Noor Albi

NOOR ALBI 48

Mamuhgee 48_*
Cak ta tsaya gaban Laylah tareda mutuwar tsaye tana fiddo dukkanin girman idanuwanta afili tana kallon ciki dayake gaban Laylan,

Kallonta ta maida Kan Turaki da sauri Dan batada lokacin Anne ita ba yanzu ba,

Ganin yanda fuskarsa take a hade tsaf yasata maida kallonta Kan Laylah cikin wata muryar tashin hankali tace”

Laylah,ciki kikayi?
A Ina?
Waye yayi Miki?
Shiyasa ake mun boyo?Kokuwa kinada wata uwar data fini da baza’a sakani cikin masana ba.

Hawaye Laylah takeyi sosai takasa ko kwakwaran motsi sbd gabaki daya neman fita take hayyacinta sbd firgicen datake..

Hannu Ms Na’ima takai ta damqo hannunta tana cewa”

Muje can bangaren zamuyi magana a tsanake Dan kinada laifi Mai girma agurina,
Gabaki daya an sauyamin ke
Komaima Dake ake boyemin..

Bangare hannunta daga na Layla yayi zuwa Lokacin fuskarsa na bayyanarda bacin ransa sosai ya jata tana kokarin qwacewa bataji Bata gani idan ba Laylah aka Bata ba ta zaunar da ita sukai budaddiyar wasika Dan koma menene Laylah tasan komai,

Ita ba cikin jikin Laylah ya dameta ba Maganar wacece a rayuwar Turaki takeson ji
Dan akan hakan yau tafison ta cinnawa gidan wuta Har Turakin da ita su mutu hankalinta ya kwanta.

Haj Zinat ta fita tana waiwayen Laylah hankalinta tashe saidai itama takasa yadda da tunanin abinda suke gani da Wanda suke Shirin ji ma,

Bin bayansu Na’ima da Turakin tayi Bata daina waiwayeba har tana kifewa da sauri ta tashi tabi bayansu qafafunta na rawa….

Bakin Kofar bangaren Na’iman ya dakata tareda sake hannunta
fuska daure ya kalli gefenda Haj Zinat ta iso da sauri ta riqe Na’iman Kai Tsaye yace”

Ta zauna aciki idan ta fito ta tafi gurinta Zan dauka matakin hakan,
Ta dawo hankalinta wannan zallan rashin Kama Kaine ga masu aiki suna kallonta,
Ki nutsar da ita zaifi Mata mutunci..

Juyawa yayi yabar gurin sbd yasan duk hakurinsa da kamewarsa bazai iya tankwafar da Na’iman ba,
Sbd Bata ganin kowa idan tana rashin Jin ta,
zubar Masa ma da mutunci zatai a gaban securities da masu aikin gidansa idan ya biyewa tankwafar da ita din.

Yana barin gurin bangarensa ya nufa ya shige batareda ko waiwayensu yayi ba saidai yasan duk fashinsa da fadansa bazai Hana Na’ima tashin hankali ba idan tagama sanin ZAINAB da cikinta duka nasa ne Dan Haka Dole zai rabasu,
Bazasu zaunu guri dayaba,

Laylah tunda tazo bazata komaba saita haihu Dan Haka Na’iman zai tura Takoma Lagos kokuma US.

Da karfi fa yaji a haukace Haj Zinat ke janta tana kokarin qwacewa
Tayi ciki da ita suna Shiga babban palonta ta qwalawa siddika Kira da qarfi tana cewa”

Yi sauri saka key ki rufemin kofar ki zare keys din..

A rude da mamaki siddika ta qaraso ta dannawa kofar key tareda zaresu tayi saurin miqawa Haj Zinat din kafin Ms Na’iman tayo kanta.

Damqe keys din Haj Zinat tayi kafin ta saki Ms Na’iman cikin tashin hankali Mai girma da itama yau haukar takusa kamata ta nufi kujera ta zauna tana zare mayafinta tayi wurgi dashi,

Danwkalinta takuma zarewa ta jefar Kan kujera tana kallon siddika cikin tsawa tace”

Kawo Mana ruwa ko zuciyata zata dawo Kan aiki.

Kallon Na’ima Dake safa da marwa cikin masifar Dake cin koina jikinta tace”

Ki zauna wlh akawi babbar matsala Mai girma.,
Ke bama matsala bace wannan akwai masifa da bala’i masu girma a cikin wannan zancen…

Kasa zama Ms Na’ima tayi taci gaba da safa da marwa cikin masifa da takaicin Mai tsananin gaske tace”

Sai naci uwar Laylah,
Zan koya Mata darasi Mai girman gaske idan munkoma ta yanda bazata Kuma ya yarda a munafurceni da ita ba,

Banyimata riqon dazaisa taji Ina cutartaba Dan me zatamun mufurci,
Yanzu gashi Nan duk yanda nake kaffa kaffa Kar tayi saurayi Ashe ciki tayo ta rufeni baibai,

Har Anne da Turakin sun sani tunda sune jininta gashinan an daukota da saidai naga ‘dan shege a gidana,

Ni tsabar masifa da bala’i Banda Allah yayita asararrar duniya wlh data Bari nasan da cikin bazan Bari Turaki da Anne su saniba haifemun shi zatai taban nasamu magaji gurin Turakin tunda yanzu yasamu lafiya hakurinsa na haihuwa ya gaza Sai bin Mata yake….

