Uncategorized

Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

Mahaifin me’ad bai bar gidan ba har sai daya gana da sajida inda yake ce mata “ta gayawa wakilan fu’ad su zo su sameshi idan sun tashi ,ita kanta sai alokacin tasan tayi kuskuren son mijin aminiyarta , Amman yazatayi da tata zuciyar datayi kudin balan kamuwa da matsanancin soyayyarsa?

Bayan kwana biyu sajida tasamu me gidan fu’ad da maganar zance aurenta da fu’ad, Amman ta boye masa gurin Wanda zashi neman aurenta,”yace karta damu InshaAllahu zaije ….fu’ad Wanda ya kasa samun natsuwar zuciya gabadaya ya tattara zance wani auren najma da sajida dayake son yi gefe saboda bulayin neman me’ad da sanyin idaniyansa ya taho guest house din me gidansa inda yafi tunanin zai samesa ya nemi izinin agurin aikinsa domin samun gano inda iyalinsa Suke,yashigo cikin parlour’n dayake zaune yasamu guri ya zauna yana sauke naunayen ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa sannan ya gaishe dashi .

Ya amsa yana ajiye magazine din dake rike a hannunsa,yana dubansa “yanzu nake shirin nemanka nan ya karo masa abinda sajida ta bugo ta gaya masa. wata mummunar tashin hankali ya tsinci kansa ciki take gefen kansa ya Sara ya d’ago agigice yana dubansa batare dayace masa komai ba me gidansa yacigaba da mgn yanzu sai ka sanar min da inda gidansu ita dayar yarinyar take sai ayi abun gabadaya a huta ,sosai fu’ad ke kallonsa da idanunsa da suka gama canza kalla har lokacin sunan mutumin dayaji yafito daga cikin bakinsa yake masa yawo acikin kwakwaluwarsa “to me hakan yake nufi da mahaifin me’ad yabada goyon bayan wannan aure? 

Zuciyarsa tabashi amsa da ya yana nufin abubuwa dayawa .

a matukar zuciye ya runtse idanunsa yana tsuma bai tsaya gayawa me gidansa matsayin mutumin dazaije gurinsa neman aure ba ….

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~   

     JIDDATULKHAIRI

      MARUBUCIYAR 

    MATAR DATTIJO 

Page 79

……Jikinsa ne yacigaba tsuma , kansa gaba ɗaya ya kulle, yayi mamakin jin abinda mai gidansa ya fad’a mishi, hankakinsa gaba daya yagama tashi ,xuciyar sa ta shiga rud’ani, “wai me surukin nashi yake nufi da shi, ?

“wane irin zato surukin nasa yake masa, ?

“me yasa ya gwammace kar’bar auren sajeeda alhalin lokacin da zai aure me’ad kin amincewa yayi ? Tambayoyin da ya rika yiwa xuciyarsa kenan .

“Yasan zai yi hkn ne Dan kawai ya bak’antawa me’ad rai .. ..

A fusace ya mike zai bar parlour’n, cikin natsuwa mai gidansa ya kira shi “fu’ad ina zaka je haka,? Tsayawa yayi yana haki batare dayace masa komai ba .

” me yasa naga yanayinka gaba daya ya canja? Dawo ka zauna”

A hankali cikin nutsuwa fu’ad ya dawo ya zauna yana fuskantar mai gidansa. “Gaya min menene damuwar ka fu’ad, naga daga yin wannan Maganar gaba daya ka canja daga farin ciki zuwa akasinsa, hankalinka ya tashi damuwa ta bayyana a idanunka, fad’a min idan akwai wata matsala ne musan yadda zamu shawo kanta “

Sunkuyar da kai fu’ad yayi sannan ya fara yin magana cike da ladabi da girmama ga mai gidan sa

“Yalla’bai shi fa wannan mutumin da zai kar’bi auren sajeeda ba kowa bane face mahaifin me’ad”

Wani irin shock mai gidan nasa yayi lokacin da yaji wannan maganar, “mahaifin me’ad fa ?” Ya maimaita yana kallon fu’ad cike da neman K’arin bayani 

“Kwarai kuwa yalla’bai mahaifin me’ad ne ,”Abinda yake ƙara d’aure min kai shi ne ta yadda zai yi ya amshi auren sajeeda alhalin a da can baya lokacin da xan auri me’ad ‘ke’kashe ƙasa yayi yace baxan aureta ba, to yanzu kuma wane dalili ne zai sa ya amince na auri sajeeda tabbas nasan akwai wata manufa a cikin zuciyar shi”.

