Noor Albi

NOOR ALBI 7

Ta bangaren Sa’adah tana Gama wankewa ciki tayo ta nufi dakin Momy data bar palon Takoma dakinta ta zauna bakin gado tareda dafe kanta dake tsananin Mata ciwo itama
Ta qaraso gurin momyn ta zauna gefenta tareda riqo dayan hannun momyn da idanuwanta sukai jajir itama idanuwanta suka ciko da hawayen tausayin momyn cikin tsananin kulawa da sanyin jiki tace”

Inshallah wata Rana Zaki komai ya wanke daga zuciyarki
Kici gaba da daurewa ahakan yafi kibar zuciyarki ta ri jayeki
karki Bari shedan yafi qarfinki,
Wata Rana zakiji zuciyarki ta saki gabaki daya
Amma Dan Allah Momy ki sassauta muku ku dukan sbd zuwa yanzu Babu Wanda baya cikin mawuyacin hali acikinku,
Abba lafiyarsa da rayuwarsa gabaki daya acikin jarabawa suke
Ta yanda ma ko yaso neman yafiyarki bazai iyaba Dan Allah Momy ki saki komai kibar rayuwarki tasamu salama da nutsuwarda kowace irin zuciya ke samu.
Na Miki alqawarin idan ganin Laylah ne damuwar daga ranar da nayi aure zanbar gidan Nan Zan tafi da ita bazata sake dawowa ba har sai ranarda zuciyarki ta samu aminci da ita wannan shine alqawarina agareki umma sbd bakisan iya qaddarar da Allah ya rubuto a tsakaninki da itaba Dan kuwa dagani har ita bakisan waye Zai zana gatankiba alokacinda tsufa ko ciwo ya riskeki,
Inaji ajikina Laylah zata zame Miki farin ciki abin alfahari Inshallah
Amma saikin bar zuciyarki ta amsa qaddarar da Allah yariga ya rubuto a tsakaninku wadda ta Dade da wucewa ki yadda cewa Laylah ‘ya ce daga wata uwar.

Ko motsawa momyn batayiba Dan kuwa sosai takejin nauyi Mai qarfi a zuciyarta,
Ita kanta tanason yayewa zuciyarta uqubar datake ciki Dan kuwa tsawon shekarun itama batayisu cikin farin cikiba ko kadan saidai Haka Allah ya halicceta da tata zuciyar riqon Mai qarfi.

Har tsakiyar dare Babu wani bayani daga asibiti sai zaman jiran tsammani da kowa keyi a dakinsa batareda kowannensu ya rintsa ba.

Laylah daqyar taga safiyar ta waye Mata tayi sallah hakanan ta fito tafara ayyukan Dake kanta batareda jikinta ya bayyanarda halinda zuciyarta take ciki ba,
Sa’adah da itama Bata cikin walwalar sbd tunanin Halinda Laylan take ciki da Abban danma takira abdullahi taji jikin Abban Wanda har lokacin Ba wani labari Mai Dadi
Tafito Dan Taya Laylah aiki sbd rage Mata damuwa duk da tasan Bata nunawa.

Ganin irin yanayin laylan na sanyi data qara yasata dauko wayarta takira Mata Abdullahi ta miqa Mata wayar cikin qarfin hali ta tambaya jikin Abban
Abdullahi ya tabbatar Mata da Abban Yana Raye saidai kam Yana kwance Babu wani Sauki saidai daga ubangiji.

Adduar samun lafiya Tai Masa ta miqawa Sa’adah wayar tana cewa”

Nagode anty Sa’adah.

Dafa kanta Sa’adah tayi tana cewa”

Kiyi kokari ki fitarda damuwarki zakiji sassauci cikin zuciyarki.

Wani irin murmushi kawai tayi tana cigaba da juye ruwan Lipton din data dafa acikin flask.

Itada anty Sa’adah yau sukai aikin abincin Rana kafin Anty Sa’adah din tasata tayi wanka tace ta shiryo suje asibitin.

Cikin sanyi ta shirya suka nufa asibiti a napep
Koda suka Isa Abdullahi bayanan yaje gida wanka da cin abinci ya Dan huta kafin yadawo Dan Haka su suka wuni a asibitin
Takasa dauke ido daga kan mahaifinta da cikin lokaci qanqani ciwo ya qarasa zabgesa Dan kuwa fuskarsa tuni Tayi wani irin rama Mai tsanani raunar da zuciyar duk wani Mai qaunarsa.

Anty Sa’adah ma zuru tayi ta zuba Masa nata idanuwan tanajin tausayin kanta da Babu shaquwa tsakaninta da mahaifinta Wanda Momy da ‘yan uwanta ke nesantata dashi sbd cusa Mata Jin zafinsa akan abinda yayiwa momyn saidai har ga Allah tasan akwai tsananin tausayi da qaunar mahaifinta cikin ranta,tana nesanta kanta dashi sbd karta qarawa momyn takaicinsu Abban da Laylah
Saidai Bata iya nesanta kanta da Laylah Dan lura da hakan shine abinda Abban yafi so da kauna
Ta zabi tasakasa farin ciki daga nesa ta hanyar bawa Laylah dukkanin kulawarta da qaunarta.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button