MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

*RANAR BIKIN SALIM*

Zainab da Halisa tare suka tafi gidan bikin ko wacce tayi ado daidai misali mussaman Zainab sarkin kwalliya komai na jikinta mai tsada ne ta shirya ‘yarta cikin ‘yan kanti masu kyau, Halisa cikin atamfa super ta shirya tayi amfani da gold d’inta irin na Najaatu to da yake hijabi tasa shine dalilin daya sa Zainab bata gani ba, gabad’ayasu harsu Saddiqa direba ya daukesu a mota gidan Alhaji ake taron bikin kafin yamma suje suga dakin amarya.

Lokacin da suka shiga Zainab sai da ta kusa fad’uwa ganin Najaatu a hakimce akan kujera tayi wani ‘bul ‘bul kana ganinta kaga mai yaron ciki fuskarta sai sheki take annuri yana sauka, tayi kyau har ta gaji tana sanye da Material pink color mai wani irin kyalli da duwatsu, tunda suka shiga falon Zainab ta kasa dauke idonta daga kanta, Uban gold din da taga ni a wuyanta shine yayi masifar tayar mata da hankali, tsabar hassada yasa taji hawaye na kokarin kufce mata, ‘kasa tayi da kanta tana kokarin daidata nutsuwarta kada jamaar dake gurin su gane halin da take ciki.

 Sai da ta daidata nutsuwarta tukkuna ta d’ago kanta tana ya’ke ta shiga gaishe da Hajia da jamaar dake gurin…….Najaatu janyo hannun Ummi tayi tana mata wasa yarinyar ta bata sha’awa sosai ganin yanda mamanta tayi mata gayu tana kaunar ‘ya mace a rayuwarta…Zainab dik irin kulawar da Najaatu takeyi akan ‘yarta hakan be burgeta ba harararta ma takeyi a fakaice k’yashi da bakin ciki duk ya cika mata zuciyarta…………..Halisa kuwa da yake tayi sabo da dangin mijin nasu tana cikinsu suna ta hira Hajiya Rakiya tace” Yanzu kuma idan an gama wannan taron sai na haihuwarki dan banyi tunanin ma zaki zo taron bikin nan ba ganin yanda cikin ki ya tsufa.”

Halisa tace” Lallai kuwa ni kam ko na haihu babu taro sai dai ku bari idan k’anwata ta haihu sai kuyi ni na girma da taron suna.

Hajia Rakiya tace”To ashe bake kadai ce mai cikin ba…..Najaatu tayi saurin sunkuyar da kanta tana jin kunya, Hajia Rakiya dariya tasa ganin yanda Najaatu ke sunkuyar da kanta tace”Allah to ya rabaku lafiya…..Zainab gumi ne ya shiga tsatstsafo mata lallai ma! Najaatu nada ciki ita tana zaune tabdijam! hankalinta ne ya tashi taji gabadaya zaman gidan ya isheta, daurewa kawai tayi la’asar tayi ta kalli Halisa tace”Ni ina ganin tafiya zanyi tunda kinga ni zanyi girki.” Halisa tace ba zaki tsaya muje muga dakin amarya ba.

Girzgiza kai tayi tana gyarawa ‘yarta takalmi tace”Watarana naje.” Najaatu ta ri’ke hannun Ummi da fad’in “Zainab ki bani ita ta kwana biyu mana.”

Girgiza kanta tayi babu kunya tace”Ba zan iya ba.”

Gabadaya mutanan dake falon suka zuba mata ido da mamaki a tare dasu….Ya Ramlatu tace”Kafin ki haifa ita ta haifa gashin nan ma wani cikin ne da ita kije ki rike ‘yarki haba jamaa ni ban ta’ba ganin mara kawaici irin wannan yarinyar ba wallahi.” Zainab tayi kwal kwal da ido tana so tayi kuka, Ya Ramlatu ta dinga farfada mata magana, hajia Rakiya ganin abun na nema ya zama rigima yasa ta dakatar da Yaya Ramlatu daga hayaniyar da take.

Zainab sama ta hau tayiwa Hajia sallama ta sakko babu wanda ta kula a cikinsu taja hannun ‘yarta suka fita…..Abinka da taron mata tana fita kowa ya shiga fad’in albarkacin bakinsa a kanta.

Zainab sai da taci kukanta ta koshi tukkuna ta dauki waya ta kirasa, Abbah jin yanda take sheshshekar kuka yasa hankalinsa ya tashi yace.”Tayi shuru tayi masa bayanin abinda ke faruwa, ‘ki tayi tace”Ita dai yazo gida bata da lafiya….Jin maganar rashin lafiyasa yasa ya bar abinda yake ya tafi gidan nasa 

A falo ya sameta ta had’a kai da gwiwa abun duniya ya isheta Najaatu nada ciki Halisa nada ciki sannan sun had’e mata kai sunsa gold iri daya ita bata dashi bayan nan kuma Yaya Ramlatu ta tsaneta taci mata mutunci tare da zagin iyayenta, wannan abubuwan sune suka dameta suka tsaya mata a wuya.