Shiru mai gidansa yayi yana nazarin Wad’annan maganganun da fu’ad ya fad’a masa, bayan sun kammala maganar da zasu yi ne suka yi sallama fu’ad ya tashi ya bar me gidansa zaune yana mamakin abinda ke shirin faruwa.

Yana fitowa harabar gidan Motar shi ya bud’e ya shiga sai yaji kamar baxai iya yin driving din ba saboda wannan Maganar da aka yi masa ,tambayar kansa ya shiga yi me Mahaifin me’ad yake nufi da wannan batun da da’akazo masa da shi da rana tsaka, ?

tunani ya rika yi gami da nazari, ba ƙaramin caji ƙwaƙwalwarsa ta rika yi ba a haka har ya isa gida wanka yayi ya sake fita neman me’ad sai bai samu ganinta bai yi tunanin zuwa gurin aikinta ba ,saboda yasan halinta ,kad’an daga cikin halinta su siyar da hali agurin shi kuma abinda bazai so faruwarsa kenan ba .

A ɓangaren me’ad kuma, har yanzu tana fama da matsalar da ita kanta bata san asalinta ba, ba kuma ta san dalilin da yasa ta tsinci kanta a wannan halin ba,sannan har wannan lokacin bata daina tunanin hakunci da chairman din office din su ya fara tunanin yanke mata ba ,ta hanyar dakatar da ita amma sbd kwarewar ta ga iya aikin da jajircewa wajen tsayawa tayi aikin yadda ya kamata yasa ya d’aga mata kafa gabadaya ta fige ta rame tafita haiyacinta ban da kuka babu abinda take ..

 Hankalinta kullun sake tashi yake ganin yadda kullum matsalarta gaba take yi bata baya ,hkn yasa ta sake dagewa da addu’a da sadaka da kiyamullaili a kan Allah ya kawo mata karshen wannan matsalar da take ciki, duk da wannan jajircewar da take wajen addu’a da sadaka still dai har yanzu bata iya xama a office dinta domin gudanar da aikinta kamar yadda yakamata ,yayinda tsakanin su mudansir da tahir amintarsu ta dawo sama sama ko nace ta kusan Yankewa, saboda kusan kowa yanzu harkar gabansa yake sai dai a kasan zuciyar mudansir yana jin cewar bazai iya barin tahir hk ba sai ya bisa da bita da kulle. 

sajida zaune a d’akinta tana tunanin yadda aurensu zai kasance da fu’ad , ita tana jin idan duk duniya zasu had’u akanta matsawar fu’ad ya amince da aureta zata aureshi ko da kuwa mutuwa me’ad zatayi ,ita Sam bataji kunyar ko tsoro acikin dady’n me’ad zai kar’bi aurenta ,a ganinta ma meye aciki Dan ta auri fu’ad? 

“Tana son shi bugu da kari kuma ita me’ad tayi wasa da damarta ta hanyar rashin kulawa da gidanta, yanxu hk tana da labarin duk abinda ya faru daga korar da mahaifinta yayi mata har zuwa neman da fu’ad ya haukace agari yana yi akanta, gashi ita tasan hotel din da me’ad take gaya masa ne kawai ba zatayi ba ,tana nan tana jiran yagaji da nemanta ya hakura ya dawo haiyacinsa suyi aurensu a wuce gurin Dan ta najma me sauki ne ita me tasan yadda zatayi daita a karshe matukar ya aureta bazai ta’ba tunanin wani aurenta ba hatta me’ad din karon kanta zatasa ya manta daita arayuwarsa ,tana cikin wannan tunanin kiran khalid yashigo wayarta,taja dogon tsaki tare da furta another problem sannan ta d’auki wayar “meye ne zaka dameni bafa nason takura 

“Ki fito ina jiranki a harabar gidanku ya fad’a atakaice tare da katse kiran .

khalid matashin saurayi ne D’an kimanin shekaru a shirin da shida zuwa da bakwai ,abokin aikinta ne dake bibiyarta da sunan friendship har ta kai daya fito fili ya bayyana mata sirrin dake ransa , Amman fur taki amince masa asalima sai yanke halaka tayi dashi saboda bataga wani abin so ajikinsa ba ,kuma tun daga ranar bata sake barin sun had’u da junansu ba balle ya karanto shirme ,shi kuma babu abinda yake kwadayi da son gani kmrta .duk da bata sanar masa ba yasan komai akan yadda take mugu mugun son fu’ad .  

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button