MADADI Page 81 to 90

“Halisa bana gari a halin yanzu ku kwantar da hankalinku dukkanin abinda ya faru da sanin Ubangiji na samu labarin komai bayan tafiya ta jos wuta ta cinye d’aya daga cikin rumfunana to bana mamaki da ikon Ubangiji da kuma abinda ya saukar a kan dukiyata, kada ku manta shine ya bani ita lokacin da banyi tsammani ba, nasan idan yaga dama zai mayar min da abinda na rasa cikin lokaci kankani babban farin cikina wutar bata ta’ba kowa ba shine abinda yafi komai faranta min rai! Dukiya a duniya na sameta kuma anan zan tafi na barta to banga abin tashin hankali ba, kuma ba wai gabadaya abinda nake dashi ne ya ‘kone ba akwai kaya masu yawa a sauran rumfunana ina da kudi a banki wanda ban san yawansu ba to me zai sanya na kasa tawakalli dan Allah ya zartar da ikonsa, inaso dukkaninku ku kwantar da hankalinku kuyi addua akan Allah yasa haka shi yafi alkairi.”
Halisa jikinta yayi sanyi tace”To shikkenan gabad’ayanmu ma muna gidan Alhaji kowa hankalinsa ya tashi gashi babu wanda ka fad’awa inda kake sai da Salim ya dawo yake fad’a mana wai tun misalin biyu na rana ka tafi jos dauko Naja’atu.”
Yace.”Eh nayi haka ne saboda wani dalili nawa amma yanzu gamu a kan hanya nida Naja’atun insha Allah kafin gari ya waye zamu sauka.” Halisa a sanyaye tace”To Allah ya saukeku lafiya.” Ya amsa da ameen tare da kashe wayar tashi gabadaya.
Halisa a sanyaye ta shiga sanar dasu Hajia abinda yace mata Zainab ta cika ta batse sai haushi takeji kishi kamar ya kasheta, akan me zai tafi dauko Naja’atu ya bar iyalinsa ai bashi ne yake da alhakin daukota ba tunda iyayenta da dan uwanta suna raye shi meye nasa, zainab sosai take kishin naja’atu dan Halisa bata gabanta tunda lura kamar ta tashi daga aiki……..Naja’atu a sanyaye ta kalleshi tace”Abbah wani abu ya faru da kaine naji kamar kana maganar gobara.” Ba tare da ya kalleta ba yace.”Eh bayan na dauko hanya da niyyar zuwa nan sai al’amarin ya afku wuta ta cinye babbar rumfata dake cikin kasuwa.” Jikinta yayi sanyi sosai tace”Allah ya mayar maka da alkairi Abbah Allah ya sadaka da rabo mai amfani.” Yaji dadin adduarta sai ya amsa da “ameen ya Allah nagode sosai.” motar tayi shuru kowa na tunane tunane a cikin zuciyarsa, Abbah Abbas sosai yake gudu kan kwalta dan gabad’aya ba yaso su kwana a hanya dalilin da yasa kenan ya kashe dukkanin wayoyinsa ya mayar da hankalinsa guri guda…….Sai gefin asubahi suka shigo garin kano a lokacin Naja’atu ta dad’e dayin bacci dan da yaga tana gyangyad’i sai tsayar da motar ya umarceta da ta koma bayan motar ta kwanta, Lokacin da ake kokarin shiga massalaci domin gabatar da Sallah asubahi yayi parking din motarsa a kofar gidan mahaifinsa, Allah ya godewa kafin ya bude motar ya fito da sauri ya nufi masjid din dake jikin gidan Alhaji, yana kokarin shiga massalacin Baba malam shima na kokarin shiga, sai sukayiwa junansu sallama suka shiga massalacin a tare, baba malam ya wuce ciki shi kuma ya tsaya bakin famfo domin daura alwala…..Naja’atu tun bayan fitarsa a motar ta tashi zaune tana muzarai gami da kalle kallen jama’ar dake shiga massalaci a gaban idonta Baba malam ya fito daga gida ya shiga massalacin ta dinga jin faduwar gaba da wani irin tsoro gami da kunya da nadama na damunta yanzu da wane ido zata kalli iyayenta da sauran jama’ar gari?………………
*Littafin na kudi ne…..!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 idan katin waya zaki tura sai kiyi min mgn ta whasap da wannan number…… *07084653262 BINTA UMAR ABBALE*
64*********Ta jima zaune a cikin motar kafin ta yanke shawarar budewa ta fito a hankali tana waige waige, gidan alhaji ta nufa domin bata tunanin zata iya shiga gidansu dan bata san irin kar’bar da mahaifiyarta za tayi mata ba.
