Hausa Novels

Lu’u Lu’u 45

_Bismillahir rahamanir rahim_

*45*

 

Tattausan kayan bacci ya d’auko mata dogon wando da rigarshi mai k’ananan hannaye farare tas masu tambarin sunan Rundahao, saida ya zaunar da ita yana k’ok’arin kwantar da ita sai ta dage ta k’i kwantawa, zaune yayi yana fuskantarta, ita ma shi ta kalla a lokacin suka had’a ido, a tausashe yace “Saki abinda yake ranki Sajeeda, bari hakan a zuciya zai haifar miki da damuwa.”

D’aga mata gira yayi yace “Yi kuka, yi kuka ki k’oshi Sajeeda.”

Kamar ya bata lasisin sai kuwa ta fashe da kuka iya k’arfinta, take ya lumshe ido saboda ji yayi kamar ta karci zuciyarshi da k’arfe.

Jawota yayi jikinshi ya kwantar yana shafa bayanta alamar rarrashi, saidai bai ce mata k’ala ba ya bata damar kokawa dan rashin hakan zai zamar mata matsala.

Saida ta ci kuka mai isarta daga nan har bacci ya d’auketa tana ta ajiyar zuci, gyara mata kwanciya yayi ya rufeta da abun rufa sannan ya koma ban d’aki yayi wanka shi ma ya d’auro alwala ya dawo, sallaya ya shinfid’a sannan ya kabbara sallah yayi raka’a takwas sannan ya sallame, mik’ewa yayi ya sulale ya fice kai tsaye d’akinshi ya nufa.

Wudar ya samu idonshi rufe alamar bacci yake, saidai duk da ba wani tsaye yayi ya dubashi ba ya dai fahimci ba wani sauke numfashi yake ba, sharewa kawai yayi dan abinda ya fito da shi ba na wasa bane, mahaifinshi kuma yana ganin idan ma yayi gigin tashinshi zai kuma cakula masa lissafi ne da maganar matarshi. Dan haka ya rab’ashi ya wuce zuwa wajen da kayanshi suke ya canza sannan ya d’auki k’aramar bindigarshi ya saka a k’ugu sannan ya fita a d’akin a hankali.

Tunda ya duk’ufa a cikin gidan nan daga inda aka yi harbi har zuwa gawar wanda aka samu, dagewa yayi da taimakon su Haman da sauran tawagarshi har saida suka gano bakin zaren, daf da asuba ya dawo gidan ya shiga d’akinshi dan canza kayanshi, abinda ya fara tsaya masa a zuciya shi ne yanda ya bar mahaifinshi haka ma yanzu ya same shi, sai hakan ya d’an jefa masa shakku, tunda dai ai mai bacci ya d’an motsawa ko da cikin baccin ne har kwanciyarshi ta canza, bare kuma shi da ba lafiya ce da shi ba.

Da sauri ya k’araso gare shi ya kai hannunshi kan fuskarshi ya tab’a, sanyi k’alau ya ji kamar komai baya tafiya, da sauri ya sunkuya ya sake kai hannunshi kan wuyan shi ya tab’a, a rikice ya d’ago hannunshi ya rik’e wuyan hannun yana sauraren harbawar jijiyarshi, a kid’ime ya furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Pah! Pah ka tashi ! Pah kar ka min haka kai ma dan Allah, ka tashi.”

Cakumar rigarshi yayi ya rumgume ya tusa kanshi ay k’irjinshi yan hawaye, mutuwa dole ce ga duka mai rai, saidai ya ji zafin ta mahaifinshi daya kasance ya tafi ba tare da ak’ida ba, sannan ya tafi da ciwon son matar da yake aure, sam hakan bai masa dad’i ba.

Masarautar Khazira dai sai ta sake rikicewa saboda mutuwar sarakunan nan guda biyu a lokaci d’aya, haka aka wayi safiyar gidan a kid’ime a kuma gigice ana ta shirin kawar dasu zuwa gidansu na gaskiya.

Shaf ya manta da Ayam dake d’akinta, ya manta ita kanta a wani hali take na d’imuwa da kewa, sanda yake rumgume da Kossam dake kuka ne kawai abun ya zo masa a rai, da sauri ya d’an janyeta a jikinshi a ladabce ya mik’e da sauri ya nufi d’akinta.

