UBAYD MALEEK 29

NURU aure da kike gani Kona soyayyane saika dage da kulawa da naci akan wasu abubuwan sbd kusan a rayuwar aure ke mace kece zakija ragamar Kama hanyar zuwa wani mataki,

NURU kinshigo wata irin baudaddiyar rayuwar aure wadda kike buqatar juriyada kokartawa kafin kisamu matsayinki na Matar gida idan ba hakaba rayuwarki da quruciyarki zasu qare su tsufa cikin tausayi me tsanani,

Aure gidan sarauta musamman irin naki auren dayake da qalubalai da tazarori masu yawa,

Shawara daya anan itace ki maida hankali ki dage karki dage a Gina karatu kawai ki zauna kiyi nazari aurenkima kina buqatan dage Masa Dan bawa kanki suna da matsayi a gidanki sbd karki tsufa agidanki bakisan suna ko matsayinki a gurin Wanda kike aureba Dan kuwa wannan wata rayuwace da Kika shigo ba Babu fita sai mutuwa hakama akwai qalubalai agabanki Dan haka ki nutsu kiyi abinda yakamata kiyiwa kanki yaqi kema Dan tabbatarda zamanki acikin aurenki sbd auren MALEEK babban rabone agareki ki,

Kibude idanuwanki ki daina yadda da kowa da komai sai abinda zuciyarki ta nutsu dashi NURU.

Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace”

Nagode jekadi.

Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace”

Ranki ya dade Zaki iya tafiya.

Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.

Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai

Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta fito daidai shigowan farhat Nan suka shirya sukai sallah tare daganan tacewa farhat baccin awa biyu zasuyi kafin la’asar

Nan suka kwanta.

##MAMUH##

KUYI MANAGE.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button