UBAYD MALEEK 28

Tun daga lokacin Basu sake ji ko ganin wani Abu daya danganci garin meriz ba sai yau sama da shekaru arbain kenan.
Tabbas zarginsu ya tabbata cewar a gizah kowanene yake Dan haka yanxu Kam aikinsu na gaske zai fara.
Dagowa yayi ya kalli Mr Omar dake jiran umarni ya maida idonuwansa kan jekadi Kai tsaye cikin kamewa yace”
Baza’a bari kowa yasan da zancenba ciki kuwa harda ita datayi aikin ki maidaita gizah idan tanacan ne za’a San waye shugaban aikin nata sbd na tabbatarda ita kanta nasan wa takewa aikiba sbd al’amarin me girmane bazasuyi saurin bayyanarda kansuba,
Amfanin wannan aikin na meriz da aka sata shine komawata gizah neman magani sbd sunyi tunanin acan ne kawai za’a samu maganin warkar Dani dagacan ne zasu qarasa niyarsu wadda baasantaba.
Gyada Kai jekadi tayi tace”
Kabar komai ahannuna kafin ka iso gizah Inshallah aikin yayi nisa
Inshallah sai Allah yacika nufin kaleeb Dan kuwa alqawarine sai anciyar da dabbobin gizah Naman duk Wanda ko da ido yataba ganin garin meriz bare ya taba.
Mr Omar ne ya matso yace”
Jekadi sai magana ta gaba itace umarnin maleek ne kada mushrah tasan abinda yafaru sai lokaci yayi hakama iyayenta
Duk abinda tayi idan lokaci yayi zatafada musu dakanta aranar qarshe da Babu gyara.
Gyada Kai jekadi tayi tana sake yiwa MALEEK fatar samun lafiya ta miqe ta fice.
Mr Omar kuwa gyara tsayuwa yayi yana sauke Kai yace”
Maleek meye ainihin wannan hukuncin na jinin mushrah da aka sanarwa jekadi.
Jininta ta aikata kuskure babba na cutatar da ‘yar uwarta hassadarta tasa tasaka kanta cikin masifarda tun kafin mahaifinta yazama saurayi bare yayi auren haihuwarta.
Wayar kaleeb ya karba da Mr Omar ya miqo Masa bayan yagama yimasa bayanin komai dasuke ciki suka fara magana kowanne cikin kalar nasa ikon da kamewa ta sarautar dake jininsu kafin ya ajiye wayar.
Miqewa yayi tareda nufar kofa sai ya dakata ahankali batareda ya juyoba Kai tsaye yace”
Ka bawa jekadi muriz din damuke ajiya sbd bincike abisaga umarnin kaleeb kullum abata drop daya acikin abinsha ahaka har agama gano ainihin shugabanta duk tsanani kada abari asan muriz ake Bata sbd kaucewa basu alamar ansan dasu.
Cikin jinjina Kai Mr Omar yace”
Yanda kaleeb yace shine daidai.
Fitowa sukayi suka nufo ciki Koda suka shigo direct sama maleek ya wuce kasancewar NURU batanan hakama afia yasa jekadi da kanta ta tsare kitchen harsaida Fana tayiwa maleek din breakfast aka jere Masa Mr Omar Kuma na daga bakin kofar Palo shima ya kafa ya tsare.
Padima datake jiran Jin mugun labari na kuka ya faru agidan taji Babu komai batajin motsin kowa alamun lafiya Amma duk da hakan qin fitowa tayi tanajin hankalinta Sam be kwantaba gabaki daya gizah takeson komawa ta karbi dukiyarta da tukuicinta na aikin da aka sakata da dasa tata cin sabuwar duniyar.
Sai yamma sosai su NURU suka dawo cikin farin ciki da walwala suke duk su dukan sbd Gama exams dasukai.
Wanka nuru tafarayi ta Sanya blue pencil jeans da farar _Gaultier_ top me hannun shimi ta fito a kicinma taci abinci tanason mgn da jekadi Amma Sam jekadin taqi Bata dama qarshema ce Mata tayi allergy ne Kamar yanda Mr Omar yafada Mata.
Padima Saida NURU tadawo tafito suna fira sama sama Dan takasa sakewa Kai tsaye tacewa NURU gida zata koma.
Da mamaki NURU ta kalleta zatayi mgn jekadi ta qaraso cikin girmamawa ta kalli NURUn tace”
An kammala maganin maleek.
Da wani irin farin ciki me tsanani data danne padima ta juyo ta kalli jekadin tanajin dukkanin damuwarta ta yaye kenan yasha tea din boyewa suke baida lafiya kenan.
Miqewa NURU tayi tabar gurin tana cewa”
Padima Ina zuwa.
