Uncategorized

Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

“Meye amfanin D’an da bai jin maganar iyayensa da yi musu biyayya? 

“Ni tsine mata ma naso yi tabi uwa duniya kowa ya huta ,dady yana fad’ar hk numfashinsa ya fara sama sama sai faman haki yake ,mummy tana ganin hk ta fara salati game da waige waigen Kafin kace me tuni dady ya fara fita haiyacinsa ,mummy tayi matukar rud’ewa sakamakon numfashinsa daya tsaya a matukar gigice ta kwallawa suhailat kira itama tashigo d’akin a rud’e tayo gurin momy dake jijigasa , tare da taimakon sulahait suka dawo da dady parlour’n, ruwa sanyi mummy ta dinga shafa masa sannan ya dawo haiyacinsa ya jike sharkaf da ruwa kwance ya ganshi ajikin momy wacce idanuwanta tuni sun dade da yin luhu luhu saboda kuka, dady ya d’ago idanunsa ya kalli momy da take faman tofa masa adduoi, da kyar dady ya iya bud’e bakinsa “wai ,abinda nake tunanin ne ya faru..?

Mummy tace ” a’a babu abinda ya faru ina dai tunanin BP dinka ne ya tashi bara nai ma doctor waya yazo ya duba ka. 

Jikin momy na rawa ta tashi daga gun datake zaune tana rungume da dady tmkr wani karamin yaro ,bedroom dinta ta nufa ta d’auko wayarta dake ajiye akan gado ta fara lalubo lambar cikin kankanin lokacin takira doctor ya d’auka ,ta fad’a masa duk halin da’ake cikin doctor yace “gashin nan zuwa .

Doctor Peter ya faka motarsa ya fito da sauri ya nufi hanyar da zata sadashi da parlour’n dady ,Amman a wannan lokacin momy tai masa jagora zuwa bedroom din ,doctor ya fito da kayan aiki yasoma dubashi ,byn ya gama ya kalli mummy yace ” “madam ya’akayi hkn ta faru jininsa ya hau dayawa sosai ?

“yakamata ku kiyayye ‘bacin ransa domin ya samu cikakkiyar lafiya mai dorewa mumy tace “doctor yanayin rayuwa ne kawai Amman za a kiyaye InshaAllahu. Doctor  

Ya bar magunguna da dady zai yi amfani dasu ,allurar bacci akayi masa domin ya samu ishashen bacci sannan yakama gabansa .

Ta bangaren fu’ad shima yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, duk inda yasan zai ganta yaje har dama inda bayi tunani ba, hankalinsa yayi maseefar tashi yarasa inda zai sa ransa yaji dadi shi kam a yadda yake ji acikin ransa bazai iya hakura da neman me’ad ba ,kodan tilon diyarsa mara lafiya har hawaye ya zubar aranar ya samu guri gefen titi yayi parking din motarsa ya d’aura kansa a saman sitiyari yana kukan tausayin halin da nasreen dinsa Zata shiga a sanadin wannan tashin hankali, yasan me’ad bawani kulawa zata bata yana jin tsoron ya rasata, ya dade agurin sannan ya tada motarsa yayi hanyar gida ,koda isa gidan kasa zama yayi sai faman zariya yake acikin parlour’n sakamakon sautin bugun zuciyarsa daya addabi kunnensa “wayyohlly Allah nah ya furta yana me rike kugunsa da hannu daya …..

 Daren ranar kuwa kwana me’ad tayi nafila Sam takasa runtsawa , saboda tashin hankali datake ciki yafi karfin tunaninta , tunanin mahaifinta yafi komai addabar zuciyarta, tayi shiru agurin tana lazimi tana jin kmr takirasa ta sake bashi hakuri ,daga inda take zaune ta mika hannunta ta d’auki wayarta tasoma neman layinsa ,takira wayarsa yafi sau biyar ba’a d’auka ba kawai ta rushe da kuka tana cigaba da addu’a, sai kusan ukun dare bacci ‘barowa yayi awon gaba daita. 