Wallahi Laylah taci Amanata Kuma wlh zatasan bacin Raina baida kyau ko gaba ance tasake min irin Haka bazata kumaba……..

Ruwan da siddika takawo masu Dan sanyi Haj Zinat tagama shansu tayi wurgi da robar ruwan da sauran Dake ciki
Siddika tabi robar ta dauke tareda zuwa ta dauko abun gogewa…

Na’ima ki dawo hankalinki ki fuskanci gaskiyar da idonmu ya ganar Mana,
Idan Baki dawo hayyacinki Kika kalli komai a bude ba za’a cigaba da rufemu ne Muna bulayi cikin hauka…

Cikin jikin Laylah na waye?
Sbd kariyar danaga Turaki da Anne sun bayyanarda Shirin Bata ta gaske ce bana tunanin ‘ya zatai cikin shege ayi Shirin Bata wannan kariyar…..

Zama Ms Na’ima tayi a kujera tana yiwa Haj Zinat din wani kallo tace”

Bangane wannan bayanin ba…

Na’ima wlh nafara tunanin Mai cikin da muke nema Laylah ce,

Ranarda yace Miki karki kuskura ki Isa gidansa idan kin koma US,

Maganarsa ta tabbatarda abinda yake son hanaki Isa garesa Yana cikin gidansa kenan sbd tun aurenki dashi Bai taba hanaki tafiyaba ko wace irice sai lokacin,

Kuma muka kira Laylah Dan neman sanin abin dayake faruwa cikin gidan tabamu tabbacin Babu kowa a gidan bayan ita da Cindy…
Yanzu Kuma ga ciki a gaban idonmu mungani,

Gata Babu sanarwa yaje ya daukota mungani,

Gashi suna kokarin Bata kariya daga gareki,
Idan har tayi cikin shege da Bai shafeki ba meyesa za’a Bata kariya daga gareki bayan kece yakamata ki Bata kariya daga garesu sbd fusatar da zasuyi idan tayi cikin shege…….

Zuru Ms Na’ima tayiwa Zinat da Ido tana kallonta tamkar wuwuya,

Kiran sunanta Zinat tayi tana girgizata tace”

Kinaji kuwa???

Girgiza Kai Ms Na’ima tayi tana cire hannun Zinat din daga jikinta tana cewa”

So kike kicemun cikin Turaki ne a jikinta?

Da mamakin tambayar Zinat ke kallon Na’iman tace”

Bazaki bude qwaqwalwanki ki fahimta ba kenan…?

Sake girgiza Kai tayi tana dauke kallonta daga Zinat din tace”

Zancen ne bamai taba yiyuwaba,
TURAKI fa kikace da cikin jikinta?
Kinsan me kike fada kuwa?
Abbantane fa,
Aminin Mahaifinta daya hada auren uwarta da ubanta,

Tayaya kike kawo wannan rikitaccen bayanin?
‘yar uwarta dasuke uba ‘daya yake Aure shi Turakin idan kin manta,
Hakama tamkar ‘yar cikinmu muke riqonta,
Wannan tunanin babusa a cikin duniyar mutane..wallahi bazai yiyuba.

A rikice Zinat ke kallonta tace”

Abokin uba nawane yayi lalata da Yar abokinsa?
Qanwar Mata nawa ta kwana da mijin yayarta,
Hakama ke da kike kallonta matsayin ‘ya ta riqo wlh akwai ‘yayan dasuka kwana da mazajen uwayensu Mata da suka haifesu bare ke ‘yar riqo kike magana anan,

Yarinya kyakkyawar gaske da ita ga saka kayan banza anyhow
Tayaya kike mamakin hakan bazata iya faruwaba???

Cikin zafi ta katse Zinat din tana sake win yarda ko kunnuwanta suci gaba da Jin wannan balain Dan wlh bazai yiyuba,
Tashin duniyar Laylah da Turakin za’ayi idan Suka Bari shedan ya rude su sukai Mata wannan Cin amanar da Bata karbu ba,

Batason ko tunanin hakan na shiga kanta shiyasa ta katse zancen da cewa”

Kidaina kawo wannan tunanin wllhi ko dauka kaina bazai iya ba,
Buqa kaina kike neman Yi da wannan tunanin Dan komai zai iya faruwa kinsani.

Hmm Turaki ba Haka yakeba,
Duk neman matansa daya sakawa kansa yanzu wlh bazai taba ko kallon Laylah da wani yanayinba,
Ataqaice ko kallon fes baya Mata bare wani abun daban yazo ransa,
Barsa naji dasu akan wannan laifin dayamin…

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button