Da kyar ya rarrasheta ta shiga shirya masa karya da gaskiya tana kuka take fada masa Yaya Ramlatu ta tara Jama’a taci mata mutunci tare da zagin iyayenta akan wani dalili wanda bai taka kara ya karya ba, Abbah yaji ransa ya ‘baci amma baiyi saurin yanke hukunci ba sai da yace ta fada masa dalili…..Tace” Saboda kawai na ‘kar’bi Ummi a hannun Najaatu shikkenan sai cin mutunci ya biyo baya wai nayiwa Najaatu gorin haihuwa kafin na haifa ita ta haifa gashinan zata sake haihuwar wani gabad”ayansu haka suka dinga cin mutuncina akan rashin gaskiya…….Yace”Kiyi hakuri zanji dalilin daya sa suka tozarki a gaban jamaa taro idan na Ramlatu ne ki daina zuwa tunda bakwa jituwa da juna ita kuma Najaatu data bada goyon bayan aciki mutuncinki zanji dalili! ni kike aure ba wani ba saboda haka taro kin daina zuwa tunda ba alkairi suke shukawa ba! Tace” sannan kuma Naga gold aunty Halisa da Najaatu sun sa iri d’aya ni ina nawa.”

Gabansa ne ya fad’i! kai Zainab rigimammiya ce tabbas gold din nan ne da Najaatu ta siyo musu lokacin da sukaje umara ta gani, domin ya wanke kansa daga zarginta yace”Najaatu ce ta daukar musu su biyu kema zan baki kudi kwatankwacin na gold din ki siya.” Tana kuka tace”Ni wallahi irin nasu nake so me yasa bakya ce ta d’aukar min ba kaga irin rashin adalcin naka ko wannan uban gold din

ai bai zama lallai a samu irinsa anan ba.” Yace.”To shikkenan ki bari idan munje tare sai ki siya dama farkon azimi nake so na sake tafiya zamuje tare insha Allah.” Shuru tayi tana goge fuska yace”Ina fata dai babu wanda kikayi wa rashin kunya acikin mutanan dake gurin.” 

“Babu wanda nayi wa magana ai ganin sun had’e min kai suna cin mutuncina yasa nacewa aunt Halisa zan dawo gida.” Yace.”Ita Halisan tana zaune ake zagin ki ba tayi magana ba.”? 

“Eh ba tace komai ba har na fito daga gidan.” Abbah ya jima kansa a kasa yana nazarin al’amarin tabbas idan yay binkice ya tabbatar da gaskiya lamari to babu shakka Halisa da Najaatu sai sun raina kansu wato har dasu za’a hadu a ciwa matarsa mutunci ya rasa me yasa tsakanin Yaya Ramlatu da Zainab basa shiri…………A ranar beje gidan ba saboda yasan cike yake da jamaa zamansa yay tare da Zainab din tana ta kalallameshi da kalamai sai ‘kara rura wutar al’amarin take……Bayan ya dawo daga sallar ishai gurin Halisa ya wuce yaga bata dawo ba, rai a bace ya kirata a waya lokacin suna gidan Salim suna kar’bar amarya tunda sune iyaye.” Hayaniya yasa ta fita daga cikin Jamaa ko kafin tace komai taji yana magana a fusace! Tace”Yi hakuri Abban Mufida na rana d’aya dai ai ka d’aga mana k’afa yanzu haka ma muna gidan amarya nida Najaatu.” Yace.”Dole sai daku za’a kar’bi amaryar kinfi kowa sanin bana son kuyi dare a waje sabida haka dake da ita Najaatu ina son ganinku a gida dan tun la’asar na dawo naji kuma dukkanin irin rashin arzikin da kukayi.”

Halisa na kokarin tayi magana ya katseta da fadin”Ina jiranku yanzu yanzu.” Kashe wayarsa yayi ya ajiye gefe ya cigaba da girgiza kafafunsa, Zainab duk wasu matakan kare kanta ta tanade su tana jiran suzo ayi wacce za’ayi.

Halisa Najaatu taja gefe ta fad’a mata abinda ke faruwa, dukkaninsu jikinsu yayi sanyi da kiran gaggawar da mijin nasu yake musu…….Halisa na draving tace”Najaatu anya ba Zainab ce taje masa da wani sharrin ba.” ? Cikin rashin damuwa tace”Idan taje masa da sharri kanta zai koma insha Allahu mu dai babu abinda mukayi mata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button