Hausa Novels

Lu’u Lu’u 46

_Bismillahir rahamanir rahim_

*46*

 

 

Shi kuma sam bai fahimci inda suka dosa ba dan haka ya kallesu da mamaki yace “Kamar ya Mah?”

Dungure masa kai tayi tace “Shak’iyi, ciki ne da ita to.”

Wani irin zaro ido Ayam tayi ta wangale bakinta gaba d’aya ta rarraba idanunta akan su, shi ma da sauri ya kalleta yana wulk’ita ido da mamaki, sosa k’eya ya fara cikin sand’a ya sulale ya bar d’akin, Ayam ma sauka tayi daga gadon tana kallon k’eyarshi tace “Yallab’ai tsaya, dakata mana, wallahi ka zo…”

Ficewa sukayi daga d’akin kuma dukansu kama gabansu sukayi dan kunya ce ta gaske ta rufe su.

Har k’ofar falon suka rakaso zasu tafi, ban kwana sukayi cike da taya juna jimami kafin su nufi motocinsu, tare da Umad suka jera suna tafe inda take tambayar shi “Yaushe za ku taho?”

A ladabce yace “In Shaa Allah Mah zamu shigo.”

Jinjina kai tayi tacce “Ka ga dai yanzu tana buk’atar kulawarka, ka kula da ita ka ji ko?”

Jinjina kai yayi yace “Shikenan Mah.”

*A kwana uku* matan da suka rasa mazajensu takaba suke irin ta addinin musulunci, inda yayansu da masoya kuma suke cike da jimami har yanzu, Umad ma ya koma Giobarh karb’ar tashi ta’aziyar inda suka tattauna da sarki Abdallah lallai lallai zai dawo nan da kwana kad’an dan ya d’auki matarsa.

Kwana biyun da yayi bata ganin gilmawarshi sai ta fara fahimta ashe ya mata illa a tsanake, bata tab’a yarda tana jin wani abu a game da shi ba sai kwanan nan, hakan yasa kullum cikin tuna ranakun hidimar bikinsu take, irin yanda yake matse mata wuri, da yanda komai sai ya tab’a jikinta, sai hakan ya zama abokin nishad’inta, uwa uba kuma idan ta dafa cikinta ta furta “Ciki ne da ki? Kuma wai na Umad?”

Sai ta saki murmishi mai sauti ta rasa dad’i take ji da hakan ko kuma akasin haka, a yanzu dai bata wani laulayi inba yawan cin abinci ba, duk da mutuwar nan da aka yi bata wasa da cin abinci, idan ta ji cikinta na buk’ata ko kuma ita ce tayi sha’awa ta kan umarci hadimai su wadata gabanta da kayan alatu.

*Bayan kwana uku*

Lomar farko kenan ta kai bakinta wayarta ta d’auki kururuwa, saida ta kuma kai loma ta biyu baki sannan ta karb’i wayar da hadimar ke mik’o mata, dannawa tayi ta d’auka sannan ta kara a kunnenta a sanyaye cike da sangarta tace “Hello.”

A tausashe Umad ya amsa da “Hello! Ya kike?”

Turo baki tayi tace “Lafiya lau, ya hak’uri?”

“Alhamdulillah.” Ya fad’a kafin ya d’ora da “Me kike ci?”

Hannunta ta kalla dake cikin plate d’in da aka had’a mata kwad’on salade da cocomber sannan tace “Salade.”

Numfasawa yayi yace “Yana sa ki ci sosai ko?”

Kyab’e fuska tayi tace “Um.”

Murmushi yayi yace “Zai daina, yanzu fad’a min yaushe zaki zo?”

Zaro ido tayi tace “Ina?”

A hankali ya furta “Gidan ki mana, gidana.”

Girgiza kai tayi tace “Um um! Na zo ka dinga min wannan abun ko?”

Gimtse dariyarshi yayi yace “Wane abu kuma na ke miki?”

Shagwab’ewa tayi tace “Ka yi ta tsutsar min baki kana tab’ani ko ina.”

Da mamaki yace “Ba kya so dama?”

Da sauri tace “E.”

Jinjina kai yayi kamar yana gabanta yace “Shikenan to na daina daga yau.”

