Lu’u Lu’u 39
*39*
A hankali Musail ya mik’e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace “Na d’auka na raineki da kulawa, ki kashe ni ba damuwa, amma ‘yata ki rabu da ita ta rayu cikin farin ciki.”
Tsakiyar idonsa ta kalla tace “Ni ba’ yar ka ba ce? Idan ka san ba ka so na me ya sa ka yi cikina?”
D’auke idonshi yayi daga kanta yace “Ina so na ji daga bakinki, shin da hannunki a wannan harin ko babu?”
A hassale tace “Da hannu na a ciki, kuma da taimakon wad’anda ba ka tsammani na zartar da hakan, d’ayan ka kama shi yanzu sai kuma ni da ke gabanka, amma na biyun ina tabbatar maka zai ga bayankkkka…”
Duk da ta kai k’arshen kalmar amma marin daya mata ya gigita ta sosai, k’ara ta saki ta da durk’ushewa tana dafe kunci, da sauri Ayam da ta fi kusa da ita ta sunkuya ta kamata sannan ta kalli Musail dake huci tace” Pah, ka yi hak’uri mana.”
Tallabo fuskar Zafreen tayi dan ta ga ko bata ji ciwo ba, da k’arfi ta fizge fuskarta ta mik’e a hassale ta kalleshi sannan tace” Ko za ka kasheni ba zan canza k’udiri na a kan ka ba, mugu.”
Juyawa tayi da sauri zata koma d’akinta sai kuma ta tsaya cak sakamakon fadawan da suka shigo da gudu gudu suka jeru a bakin k’ofar, daga ganin dakarun zaka fahimci daga masarautar da suke, Juman da ta fi kowa gane su wanene tuni ta mik’e tsaye tana zazzaro ido tana kallonsu.
Babban dogarin cikinsu ne ya fara shigowa hannunshi rik’e da bindiga dan bada tsaro, a bayanshi tsofaffin suka shigo, cikin nutsuwa da shan k’amshi suke takon, saidai fuskarsu ta nuna alamun tashin hankali da jimami, rik’e suke da hannun juna cikin shiga ta alfarma, fararen kaya masu ado kamar ba gobe, inda Bilkees ke sanye da wani babban lullub’i har yana jan k’asa.
Saman fuskokin da suka sauke dubansu yasa fuskarsu ta canza daga alhinin nan zuwa murmushi dake bayyanar da tsantsar farin ciki da kuma annuri.
Umad da Haman da shi dai tunda ake tattaunawar nan bai ce uffan ba ne suka mik’e a tare saboda girmamawa, Juman na had’a ido da iyayenta wani dad’i ya lullub’eta, da gudu ba tare da jin ta manyanta ba ta isa garesu, tana zuwa ta sake k’urawa fuskokinsu ido, ba ta jira komai ba ta fad’a jikin mahaifiyarta wacce ita ma k’walla suka fara gangaro mata.
Cikin kuka mai tsananin gaske Juman ta furta “Mah, na yi kewarku sosai.”
Cikin kuka ita ma ta amsa da “Ni ma haka Juman, kin girma sosai.”
K’am k’am suke mak’ale da juna hakan yasa sarki Abdallah rumgume su gaba d’aya yace “Ni ne ba kwa k’auna kenan?”
D’an d’agowa sukayi suna had’a ido ta fad’a jikinshi tana sake fashewa da wani kukan, daddab’ata ya dinga yi yana share k’walar farin ciki shi ma yana fad’in “Shikenan ‘yata, ya isa haka, kukan ya isa haka.”
Da sauri Ayam ma ta matso ta rumgume Bilkees, sun jima haka kafin ta d’ago tana murmushi saboda abinda sarki Abdallah ke fad’i cewa “Mik’o min matata nan na rumgume.”
Fad’awa tayi jikinshi tayi luf abinta kamar za ta yi bacci. Musail da ya gama tsurewa a tsaye kallonsu kawai yake, mamakin yanda suka musu dirar mikiyar nan ya ke, wad’anda basu tab’a zuwa ba su ne yau suka zo? Zuwan ma kuma da wasu irin dakaru kamar ma su jiran ya k’i, ga shi sun musu wani irin zuwa da sassafe haka, gashi tashin hankalin da suka kwana dashi har yanzu gidan a hargitse yake, hadimai sun bazu ta ko ina ana ta gyaran gidan saboda kamewar da yayi, wannan hayaniyar ce ma da nisa a cikin abinda suke tattaunawa ya hanasu jin shigowar motocinsu sai kawai dirowar dakarun nan.
