Uncategorized

Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

Ad

_____

nasreen taji abinda momy’ta ta fad’a sarai amman taki motsawa daga inda take zaune, illa idanun data tsurawa momy’nta tana kallonta cike da tambayoyi.

ahankali Me’ad ta zagayo inda take zaune tana kallonta “bby let’s go now tana me kamo tafin hannunta ta fito daita daga cikin motar, sa’an nan ta meida murfin motar ta rufe, tasoma tafiya rike da hannun ta. 

  yayinda ma’aikatan gidan suka shiga gaisheta cike da girmamawa, hannunta kawai ta iya d’aga musu tacigaba da tafiyarta batare da juyowa ba,

Momy tana zaune a parlour’n tana waya Me’ad tasanyo kai cikin parlour’n a matukar birkice bakinta d’auke da sallama, momy na ganinta tayi saurin katse kiran saboda yanayin data ganta ,wujiga wujiga tamkar wace tayi shekara tana jinya.

“me’ad lafiya kuwa naganki haka kmr wacce ta tashi a jinya?

 “ko kuma kunyi Abind kuka saba ne da mijinki kika kwaso jiki zuwa gida? 

momy tajirowa me’ad wannan tambyar Tana dubanta a matukar tsorace me’ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune batare da tace mata komai ba, illa wani tashin hankali data tsinci kanta ciki.

 NASREEN ta isa gurin momy tashige jikinta tana gaisheta ,momy ta rungumeta ajikinta tsam kana tace “ykk nasreen?

 “yana ji jikin naki da zafi ko bakida lfy ne? 

 Naunayen ajiyar zuciya me’ad ta sauke kana tace “fitowarmu kenan daga hospital yau kwananmu uku NASREEN babu lafiya Tak’arasa mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka. 

Ad

momy tayi Shiru tana kare mata kallo had’e da nazarin yarinyarta, a kallon da take mata ta fuskaci tana cikin matsananci damuwa da tashin hankali, yayinda ita kuma me’ad din tashiga share hawaye wasu na gangaro mata… 

“To meye kuma abun kuka ?

” ko ciwon ne yayi tsanani?

 Me’ad ta girgiza mata kanta wasu sabbin hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta.

 ” meke damunki me’ad dan banji dadin ganin yanayinki ba ? ” sannan meye damuwarki ahalin yanzu da kike zubda hawaye ko duk akan matsalar ciwon NASREEN ne? 

ta sake girgiza kai kawai tana share hawaye, momy ta fuskanceta sosai hankalinta a matukar tashe “ke me’ad ki bud’e idanunki ,ki saka cikin nawa ni mahaifiyarki ce da duk duniya baki da kmr ni kuma nice nazama dole nasan damuwarki da abinda ya kawoki gida adaidai wannan lokacin daya kamata ace kina gurin aiki ne ko gidan aurenki “ki sanar dani damuwarki da abinda ke damunki domin Nasan mataki d’auka.. 

me’ad ta kalli momy fuskarta cike da tsantsar damuwa da tashin hankali still hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta tace “momy ina cikin babbar matsala ,ina cikin damuwa da tashin hankali, momy na cuci kaina da kaina na yaudari kaina,na zalinci kaina, na jawo kaina maseefar datafi karfina…. Momy nayi aure batare da farincikinku ba ,most especial dady, banyi muku biyayya akan aurena da fu’ad ba , gashi ayau an wayo gari komai na neman ta’bar’bare min, narasa gane komai nawa ,rayuwa na neman juya min baya ,  

“ahalin yanzu na dawo gida ne saboda bana jin zan iya cigaba da rayuwar aure da fu’ad …….

 jin wannan maganar yasa jikin momy yayi sanyi ta gyara zamanta tana duban me’ad cike da matsanancin tashin hankali, sannan tace “amman meye dalilinki na fad’ar duk wad’an nan maganganun hk ?

“abinda akayi shi tsawon shekarun goma sha meye na dawo shi ahalin yanzu? 

“sannan meye dalilinki na cewar bazaki sake rayuwar aure da fu’ad ba wani mummunar abun yayi miki ? Momy ta tambayeta jikinta na wani irin rawa haka zalika gabanta na fad’uwa ..

me’ad ta kalli momy ganin damuwa kwance akan fuskarta ,yasa wani irin tausayin mahaifiyarta ya saukar mata, ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gayawa momy.

momy tayi wata irin zabura daga zaunen datake rungume da nasreen ta mike tsaye kana ta zaunar da nasreen jikinta na d’aukar kyarma , dan maganar ta bugi zuciyarta matukar , ahankali tasoma kai kawo acikin parlour’n, lokaci guda kuma ta koma ta zauna ta kalli me’ad tace” yanzu ina najma take sannan a wani hali Sajid take ciki?

“momy nagaya miki na barsu agidan ,dan tunda abun nan ya faru ban sake taka kafata cikin gidan ba ,kinga sai suji dadin yin aurensu da tushe .

 “shikena me’ad to yanzu meye abun yi? 

me’ad tayi murmushi me tattare da takaici abinda sajida tayi mata ,sannan tace “momy kada ki damu ni nasan yadda zanyi da Sajida ,wallahi Momy sai tayi datasani tunanin auren fu’ad arayu…. 

“datasani uwar me zatayi tunda ke bakiyi dakinsani ba a aurensa da kikayi ? Wannan Sautin muryar ta katse mata hanzari ,ko ba’a gaya mata ba tasan sautin muryar mahaifinta ne yashigo parlour’n ,atare suka jiyo daga ita har momy suna mamaki jin Furucinsa.

Ahankali ya tako har zuwa inda suke yana tafi da hannunwansa Duka cike da tsansar jin dadin ganinta cikin damuwa da tashin hankali”ku daina mamakin jin abinda na fad’a “arayuwa kowa abinda yake so yake da burin mallaka, “kmr yadda kikayi tsayin daka kikace duk duniya babu wanda yayi miki sai d’an talaka dagin matsiyata, itama hkn ce zata kasance daita Dan hk banga abun tada jijiyoyin wuya ba …..

“Me’ad…. !!! dady Ya kira sunanta har sau uku in a serious thought wanda yasa kirjinta bugawa da sauri batare da tasan da hakan ba, “na’am dady ta amsa masa wasu hawayen na ciccikowa a idanunta sannan tasanya kwayar idanunta cikin nasa zuciyarta na sake lugud’en bugu da karfi saboda fargaban jin abinda zai sake fad’a.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button