Ita ma kamar tana gabanshi tace “Ka yi alk’awari?”

A take yace “Na yi.”

Jinjina kai tayi tace “Shikenan zan zo.”

“Yaushe kenan?” Ya fad’a yana gyara zamanshi da yin yar mik’a, a sanyaye tace “Idan na fad’awa Mah.”

Lumshe ido yayi yana d’an taune leb’enshi cikin wani irin salo yace “Ina… son…ki Aya…m, sai kin zo.”

Daga haka ya kashe wayar ita kuma ta bi wayar da kallo, murmushi ta tsinci kanta da saki na jin dad’in abinda ya fad’a, aje wayar tayi sannan ta ci gaba da cin salade d’inta hankali kwance.

Saida ta kammala sannan ta mik’e a nauyaye tana jin wata kasala ta nufi d’akin Juman, da sallama a bakinta ta shiga inda Bilkees ta amsa mata dake zaune da carbi a hannunta tana ja.

K’arasawa tayi ta zauna ta d’ora kanta a kafad’ar Bilkees, hannunta tasa ta rik’o hannun Juman tana murzawa a hankali tan kallon fuskar Juman d’in, tana tsananin tausayin mahaifiyarta sosai, irin yanda suka rayu da mahaifinta da rad’ad’in da take fama da shi yanzun na rabuwarsu kwatsam, sai abun ya nemi cireta a hayyacinta gaba d’aya, sa’a d’aya da mahaifiyarta ta kasance a tare da ita a daidai wannan lokacin, sannan ta zama jajirtatta mai d’ebe mata kewa da k’arfafa mata gwiwa da dad’ad’an kalamai, sannan take tunasar da ita mahaliccinta ne ya so hakan, sannan da tuna mata ita ma zata riskeshi inda ya je, sai komai ya zo mata da sauk’i har wani lokacin idan ta fara hawaye take gaggawar dakatar da su saita maye gurbinsu da ambaton Allah da yi wa mamacin addu’ar dacewa a sabon gidansa.

Muryar Bilkees ce ta dakatar da tunanin sanda take fad’in “Ki shirya jirgin asubar yau zai tashi tare da ke, zaki koma kusa da mijinki.”

Da sauri ta d’aga kanta ta kalli Bilkees d’in, fuskarta data nuna tsufanta take kallo irin ta had’eta ba alamar wasa, turo baki tayi ta maida kanta saman kafad’ar tace “Ni ba gobe ba gaskiya Kaka.”

Kallonta tayi tace “Kamar ya? Saboda me?”

Turo baki tayi tace “To ai shi ma ya ce sai sanda na ke so zan tafi.”

Da sauri Juman ta d’ago kanta ta kalleta, fizge hannunta tayi dake cikin na ta ranta a b’ace muryarta har hard’ewa take tace “Maza tashi ki bar nan, kuma ki tabbatar kin fara shirin tafiya wajen mijinki da asubar nan.”

D’auke kanta tayi daga kanta tana fad’in “Bai zama izina gareki ba ki rumgumi mijinki kafin mutuwa ta rabaku.”

Sai kawai ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da hijab, da sauri Ayam ta gyara zamanta ta dafa kafad’arta tace “Mah kiyi hak’uri dan Allah ki daina kukan, zan tafi to, na tashi ma kin gani ko ? Zan shirya yanzu kuma zan tafi d asubar.”

Mik’ewa tayi ta kalli Bilkees dake kallonsu ta rasa wacce zata rarrasa tace “Kaka ki ce tayi shiru to, na tafi ai kin gani ko.”

Da hannu Bilkees ta mata alamar ta tafi, hakan yasa ta juya da sauri ta bar d’akin zuwa na ta, dukanqu saida suka ci kuka har ita kanta Ayam d’in kafin ta fara tattara duk wani abu da ta san zata iya buk’ata a zamanta na dindindin.

*Tana* zaune kan sallaya ta idar da sallah isha’i ya kirata a waya, a kasalance ta mik’e ta d’auki wayar dake kan gado sannan ta zauna bakin gado ta d’ora a kunne ta fara da sallama, amsawa yayi a nutse tare da fad’in “Kin wuni lafiya?”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button