Washegari da wuri ta tashi ta shirya nasreen cikin uniform din school itama ta shirya kanta ,ta tasota gaba, tana gaba tana binta abaya har reception,ta bada makulin d’akin domin killaceshi sannan suka fice .

kai tsaye wani had’ad’en restaurant suka nufa tayi musu order abinci, ta turawa nasreen abinci agabanta tare da yin tagumi ta tsura mata ido “ki ci abinci ….. “Momy ke meyasa bazaki ci ba ?Tayi mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka “kici kawai nasreen bazan iya ci ba …….

take idanun nasreen ya cicciko da kwalla “why momy…..ta fad’a hawaye na gangaro mata”tun jiya banga abinda kikaci ba ,idan bazaki ci ba nima bazanci ba takarasa mgnr hawaye na biyo kuncinta sharrrrrr ..

me’ad tayi saurin kai hannuta saman fuskar nasreen tana goge mata hawaye “, no my bby dont cry I will eat tasoma k’ok’arin dibar abinci ta kai bakinta “gashi ina ci kema ki ci kinji bbynah banason damuwarki ina matukar sonki duk da dadynki nagani kmr banasonki ,adalilin ban ajiye aikina ba Wanda hkn bashi zai nuna bana sonki ba ,nice nayi silar zuwanki duniya idan wuya ake ci naci idan dadi ne naci” ta yaya mutun zai d’auki ciki har na tsawon wata tara yayi na kuda ya haifi d’ansa ace masa bai sonshi …..

“ki daina d’aukar maganganun mahaifinki, abaya nasan nayi sakaci , rashin kulawa dake Wanda bashi yake nufin bana sonki ba ….ina sonki nasreen fiyye da kaina sannan a shirye nake Dana sadaukar da rayuwata akanki, akan mahaifinki nayi komai har sanda na mallakeshi matsayin miji gareni ,ina kuma ga ke dani kad’ai nasan azaba da wuyar Dana sha tun daga haihuwarki har zuwa yanzu.

Ta k’arasa mgnr tana bata abinci abaki suna ci tana kwantar mata da hankali har suka gama tayi dropping dinta a school takama hanyar zuwa office,Akan hanyarta ta zuwa aiki duk inda taga Almajiri sai ta tsaya tabashi sadaka maganin maseefa ..

Ahankali ta Sanyo hancin motarta cikin ma’aikanta tsirarrun mutanen da suka yi sammakon zuwa suka bita da kallo , inda take jikinta ya bata akwai abu dake tafiya a kasa, wata irin damuwa me tattare da tashin hankali ne sukayi mata diran makiya ,amman hk bai hanata sanyawa zuciyar Kwarin gwiwar ba ,ta nufi gurin data saba ajiye motarta tayi parking tana fargaban fitowa ,kusan minti talatin tana zaune works nata faman shigowa ciki har dasu mudansir da ma’aruf suka fito atare suna kyalkyake dry da alamun suna cikin nishadi suka shiga cikin ma’aikatan batare da sun lura daita ba.

 tana zaune tahir shima yashigo ya wuceta. 

 ahankali ta fito da system dinta tasoma operating domin k’arasa tura sakonin da’akayita turo mata daga daren jiya zuwa safiyar yau din nan ,bata fito ba har sai da taga shigowar chairman sannan ta fito adaidai karshen dogon korido ta had’u da mudansir yayi saurin k’arasowa inda take ya amshi jakar hannunta da system, ita kuma tacigaba da tafiya ta nufi hanyar office dinta da niyyar shiga ta gani ko zata daina jin zafin dayake mata.

Mudansir yabiyo bayanta da Dan hanzarinsa “madam yau fa akwai meeting da chairman “nasani ta bashi amsa atakaice tana kusa kanta cikin office dayake tun shigowar mudansir ya bud’e, wanda ya zamemasa kaida .

ai da wani irin sauri me’ad ta fito daga cikin office dinta kmr zata hantsila tana furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun lahaula wala kuwata illa billa….

Shi kuwa mudansir kad’an yarage bai kyalkyale mata da dryr mugunta ba saboda yadda yaga tafito aguje kmr mota ….

numfashi take fitarwa ahankali tana jin zafi ajikinta, tayi saurin barin jikin kofar Dan tiririn dake ta’ba fatar jikinta, ta nufi conference room, koda ta isa ta iske chairman zaune tare da mataimakinsa Wanda yakasance ba indiye ne ,shine na biyu a company sai ita, duk sauran wad’an da ke zaune agurin akarkashin ikonta suke, ahankali ta samu guri ta zauna a natse zuciyarta na bugawa ,wannan shine karo na farko da za’a yi taro ta tsinci kanta cikin matsanancin fad’uwar gaba ,duk taron da za’a yi cike take da natsuwar zuciya da kwarin gwiwar tare da isa da mallaka da nuna ita din wata ce acikin ma’aikatar ,sai gashi yau babu wannan zarra da isa da mallaka sai tsagwaron tsoro dankare da zuciyarta. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button