A hankali ya shiga takawa k’afafunsu na neman bijire masa haka dai ya kai kanshi gabansu ya tsaya, a ladabce abinda bai tab’a yi ba, hasalima bai gansu ba bare yayi sai gashi ya rusuna yana fad’in “Barkanku da zuwa masarautar Khazira.”
Sarauniya Bilkees da sarki Abdallah tare suka kalli juna, sai kuma Juman data kallesu ita ma tana mamakin abinda yayi, cike da dauriya sarki Abdallah ya gyad’a kai yana murmushi sannan yace “Muna godiya da wannan karamcin.”
D’an juyawa yayi ya kalli babban bafadenshi ya masa alama da ido, juyawa yayi ya umarci sauran dakarun da su fice, suna fita kuma Bukhatir ya shigo tare da Zeyfi su ma cikin shiga ta daraja, sannan mahaifiyarshi ta biyo bayansu da sauran yan uwa a k’alla goma.
Ido da Zafreen ta d’ora akan Bukhatir yasa ta waro ido tana kallonshi, satar kallon mutanen dake wajen tayi sannan ta kuma kallonshi bakinta d’auke da tambayoyi bila adadin.
Farin cikin daya kacame iyalin a lokacin na murnar ganin juna bayan shekaru masu tsayi, shi ya d’auke hankalinsu har Zafreen ta matsa kusa da Bukhatir daga bayanshi cikin rad’a tace “Me ka ke yi nan a daidai wannan lokacin? Baka san abubuwa sun lalace ba ne?”
Saida ya saci kallon mutanen ya ga babu mai kallonshi sannan yace “Na sani, amma dole ce ta sa na zo, sarki ya umarce ni ba yanda zan yi.”
Tsaki tayi cikin jin haushi tace “Kashh!”
Juyawa tayi ta nufi d’akinta ranta a b’ace sosai, da kallo Musail ya bita tare da k’ank’ance idonshi sannan ya saci kallon Bukhatir, k’wafa yayi a sanyaye tare da murmushin mugunta wanda shi kad’ai yasan ma’anarsa.
Da tsantsar farin ciki Juman ta kuma kallonsu da kyau tace “Mah, ya aka yi kuka zo nan haka ba sanarwa? Ya kuma na ganku gaba d’aya?”
Yar dariya tayi ta kalli Ayam dake gefenta ta dafa kanta tace “Shagalin bikin jikata muka zo.”
Da sauri suka shiga kallon kallo, duba da su ma akwai magana a bakinsu yasa Musail fad’in “Ranka shi dad’e, ina ga mu je b’angarena mu zauna, dan nan ana gyarawa, wata yar hatsaniya ce ta faru da tsakiyar dare.”
Cike da dattako sarki Abdallah yace “Mun samu labarin komai da ya faru, shiyasa ma muka taho da wuri haka dan tabbatar da kuna cikin k’oshin lafiya.”
Galala Musail ya kalleshi sanda yayi magana yana mamakin furucin shi, hakan na nufin shi ma yana da nashi d’an lek’en asirin a cikin fadarsa?
Adah ne ya fara wucewa gaba sannan Musail suka fita a falon, cikin nutsuwa da kallon juna har suka shiga falon na shi, wanda babu wanda bai kalleshi ba saboda had’uwarsa da tsaruwa, wuri suka samu duk suka zauna, inda Ayam ke zaune tsakanin sarki Abdallah da sarauniya Bilkees akan kujera mai zaman mutum uku.
Juman kuma na zauna kujerar mutum biyu ita da Musail sai Adah dake tsaye a bayansu, sai Umad da Haman da Bukhatir suna k’asa kan carpet da sauran yan uwan Bukhatir maza da mata.
Juman dake kallon iyayen na ta ne ta fara cewa “Pah, ya aka yi kuka san abinda ke faruwa?”
Kallonta Ayam tayi tace “Ba wannan ba Mah, ya aka yi suka kan da maganar auren da ake fad’a a kai na?”