.” tace tare da mi’kewa yay saurin dauke kansa xuwa tayi ta gifta shi, kofa ta bude ta fita ta barshi a tsaye a dakin….Gabadaya ji yay gwiwarsa tayi sanyi anya kuwa zai iya wannan ya’kin? daurewa yayi ya fita falon nan ya same su suna magana, Ya kalleta da fad’in Abunda yasa Nace ‘kawarki ta tsaya kada ta tafi sabida bukatarki da kika fad’a a kanta inaso naji abinda take bukata kafin na fita….Kamar tace masa kaida kake da sirri da ita kuma! sai ta share maganar tana dauke kai tace”Sana’a zata fara bata da jari shine nace ko zaka taimaka mata.” Da sauri yace.”Me zai hana muka taimakawa na waje ma ballantana na gida, insha Allah zan tura miki sai kuje tare idan kin cire ki bata, ya kalleta da fadin ” Munira Allah ya kiyaye hanya a gaishe da mutanan gida.” Munira tace”Zasuji insha Allah nagode sosai Abbah Allah ya raya zuria.” Ya amsa da amin hankalinsa a kan Najaatu dake ta faman dauke kanta har yanzu taki sakar masa fuska…..Shi kam jikinsa ne yayi sanyi sanin da yayi yau a gidanta yake fargabarsa kada dare yayi labari yasha bambam dan ya lura a fusace take, sasauta murya yayi yace.”Ni na tafi kasuwa.” Tace”Allah ya bada sa’a.” .Yana kokarin bude kofar falon ya amsa da amin ya rabbi
Abbah dubu dari cif ya bawa Munira Najaatu ta cire mata kudinta ta bata tare da kara mata dubu goma akai bayan sutturu da kayan kwalliyar data had’a mata, Hajia da baba talatu suka harhad’a mata kayayyaki masu yawa, Munira kasa daurewa tayi ta dinga kuka tana gode musu ashe dama Najaatu alkairi ce a garesu! Allah kenan, Dan Azimi ne ya dauketa a mota ita da kayan ta domun kaita can kyauyen nasu.
*BAYAN WATA UKU*
Salim yaji sauki sosai sai dai kullum yana gida babu abunyi sai yamma tayi yake fita ya zauna a cikin abokansa marasa sana’a! Mahaifinsa ya yanke shawarar siya masa adaidaita sahu ya fara ja domin zaman hakan bashi da amfani, koda Sakina ta sheda masa maganar farin ciki yayi domin shima zaman ya isheshi, yanzu yana jiran dawowar mahaifin nasa daga tafiya tunda yace idan ya dawo zasuje gurin siyar da napep din tare.
Abbah Abbas a nutse ya kalli ‘yar uwarsa yace.”Bana jin dadin ganin Salim a zaune a bakin titi babu babu abinyi kullum idan zan shigo unguwar nan sai na ganshi a zaune wannan dalilin yasa na yanke bud’e masa gurin gurin siyar da takalma anan bakin titin unguwar taku nasan ba za’a rasa shaguna ba, dan haka zan nemeshi akan maganar idan yaso sai ya fara bunkicen gurin zama.
Yaya Ramlatu fashewa tayi da kuka tace” Hakika dan uwana Bani da abinda zance maka sai dai na roki Allah yasa ka gama da duniya lafiya nagode sosai da wannan karamcin naka, dama shekaran jiya yazo yana fada min cewar mahaifinsa yay masa alkawarin zai siya masa adaidata sahu to kuma sai gashi kazo da wannan maganar .”
Yace.”Ai ba wani abu bane idan ya siya masa adaidata sahun zai iya hada kasuwanci biyu.” Hajia tace”Hakane kam kaima kayi zumunci Allah ya saka da alkairi.” Amsawa yay da amin amin kana yayi musu sallama ya tafi gurin iyalinshi…….Ya Ramlatu a waya ta kira Salim ta sheda masa maganar a ranar Salim da kyar ya iya bacci sabida murna da farin ciki hakika bai ta’ba ganin mutum mai kyakkyawar zuciya irin Kawun sa ba…….
*BA HARAM BANE!!*
*****90 Cikin sati biyu kacal komai ya kammala Abbah yasa an zubawa Salim kaya a k’aton shagonsa takalma na manya da yara maza da mata, Salim tsabar farin ciki har hawaye sai da ya zubar Mahaifinsa kuwa har kasuwa yaje gurun Abbah Abbas din ya nuna masa farin cikinsa dangane da alkairin da yayi masa ya dinga godiya kamar wanda aka bashi kyautar kujerar makka……Abbah Abbas dakatar dashi yayi yace masa dan yayiwa Salim abu bai kamata yazo yana masa godiya ba saboda a har yanzu a matsayin uba yake a gurinsa dan haka ya daina masa godiya akan abinda yayi.” Ayuba ya dinga jinjina nagartarsa tabbas a yanzu samun mutune masu yin abu domin Allah irinsa sai an tona babu shakka Alhaji Abbas yana kokarin aikata aikin alkairi da tarin dukiyar da Allah ya bashi.