A k’ofar shiga sukayi kicib’is da ita ta fito, sanye take cikin wani irin shiri na ban mamaki, sak ta fito a sarauniyarta ta k’asar Khazira, hatta da kambun da mahaifinta ya saka mata da sark’ar da ya so saka mata saida ta sako sannan ta fito, fuskarta kuma a tamke take ba alamar fara’a bare tayi wasa da wani.

Cak ya tsaya yana kallonta bakinshi da ya masa nauyi ya d’aga yace “Ay…ina zaki je? Ya haka?”

Ba alamar fara’a tare da ita fuska a gimtse tace “Zan je ga kujerar da mahaifina ya bari, ba zan zauna na yi ta kukan rashinsa ba, zan d’auki mataki akan wad’anda suka kasheshi.”

Hanya ta kama zata rab’ashi ta wuce ya rik’o hannunta, juyowa tayi suka had’a ido a d’an kausashe tace “Sake ni.”

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya saki hannunta, juyawa tayi zata wuce a tsanake yace “Mahaifina ya rasu.”

Cak ta tsaya ta juyo ta kalleshi, sai ta ji ba dad’i sosai, a hankali ta tattare rigarta dake jan k’asa ta dawo gabanshi ta tsaya, kallon juna suke kalar zasu had’e kansu, a ladabce ta furta “Kai…ma ka yi rashin mahaifi? Yanzu mun zama…marayu kenan?”

Kuka ne ya k’wace mata da sauri ta fad’a jikinshi ta fashe da kuka, daddab’ata ya dinga yi yana fad’in “Shiiiii! Ki daina kuka kinji, In Shaa Allah Ayam ba zan bari ki yi maraici ba matuk’ar ina raye, ban sani ba dai ko ni…”

Bata sanda ta d’ago ta d’ora yatsarta a kan labb’anshi ba tace “A’a…”

Sai kuma tayi shiru ta sunkuyar da kanta, binta yayi da kallo yace “Uhum?”

Cike da kunya tace “Ba zamu zama marayu ba, muna da iyayenmu masu k’aunarmu.”

D’aga idonta tayi a hankali ta kalli k’wayar idonshi tace “Kuma ni ina da kai, sannan kana da…ni kai ma.”

Rintse idonshi yayi gam ya cakumi bakinta ya shiga tsutsa a zafafe saboda bai tsammani jin abinda ta fad’a ba yanzu, saida ya tsotse man data shafa a bakinta tas sannan ya saketa suna kallon juna.

Rufe idonta tayi ta sunkuyar da kai, amma sai ta ji idonshi na ta yawo a jikinta, da sauri ta wuceshi ta nufi hanyar fita har da d’an gudunta ta bar wurin.

Saida ya ga b’acewarta sannan ya girgiza kai yana murmushi ya bi bayanta dan ana shirin tafiyar jana’izar sakaranan na su ne ya kubto ya taho.

Dayawa sun so a tafi da Wudar zuwa kasarshi inda shi ma zai samu gatan da kowane sarki ke samu idan ya rasu, amma sai Umad ya ce tunda har ya mutu a nan to anan ubangijinsa ke son a binneshi, ba buk’atar sai an canza masa k’asa.

Saida rana ta hantse sosai aka yi bisar gawawwakin, inda Sarki Musail ya samu tagomashin da duk wani musulmi dake wurin ya sallaci gawarsa, sab’anin Wudar da d’aukarsa kawai aka yi zuwa makwancinsa.

Bayan an dawo daga bisarsu ana ta hada hadar karb’an ta’aziyya, Kossam kuma da hadimanta sun yi shirin komawa Giobarh dan tayi takaba a d’akinta, gaba d’aya cikin gidan shela ta karad’e kunnen kowa cewa sarauniyar Khazira na son ganin kowa da kowa a filin taro.

Duk wanda ya ji haka yayi mamaki, saidai haka suka mik’e suna tunkarar filin taron dake d’aukar dubannin jama’a, hatta wad’anda ke kurkuku saida ta sa aka fito mata da su daga ciki har da Dhurani.

Ba iya talakawan garin ba ne kad’ai, har da manyan mutanen da suka halarci jana’iza sun zo su ji me zata fad’a, haka ma akwai wasu sarakunan na wasu garuruwan da masu garin wasu k’auyuka da dagatawansu, hakimai, malamai da dai sauransu.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button