Murmushi me Fadi jekadi tasakarwa padime tana cewa”
Ki huta lafiya jinin mushrah.
Cikin farin ciki padime tace”
Yawwa.
Dama tanason sanin halinda yake ciki duk da tasan yanzu ko kallo bazata samu daga maleek dinba Amma tanason tabbatarwada yasamu lafiyar Dan haka ta dauki tray din ta fito kenan ta hadu da farhat tana cewa”
Aunt NURU abincin daddy ne wanna?
Gyada Mata Kai kawai NURU tayi tana cewa’
Bari na aje anan ki jirani na sanyo jallabiya saimu Kai Masa.
Jekadi dake fitowa daga kicin ta matso gaban NURUn a natse tace”
Abincin maleek ba’a barinsa ako Ina shiyasa ko jiya yasamu allergy.
Kallon kanta tayi taga shigar Sam Bata daceba da zuwa gurinsa zatai magana jekadi ta sauke Kai tana cewa”
Afito lafiya.
Numfashi me sanyi ta sauke tareda daukan tray din tana satar kallon hanyar dakunansu tafara hawa saman sbd kada afia ta fito.
Tana shiga palon farko ta tsaya kofar palonsa na kurya tana sauke ajiyar zuciya sbd gabanta dake faduwa ta kalli farhat data bude kofar Kai tsaye ta shige tayi gurinsa da gudu Yana zaune kan royal kushin yayi crossing fararen qafafuwansa da Babu takalmi sai daukan ido suke kaman baya taka kasa dasu.
Shigowa tayi qafafunta na Dan rawa ta qaraso ta ajiye tray din kan table tana dagowa maleek dinma na waiwayowa yayi Mata kallo daya ya juya sbd kayan dake jikinta.
##MAMUH#
Mamuhgee 28_*Da asuba Saida afia ta tada ita sbd nannauyan baccin daya dauketa ta bude ido daqyar ta kalli afia kanta na wani irin sarawa sbd nauyi dayayi mata sbd rashin bacci da damuwar abinda yafaru cikin daren.
Tashi tayi daqyar ta nufi toilet tashiga tayo alwala tafito ta tsaya gefen afia ta tada tata sallar.
Suna idarwa afia ta ringa satar kallonta a kaikaice sbd duk wani motsin NURUn qamshin turaren dad dinta takeji ajikinta yana tashi.
Shiru tayi sbd batamasan mezatace ba Amma mamakinta anan Ina NURU ta hadu da qamshin?
Ta Yaya?
Ganin idan tayi magana Kamar ta muzanta NURUn ne yasata yin shiru ta Adana kalamanta tukuna.
Gari nafarayin haske NURU ta fito ta nufi dakin mum Sarah ta dubo jekadi har lokacin bacci takeyi saita fito ta nufi dakin padima ta tura tajisa arufe taga key din ajiki ta waje saita bude dakin tareda shiga har lokacin bacci padiman keyi ta qarasa bakin gadonta ta taba bargonta ahankali zata tasheta
Padiman tasaki wani razanannan ihu tana zabura zaune gumi duk yagama jiqata idanuwanta duk a waje take kallon fuskar NURU jikinta na Dan rawa ta sharce gumi tana saukowa daga gadon.
Da mamaki da tsoro NURU ke kallonta tace”
Lafiya padima?
Mafarki kikayine kike wannan ihun kina hada gumi haka?
Kasa kallonta padima tayi sbd har lokacin gumi takeyi cikin tsananin firgicin mummunan mafarkin datayi batareda ta waiwayo ba ta nufa hanyar toilet tana cewa”
Mafarki nayi sbd banyi addua ba na kwanta.
Bayanta NURU tabi da kallo cikin mamaki sosai kafin ta juya ta fice daga dakin ta nufi kitchen tana Danna Kiran Mr Omar.
Saidata tabbatarda ita kadaice a kicin din tace”
Gud morning Mr Omar.
Barka da tashi ranki ya dade”yafada daga can bangaren cikin girmamawa.
Shiru tayi cikin nazarin abinda zata fada Masa…shikuma Jin hakan sai ya gyara murya cikin nutsuwa da Bata tabbaci yace”
Dr Damien yazo ya duba MALEEK tun six harya wuce ma inshallah komai ya wuce.
Sake yin shiru tayi tana wani nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya me sauti tace”
Mr menene wannan ciwon?
Shin kodai wani abun sukaci kokuma ya taba skin dinsu?
Tsit Mr Omar yayi Jin tambayar tata saidai baija shirun da tsayiba Dan kada ya Bata hope na zai amsa tambayar ya Dan sake gyara murya cikin Bata girma yace”