*BAYAN WATA BIYU*
Al’amura na tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali, a zamantakewar gidan Abbah an samu daidaito ta kowane bangare yana kokarin ganin ya sauke hakkin dake kansa, shiyasa suma matan suka samu nutsuwa tunda ko wacce yana yi mata abinda take bukata, sai suyi wata da watanni basu had’u da junansu ba mutukar ba wani taro akeyi a ‘bangaran maigidan nasu ba, to nan ma idan sun had’u su ukun suna gaisawar mutunci suna kokarin danne kishi a tsakaninsu, wannan nutsuwar daya samu ne yasa hankalinsa ya kwanta harkokin kasuwancinsa suka cigaba da bun’kasa, arziki da wadata sai nunnkuwa suke sai dai godiyar Allah……….Cikin Halisa nada wata shida Najaatu ta harbu, to da yake cikin nata ba me laulayi bane yasa babu wanda ya san tana da ciki harshi maigidan shuru tayi masa bata fad’a masa ba, ta godewa Allah da yasa cikin ba mai wahala bane irin na Daddy, ashe jira yake ya k’ara kwari ya bayyana akanshi, kariris ta kwanta ciwo dan sabida rashin kwarin jikinta sai kiran Dr Saadatu yay a waya yace tazo gidan ta dubata,
Dr Saadatu kallo daya tayi mata ta gane abinda ke faruwa amma sabida ta tabbatar yasa tayi mata gwaje gwaje result ya fito tana murmushi ta fad’a masa cewar ciki ne da ita na wata uku, Abbah Abbas kasa ‘boye farin cikinsa yayi godiya yake mata kamar itace ta bashi kyautar cikin kyauta yayi mata ta mussaman kamar koda yaushe.
Najaatu ta dinga mamakin irin murnar da yake kamar wanda ba’a ta’ba yi masa haihuwa ba, a ranar yini yayi tare da ita ya’ki zuwa kasuwa, sai yamma ya fita….koda yaje gidan Alhaji kasa shuru yay sai da ya fad’awa hajia itama ta dinga farin ciki tana addua Allah ya raba lafiya………..kasancewar ranar ba girkinta bane yasa ya roki alfarma gurun ‘yar uwarsa akan taje ta zauna da ita, Yaya Ramlatu ta shirya kayanta tsaf ta tafi gidan, Najaatu taji dad’in zuwanta dama tana ta tunanin yanda za’ayi ta kwana ita kadai a gidan.
‘Bangaran Salim da Salimat kuwa sun sake daidaita kansu a karo na biyu yanzu tsarkakken aure suke so suyi Salim yini yake a shagonsa na siyar da takalma da daddare kuma ya dauki a daidata sahun sa ya tafi aiki, cikin kankani lokaci ya had’a kudin aure! Mahaifinsa da d’an uwansa sune suka je har gidan su Salimat din domin nema masa a auranta a karo na biyu, Naburago da Kanin babansa su suka kar’bi kudin auran da sadakin kana suka tsayar da ranar daurin aure wata biyu masu zuwa…….
To duk abunda ke faruwa Zainab bata da labari Halisa ce kawai tasan Najaatu nada ciki itama bashi ne ya fad’a mata ba a bakin Yaya Ramlatu taji a lokacin da tazo dubata, taji takaicin abunda yayi mata meye a ciki dan ya fada mata najaatu nada a ciki ita a yanzu daga Najaatun har Zainab din bata daukesu a matsayin kishiyoyinta ba a matsayin ‘kannenta ta daukesu, koda ta nuna masa b’acin ranta hakuri ya bata yace mantawa yayi, be fada mata ba, A nasa bangaran kuwa yana ganin rashin fad’ar shi yafi alkairi a gurinsa dan zai iya zuwa ya fad’a musu su mayar da abin kishi mussaman Zainab da ko maganar Najaatu bata so yayi idan yana gurinta shiyasa yake takatsantsan da al’amarin ko wacce dan baya so su dinga daukarsa a matsayin mutum mara adalci, Halisa Addua tayi akan Allah duk ya rabasu lafiya da abinda suke dauke dashi.