A sanyaye ta tura kofar palon hajia ta shiga da ‘yar karamar sallama a bakinta, shuru palon babu kowa sai dai tana d’an jin motsi gami da magana sama-sama a dakin data zauna kafin auranta da Bash, A sanyaye ta zauna kan kujera tana takure jikinta ta kai minti goma a zaune babu wanda ya fito hajia na sama su kuma su Halisa da yaran na cikin wannan d’akin babu wanda yasan da shigowarta, ganin gari ya soma haske yasa ta yanke shawarar miqewa domin taje tayi sallah….Dakin dasu Halisa suke ta nufa tana tafiya salau salau wanda kana ganinta zaka fahimci karfin hali kawai take yi…….A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama a bakinta, gabad’ayansu suka juyo suna kallonta, Mussadiq ya miqe a guje yaje ya rungumeta yana tsalle da murna had’e da kiran sunanta duk ya cikwikwiye mata hijabin jikinta
Mufida taje gurinta tana ta murna da farin ciki….Saddiqa kuwa tana zaune a inda take ba zaka tantance yanayin da take ciki ba….Naja’atu ta miqa mata hannu murya na rawa tace”Zo.” Saddiqa ta mayar da kwallar dake kokarin zubo mata ta miqe a nutse ta nufi inda take
Zeey dake bacci sakamakon ihun! da Mussadiq yayi yasa ta miqewa zaune tana ‘bata ranta, tana kokarin yin magana Halisa ta fito daga toilet sai kawai idanunta ya sauka akan Naja’atu dake tsaye a bakin kofa ta rungume yaran sai hawaye takeĀ
Halisa tace”Naja’atu dama ke suka gani suke wannan ihun? ni ina bandaki naji ihu ina addua Allah yasa ba fad’a suke ba ashe kece.” Tace.”Nice aunty Halisa ya kuke ina fatan na sameku lafiya.” Halisa babu yabo babu fallasa tace”Muna lafiya gabad’ayanmu.” Daga haka sai ta wuce ta dauki dadduma da hijabinta ta tayar da sallah…..Ita kuwa Zainab komawa tayi ta kwanta tana jan qaramin tsaki ita dai tana bala’in kishin Naja’atu mussaman yanda taga maigidanta gami da yaran sun damu ita.
Tace”To kuje ku zauna nayi alwala nayi sallah sai mu zauna mu sake gaisawa.”suka samu guri suka zazzauna suna kallonta ta nufi toilet sai murmushin jin dadi suke…..Mussadiq kasa hakuri yayi cike da farin ciki ya nufi gurun Zainab yana fad’in “Auntymu ki tashi ku gaisa ga Yaya Naja’atun ta dawo daga tafiyar da tayi.”
Zainab idanunta a rufe tace” Mussadiq bacci ne a idona idan na tashi a bacci zamu gaisa.” Yaron jikinsa yayi sanyi dan baiji dad’in abunba jiki a sanyaye yaje ya zauna kusa da ‘yan uwansa…….Ita kuwa Halisa bayan ta idar da sallar carbi ta shiga ja tana istigifari ga Allah(???? Su Halisa an musulunta an koma ga Allah to Allah ya kar’bi tuban ta damu baki daya)
Abbah Abbas da kyar ya samu kansa dan ana idar da sallah jama’a sukayi caaa! a kansa suna masa jajen dangane da qaddarar data fad’a masa a kasuwa kowa sai fad’ar albarkacin bakinsa yake, to shi dai magana d’aya yake fad’a cewa komai ya sameshi daga Allah ne yana rokon Allah ya kare dukkanin musulmi da mugun ji da gani…….Sai kusan bakwai da kwata ya samu ke’bewa dasu Alhaji nan ya tabbatar musu da cewar ya dauk’o Naja’atu daga inda take kuma tana cikin koshin lafiya kamar kowa sai dai maganar cikin jikinta ya sanya duk jikinsu yayi sanyi suka shiga cikin halin jimami daga bisani suka barwa Allah ikonsa domin kuwa duk abinda Allah ya zartar a kan bayinsa shine daidai, babu wanda yasan abinda Allah yake nufi dangane da faruwar al’amarin shiyasa gabadayansu sukayi wa yarinyar adduar sauka lafiya tare da adduar Allah ya inganta abinda zata haifa.